Editor

9513 Posts
A Nijeriya ne kawai miji zai bushi iska ya kori matarsa daga gida gwamnati ta ƙyale shi – Uwani Kazaure

A Nijeriya ne kawai miji zai bushi iska ya kori matarsa daga gida gwamnati ta ƙyale shi – Uwani Kazaure

“Laulayin ciki ne babban ƙalubalena a wurin aiki” Daga UMAR AƘILU MAJERI Hajiya Uwani tsohuwar malamar makaranta ce kuma masaniya akan yaren Turanci da Hausa. Ta kasance ɗaya daga cikin Mata 'yan gwagwarmayar nema wa Mata da ƙananan Yara 'yanci a Jihar Jigawa. Yanzu haka Hajiya Uwani ta fara tunanin kafa wata gidauniya mai zaman kanta saboda ta riƙa taimaka wa yara matan da aka ci zarafinsu, don ganin ta kare masu mutuncinsu kamar yadda sauran al'umma suke da. Wakilinmu na Jihar Jigawa, Umar Aƙilu Majeri ya samu nasarar zantawa da ita a gidanta da ke Dutse. Ga yadda tattaunawar ta…
Read More
PDP Za Ta Amshi Mulki A 2023, Inji Saraki

PDP Za Ta Amshi Mulki A 2023, Inji Saraki

Daga NASIR S. GWANGWAZO Tsohon shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, ka tsohon gwamnan Kwara, Dr. Abubakar Bukola Saraki a shirye PDP ta ke ta ƙwace mulki a shekarar 2023. Saraki ya faɗi haka ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi yau Talata da gidan talabijin na AriseTv. Tsohon Shugaban Majalisar ta Dattawa ya bayyana cewa a yanayin yadda Nijeriya take a rarrabe, zai ba PDP dama ta lashe zaɓen 2023. Ya ce, Nijeriya ba ta faɗa wa hali da yanayin rarraba ba irin na wannan lokaci a ƙarƙashin mulkin Buhari. "Muna da duk wani abu da ake buƙata don…
Read More
Shaye-shaye a tsakanin matasa: Ina mafita?

Shaye-shaye a tsakanin matasa: Ina mafita?

Assalamu alaikum. Yau zan yi wasiƙa ne akan wata matsala da take neman fin ƙarfinmu. Za mu tattauna ne akan matsalar da kusan yanzu ta zama ruwan dare musamman a yankunan arewacin ƙasar nan. Haka zalika, kamar yadda muka sani ne cewa, Hukumar yaƙi da fatauci da shan miyagun ƙwayoyi (NDELA) na yawan cewa akwai buƙatuwar irin waɗannan kiranye-kiranyen. Sai dai abin da mamaki ganin yadda mutane da kuma sauran iyaye ba sa iya ɗaukar kowane mataki don ganin an kawar da wannan mummumar ɗabi’ar. Kuma kowanne bigire kake walau talaka ko mai kuɗi, malami ko ma’aikaci kana da gudunmawar…
Read More
LUFADA ta shirya taro a karon farko

LUFADA ta shirya taro a karon farko

Daga MUHAMMADU MUJITABA Ƙungiyar cigaban zuriyar Lulu (LUFADA), ƙarƙashin shugabcin Alhaji Abdulrashid Mansur Ashiru ta gudanar da gagarumin taro a karon farko wanda aka gabatar a ɗakin taro na gidan Mumbayya a Gwammaja cikin ƙaramar hukumar Dala ta Jihar Kano a ranar Lahadi ta makon jiya. A jawabin shugaban ƙungiyar Alhaji Abdulrashid Mansur Ashiru ya bayyana cewa, maƙasudin wannan taro shi ne a cigaba da zamunci tsakaninsu kuma a cigaba da taimakawa juna a tsakaninsu kamar yadda ya kamata da kuma cigaban tarbiyya na wannan zuriya ta cigaban da nagarta kuma yanzu haka matasa 500 na zuriyar Lulu suka samu…
Read More
Ƙungiyar matan Ƙadiriyya ta shirya bikin murnar Mauludi

Ƙungiyar matan Ƙadiriyya ta shirya bikin murnar Mauludi

Daga MUHAMMADU MUJITABA Naƙibatu Ƙadiriyya, Malama Baraka Fatima Adamu Ɗanfanta ta shirya gagarumin mauludi, inda ta jagoranci gangamin mata daga ƙungiyoyi daban-daban da kuma ɗaiɗaikun mata daga Kano da wajenta don taya ɗaukacin al’ummar musulmai murnar zagayowar watan da aka haifi fiyayyan halitta, Annabi Muhammadu (SAWW), wannan watan mai alfarma wanda aka gabatar a Unguwar yalwa da ke Goron dutse cikin birnin Kano a ranar lahadi da ta gabata. A jawabin naƙibatul ƙadiriyya, malama Baraka Adamu Ɗanfanta ta ce, maƙasudin wannan taro shi ne jadada murna da farin ciki na samuwar wannan babban baiwa da Allah ya yi mana na…
Read More
Akwai buƙatar magance matsalar ɓatagarin ’yan jarida – NUJ

Akwai buƙatar magance matsalar ɓatagarin ’yan jarida – NUJ

Daga RAMADAN SADA Ƙungiyar 'yan jaridu ta ƙasa (NUJ), reshen Zariya da ke jihar Kaduna, ta yi kira ga hukumomin tsaro su taimaka ma ta wajen kawar da ɓata garin ’yan jaridu a cikin su. Sanarwar ya fito ne a ƙarshen taron da ƙungiyar ta yi a ranar 14 Oktoba 2021, inda ta ƙara da nuna buƙatar ta na samun cikakken jagoranci kamar yadda take gudanar da aikinta na ƙasa. Ƙungiyar ’yan jaridu ta Nijeriya reshen Zariya ta yi kira ga masu kula da tsaro da su taimaka wajen tsaftace harkar aikin jarida da kuma cire masu kiran kansu ’yan…
Read More
Buhari ya ƙaddamar da kuɗin intanet na e-Naira

Buhari ya ƙaddamar da kuɗin intanet na e-Naira

Daga BASHIR ISAH Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da kuɗin intanet na e-Naira ƙarƙashin kulawar Babban Bankin Nijeriya (CBN). Yayin ƙaddamarwar wadda ta gudana a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja a ranar Litinin, Shugaba Buhari ya yaba wa gwamnan CBN, Mr. Godwin Emefiele, bisa wannan cigaba na samar da sabon tsarin hada-hadar kuɗi a ƙasa. A nasa ɓangaren, Mr. Emefiele ya sanar da samuwar wani sabon tsarin kasuwanci mai suna “The 100 for 100 PPP – Policy on Production and Productivity,” wanda a cewarsa tsarin zai taimaka wa ƙasa gaya wajen rage dogaro da shigo da kayayyaki daga…
Read More
Dokar kiwo a Kudu: Makiyaya sun fara hijira zuwa Arewa

Dokar kiwo a Kudu: Makiyaya sun fara hijira zuwa Arewa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse Sakamakon sanarwar da mafi yawan gwamnonin kudancin Nijeriya suka bayar na hana Fulani makiyaya gudanar da kiwo a jihohinsu ta sa dubban Fulani yin hijirar dole zuwa Arewa, musamman daga jihohin Oyo, Osun, Ogun, Ondo, Lagos da Ekiti. Wakilin Manhaja a Jihar Jigawa ya gane wa idonsu yadda makiyayan suke tururuwa shiga jihar Jigawa daga jihohin Yarabawa da Igbo bayan da suka yi kiran da su fice su bar mu su yankunansu. Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah, reshen Jihar Jigawa, Alhaji Adamu Idris Babura, ya ce, shi da kansa ya gane wa idonsa 'yan…
Read More
Ku fifita labaran nasarar jami’an tsaro bisa ta ’yan ta’adda – Buhari ga ’yan jarida

Ku fifita labaran nasarar jami’an tsaro bisa ta ’yan ta’adda – Buhari ga ’yan jarida

Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bukaci kafafen yaɗa labarai da su riƙa yin magana kan asalin cigaban da ake samu wajen yaƙi da matsalar tsaro, ya ce, domin kuwa ana samun muhimman nasarori a yaƙin. A cikin wata sanarwa ɗauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin yaɗa labarai, Garba Shehu, a ranar Litinin, Buhari ya ce, ya kamata a maye gurbin kalmar 'matsalar tsaro' da 'gaskiyar raguwar rashin tsaro.' Takardar mai taken, ‘Shugaba Buhari ya taya Musulmai murna a ranar Mauludi, ya tabbatar da cewa ana samun muhimman…
Read More
’Yan Najeriya za su ba wa ɗan takarar Gwamnan New York gudunmawar Dala 33,000

’Yan Najeriya za su ba wa ɗan takarar Gwamnan New York gudunmawar Dala 33,000

Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai ]an takarar gwamnan Newyork ta Amurka, Mista Eric Adams, zai samu tagomashin gwaggwaɓar gudunmowa har ta dala dubu talalin da uku ($33,000) daga 'yan Najeriya mazauna ƙasar ta Amurka. An ba da gudunmowar gare shi ne domin ya yi yakin zaɓen da za a yi a kakar zaɓe ta watan gobe wato Nuwambar shekarar nan da muke ciki ta 2021.  Shugaban kwamitin cigaban 'yan Najeriya  a can ƙasar, Mista Yinka Dansalami, ya bayyana cewa, su 'yan Najeriya na ƙasar Amurka za suna sane da yadda harkokin siyasa suke tafiya sannan kuma suna…
Read More