14
Jan
Daga ABDUL HAQ An haifi Sheikh Dakta Ahmad Bamba a shekarar 1940, sannan ya taso a garin Alabar A.E.B ko Nguwan Gonjawa, a Jihar Kumasi ta ƙasar Ghana. Mahaifinsa shi ne, Muhammad Ibrahim Bamba iyayensa mata su ne, Hajia Khadijah (Mma Adizatu) and Hajia Fatima (Mma Hajia), su kuma sun kasance 'ya'ya ne a wajen Mma Gyamata. Ita kuma Gyamata ta kasance 'ya a wajen shahararren malamin addini sannan dattijo na farko a unguwar Gonja ta jihar Kumasi. Wato Marigayi Mallam Sani. Ya fara ɗaukar darasin ilimin addini a wataniyya a ƙarƙashin sanannen Sufin nan, Alhaji Baba Al-Waiz. Wanda aka…
