25
Oct
Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban Haɗaɗɗiyar Kungiyar Masu Sana’ar Shirin Finafinan Hausa ta Nijeriya (MOPPAN) mai barin gado, Dr. Ahmad Muhammad Sarari, ya kafa wani sabon tarihi a masana’antar shirin fim ta Kannywood, inda ya zama shugaban ƙungiyar na farko da ya fara sauka daga muƙaminsa ba tare da ya ƙara ko da kwana ɗaya ba. A tarihin ƙungiyar, wacce aka kafa ta tun a farko-farkon shekarun 2000 kuma ta samu aƙalla shugabanni guda biyar a shekaru 17, ciki har da Sarari, daga wanzuwarta zuwa yanzu, babu wanda ya samu ikon sauka daga muƙamin shugabancin a lokacin da wa’adinsa ya…
