Buhari ya nuna alhini kan rasuwar Chief Shonekan

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nuna ahininsa dangane da rasuwar dattijon ƙasa kuma tsohon Shugaban Ƙasa na riƙon ƙwarya, Chief Ernest Shonekan.

Cikin wata sanarwa da ya fitar ta hannun mai magana da yawunsa, Mr Femi Adesina a jiya Talata a Abuja, Buhari ya miƙa ta’aziyyarsa ga maiɗakin marigayin, Margaret tare da sauran dangi da masoya haɗa da gwamnatin jihar Ogun da kuma al’ummar jihar kwata.

Buhari ya bayyana yadda marigayin ya zaɓi ya ajiye harkokin kasuwancinsa don riƙe gwamnatin ƙasa a daidai lokacin da ƙasar ke da buƙatar tsayayyen shugaban da zai mulke ta.

Ya ƙara da cewa, Marigayi Shonekan ya nuna wa duniya cewa son ƙasa da da haɗin kanta da kuma sadaukarwa don cigabanta na gaba da komai.

A cewarsa, marigayin na da haƙƙi babba a kan Nijeriya, wanda a halin rayuwarsa ya kasance mai son zaman lafiya wanda bai daina aiki tuƙuru ba don ganin cigaban Nijeriya da ke bisa tsarin dimokuraɗiyya.

A ƙarshe, Buhari ya yi addu’ar samun rahama ga marigayin a wajen Allah Maɗaukaki, tare da fatan Nijeriya ba za ta mance da shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *