Editor

9513 Posts
Alfanu da muhimmancin tafiye-tafiyen Hausawa zuwa wasu ƙasashe

Alfanu da muhimmancin tafiye-tafiyen Hausawa zuwa wasu ƙasashe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A baya mun duba tafiye-tafiyen Hausawa zuwa wasu ƙasashen duniya da dalilan da suka kai su, waɗanda suka haɗa da ko dai ta hanyar fatauci ne ko cinikayyar bayi. Baya ga haka kuma, mun ga ire-iren ƙasashen da suka je, kamar Birnin Tiripoli da ke Ƙasar Libiya da Ƙasar Chadi da Turai da kuma kamar ƙasashen Kudancin Amurka da suka haɗa da Brazil da sauransu. A bisa kyakkyawan bincike da nazari, duk inda aka samu wata al’umma tana gudanar da harkokin rayuwarta to, nan ne take tafiyar da al’amuran rayuwarta da suka haɗa da al’adunta da…
Read More
Yau Buhari zai ziyarci Jihar Ogun

Yau Buhari zai ziyarci Jihar Ogun

A yau ɗin nan ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki na yini guda zuwa Jihar Ogun inda zai ƙaddamar da wasu ayyuka da gwamnatin jihar ƙarƙashin Gwamna Dapo Abiodun, ta aiwatar. Shugaba Buhari tare da Gwamna Abiodun
Read More
Da marubuta na da haɗin kai matsalarsu za ta yi sauƙi – Shamsiya Kaduna

Da marubuta na da haɗin kai matsalarsu za ta yi sauƙi – Shamsiya Kaduna

“Ba inda muryar rubutu ba ta iya shiga” Daga AISHA ASAS Marubuta mata na daga cikin ƙashin bayan duk wani cigaba da aka samu a duniyar rubutun litattafan adabin Kano. Jajircewa da sanin abin da makaranta ke buƙata ya sa suka yiwa maza marubuta da dama zarra, har ta kai ko maza 'yan uwansu sun fi karɓar rubutun na mata fiye da nasu. Duk da an tabbatar mazan ma ba wai an bar su a baya ba ne, kusan za mu iya cewa, marubuta mata tsintar dami suka yi a kale, kasancewar littafan da aka fi karantawa na rayuwar yau…
Read More
Dukkanku makiyaya ne

Dukkanku makiyaya ne

Daga AISHA ASAS Annabin rahma ya ce, “Dukkanku makiyaya ne, kuma Dukkanku abin tambaya ne a kan abin da ku ke kiyo.” A yau shafin iyali zai yi tsokaci kan iyaye da ke facali da koyarwar Musulunci kan tarbiyar ‘ya’yansu. Sun ɗaura zanen aro da bai dace da addini da al’ada ta malam Bahaushe ba. Cikin sauƙin da mu ka samu a matsayinmu na Musulmai, Musulunci ya bayyana mana komai na rayuwarmu, tun daga aure zuwa haihuwa da kuma tarbiyar ‘ya’yan da Allah Ya ba mu amanarsu. Hakan na nufin, addini bai bar mu kara zube ba. Sai dai duk…
Read More
Amfanin tazargade ga lafiyar iyali

Amfanin tazargade ga lafiyar iyali

Daga BILKISU YUSUF ALI Anti Bilkisu, muna son mu ji amfanin tazargade ga lafiyar iyali. Tazargade tana da matuƙar amfani a zamantakewar iyali hasali ma a shekarun baya zai yi wahala ka shiga gidajen Hausawa ba tare da ka tarar da an yi tanadinta ba don magance larurori na jiki ko na al’ada. Hausawa na amfani da ita don magance cutoci mabambanta. A wani nazari da Farfesa Bunza ya yi ya bayyana ana amfani da tazargade don:- -Magance larurorin ciki, kamar matsalolin dattin ciki da kumburin ciki da ƙugin ciki wanda ake haɗa ta da tsamiya da gauta a sha.…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Buhari ya janye haramcin Tiwita a Nijeriya

Da ɗumi-ɗumi: Buhari ya janye haramcin Tiwita a Nijeriya

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ɗage takunkunmin da ya ƙaƙaba wa kamfanin Tiwita a Nijeriya bayan cika sharuɗɗan da gwamnati ta gindaya masa. Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa mai ɗuake da sa hannun shugaban hukumar NITDA bayan sahalewa daga ministan sadarwa, Isah Ali Pantami. Ana sa ran shafin Tiwita ya soma aiki daga ƙarfe 12 na daren yau Laraba.
Read More
‘Yan sanda sun cafke matashin da ake zargi da kashe ɗalibar Jami’ar Jos

‘Yan sanda sun cafke matashin da ake zargi da kashe ɗalibar Jami’ar Jos

Daga BASHIR ISAH 'Yan sanda a garin Jos, babban birnin jihar Filato, sun cafke matashin da ake zargi da kashe wata ɗalibar Jami'ar Jos mai suna Jennifer Anthony. A ranar Laraba 'yan sanda suka baje kolin masu laifi da suka haɗa da masu garkuwa da mutane, 'yan ƙungiyar asiri, masu safarar mutane, 'yan fashi da makami da kuma Moses Oko ɗan shekara 20 da aka zarga da halaka Jennifer a ranar jajibirin sabuwar shekara. An ce bayan halaka Jennifer da ya yi, Oko ya kuma ƙwaƙule idanun marigayiyar gami da cire wasu sassan jikinta don cimma buƙatar tsafi. Bayanan 'yan…
Read More
Tsohon gwamnan Oyo, Alao-Akala ya kwanta dama

Tsohon gwamnan Oyo, Alao-Akala ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH Sahihan rahotanni daga jihar Oyo sun nuna cewa tsohon gwamnan jihar, Adebayo Alao-Akala, ya rasu. Mai magana da yawun jam'iyyar APC, Olatunde Abdulazeez, shi ne ya tabbatar da mutuwar Akala a wata tattauwa da jaridar Punch a ranar Laraba. Marigayin wanda haifaffen garin Ogbomoso ne kuma ɗan siyasa, ya bar duniya ne yana da shekara 71. Wata majiya ta kusa da marigayin ta bayyana cewa, tsohon gwamnan ya rasu ne a ɗakinsa a Ogbomoso a ranar Laraba bayan fama da ya yi da rashin lafiya. A halin rayuwarsa, Mr Alao-Akala ya taɓa aikin ɗan sanda, kuma ya…
Read More
‘Yan bindiga sun sace mahaifiyar ɗan majalisa a Kano

‘Yan bindiga sun sace mahaifiyar ɗan majalisa a Kano

Daga WAKILINMU Bayanan da MANHAJA ta samu daga jigar Kano,sun nuna wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun dira Kano har ma sun sace mahaifiyar ɗan Majalisar Jihar mai wakiltar Mazaɓar Gezawa, Hon. Isyaku Ali-Danja. Jaridar DAILY NIGERIAN ta kalato cewa, 'yan bindigar sun yi dirar mikiya ne a gidan mahaifiyar ɗan majalisar da ke Gewaza da misalin ƙarfe ɗaya na dare inda suka fasa ƙofar gidan da ƙarfin tsiya kana suka yi awon gaba da dattijiyar. Da yake bayani kan lamarin, Ali-Danja, wanda tsohon shugaban majalisar Kano ne, ya ce da farko sai…
Read More
An gudanar da taron ƙaddamar da fim ɗin ‘Lu’u-Lu’u’

An gudanar da taron ƙaddamar da fim ɗin ‘Lu’u-Lu’u’

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano Bayan kammala shirya katafaren fim ɗin wanda ya zo da wani sabon salo na ban mamaki. Kamfanin shirya finafinai na 'Kannywwod Executive' ya shirya taron ƙaddamar da shi kafin a ɗora shi a shafin su na 'YouTube' wanda a ke sa ran za a fara kallon sa a farkon shekarar nan ta 2022. Taron, wanda aka gudanar da shi a ranar Litinin, 27/12/2021, a wajen taro na Ali Jita da ke Lawan Dambazau Road a Kano, ya samu halartar manya daga ciki da kuma wajen masana'antar finafinai ta Kannywwod. Tun da farko da ya ke jawabi…
Read More