12
Jan
Daga NASIR S. GWANGWAZO A yammacin ranar Litinin, 3 ga Janairu, 2022, wato ranar da aka yi jana’izar marubuci kuma ɗan siyasa a Nijeriya, Alhaji Bashir Othman Tofa, rasuwa, Majalisar Dattawan Kannywood ta kai ziyarar ta’aziyya gidansa da ke Gandun Albasa a Birnin Kano. Wannan ya biyo bayan taron da majalisar ta gabatar ne a daren Lahadin da ta gabata, wato 02 Janairu, 2022, inda ta shirya liyafar taya murnar shigowar sabuwar shekara lafiya, to amma sai aka wayi gari da rasuwar hamshaƙin dattijon ƙasar, inda nan da nan dattawan na Kannywood suka sake tattara kansu, suka ɗunguma wajen ta’aziyya. …
