Editor

9513 Posts
Buhari ya yaba da zaɓukan APC a Katsina

Buhari ya yaba da zaɓukan APC a Katsina

Daga UMAR GARBA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓukan shugabannin jam'iyar APC a Katsina tun daga matakin mazaɓu, ƙananan hukumomi har zuwa matakin jiha. Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ne ya bayyana haka a lokacin da kwamitin shirya zaɓukan shugabannin jam'iyyar ya miƙa rahotonsa na ƙarshe bayan kammala aikinsa. Kwamitin wanda ke ƙarƙashin jagorancin shugaban ma'aikatan fadar gidan gwamnati na Katsina, Muntari Lawal da haɗin gwiwa da kwamitin shirya zaɓukan daga uwar jam'iya ta ƙasa. Masari ya kuma bayyana cewar Shugaba Buhari ya yi matuƙar farin ciki bisa ga yadda aka…
Read More
Kasafin 2022: Buhari ya kasa cika alƙawarin da ya ɗauka a fannin ilimi

Kasafin 2022: Buhari ya kasa cika alƙawarin da ya ɗauka a fannin ilimi

Daga BAKURA K. MUHAMMAD a Bauchi Duk da alƙawarin da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yi a zauren taro na ƙasa da ƙasa cewar, zai ƙara kason fannin ilimi daga cikin dabtarin kasafin kuɗi na shekaru masu zuwa ya ƙaru zuwa a taƙaice kashi hamsin cikin ɗari, kuma da sannu zuwa kashi ɗari a shekara ta 2025, sai kwatsam a cikin dabtarin kasafi na shekara ta 2022 kaso da aka yi wa fannin ya faɗi warwas zuwa Naira tiriliyan ɗaya da kusan ɗigo uku ko kashi bakwai da ɗigo tara cikin ɗari, daga cikin gundarin dabtarin kasafin da ya ƙunshi…
Read More
Tattaki a yanar gizo: Leƙe cikin zaurukan YahooGroups

Tattaki a yanar gizo: Leƙe cikin zaurukan YahooGroups

Daga KHALID MUSA Mahawarar RuwaKafin ɗaurin ɗamba, Ina son masu sauraro na su sani cewa, wannan muƙala ba nazarin ilmi ba ce (Academic Presentation). Don haka ba lallai ne ta cika dukkan ƙa’idojin nazari a tsarin darasin harshe ba. Wannan takarda nazari ce kawai ta mai sha’awar adabi da bibiya. Na kauce wa bayar da tarihin taurarin muhawarar, haka nan ban yi izna da kawo fassarar wasu jigogin kalmomi ba, domin larurar da na ambata a sama da kuma kauce wa tsawaitawa. Ina fata za a lura kuma a yi min uzurin dukkan wata gazawata da ka iya bayyana cikin…
Read More
Aikin gayya don inganta walwalar al’umma

Aikin gayya don inganta walwalar al’umma

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Aikin gayya wata tsohuwar al'ada ce da al'umma suka saba amfani da ita, don taimakon junansu a yayin da aka fuskanci wani babban aiki ko ƙalubale da ya ke buƙatar hannu da yawa, domin a samu sauƙin magance shi. Ko da ya ke har yanzu ba za a ce an daina ba, musamman a ƙauyuka, amma ba kasafai aka cika bai wa aikin gayya muhimmanci ba, saboda yadda haɗin kai da zumunci ya yi rauni a tsakanin jama'a, bambance-bambance da hidimomin rayuwa sun sa jama'a ba sa kallon kansu a matsayin al'umma mai manufa da buri…
Read More
Jirgin Abuja zuwa Kaduna zai ci gaba da aiki yau – NRC

Jirgin Abuja zuwa Kaduna zai ci gaba da aiki yau – NRC

Daga BASHIR ISAH Hukumar Gudanarwa ta Ma'aikatar Sufurin Jiragen Ƙasa ta Nijeriya (NRC), ta bayar da sanarwar cewa jirgin da ke zirga-zirga tsakanin Abuja da Kaduna zai ci gaba da aiki yau Asabar kamar yadda aka saba. Hukumar ta fitar tsari da kuma lokutan yadda jirgin zai ci gaba da gudanar da aikinsa, inda ta ce yanzu da ƙarfe 09:50am jirgin zai riƙa tashi daga Idu, Abuja, sai kuma ƙarfe 10:50am daga Rigasa, Kaduna. Sanarwar hukumar ta nuna cewa, sauran jiragen ma za su ci gaba zirga-zigarsu babu tsaiko. Daga nan, hukumar ta yi amfani da wannan dama wajen bai…
Read More
Sojojin Najeriya sun gama da Malam Baƙo, magajin Shugaban ISWAP ɗin da suka kashe, Al-Barnawiy

Sojojin Najeriya sun gama da Malam Baƙo, magajin Shugaban ISWAP ɗin da suka kashe, Al-Barnawiy

Daga AMINA YUSUF ALI Mai ba wa Shugaban ƙasar Najeriya, Muhammadu Buhari shawara a kan sha'anin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya) ya sanar da mutuwar Malam Baƙo, magajin tsohon shugaban wannan ƙungiyar ta'addancin mai haɗari ta ISWAP, Abu Musab Al-Barnawiy. Munguno ya yi wannan bayani ne, a lokacin da yake jawabi ga wakilai daga majalisar dokoki, a yayin taron ganawa tsakanin shugaban ƙasa da shugabannin tsaron ƙasar nan, ranar Alhamis ɗin da ta gabata a Abuja. A dai taron wanda shugaban ƙasa Buhari ya jagoranta, an yo waiwaye game da mutuwar tsohon shugaban na ISWAP Albarnawiy wanda Janar…
Read More
An sako ɗalibai 30 da malamai biyu na Kwalejin Yauri

An sako ɗalibai 30 da malamai biyu na Kwalejin Yauri

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Rahotanni daga Jihar Kebbi na bayyana cewa, ɗalibai 30 da kuma  malamai biyu da aka sace daga makarantar Kwalejin Tarayya ta Birnin Yauri sun samu kansu. Kamar yadda wata takarda mai ɗauke da sa hannun Alhaji Yahaya Sarki, Mataimaki na Musamman kan Harkar Yaɗa Labarai ga Gwamna Atiku Bagudu na jihar, ta bayyana cewa, “Yau Alhamis 21 (jiya) ga watan Oktoba, ɗalibai 30 daga makarantar FGC Birnin Yauri sun iso nan babban birnin jiha  bayan da aka sako su. Yanzu haka ana cigaba da duba lafiyarsu kafin a sada su da iyayensu. Haka-zalika yanzu haka gwamnati tana…
Read More
Gobe Asabar za a ƙaddamar da littafi kan fyaɗe a Kano

Gobe Asabar za a ƙaddamar da littafi kan fyaɗe a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gobe Asabar ne dai za a ƙaddamar da littafin fyaɗe mai suna 'Fyaɗe Makamin Cutar da Al'umma',  wanda Falalu Yunusa Abubakar ya rubuta, wanda malami ne a Hukumar Makarantun Sakandire ta Jihar Kano (KSSSMB). Malamin, ya rubuta littafin ne dai dangane da illoli da matsalolin da fyaɗe ke haifarwa a cikin al'umma. A cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin ƙaddamar da littafin, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino MON ya rabawa manema labarai a Kano, ya ce za a ƙaddamar da littafin ne a a gidan Mumbayya da ke Gwammaja a cikin birnin Kano. Sanarwar ta…
Read More
Buhari ya rushe hukumomin kula da hada-hadar man fetur da shugabanninsu

Buhari ya rushe hukumomin kula da hada-hadar man fetur da shugabanninsu

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar litinin ɗin da ta gabata ne, dai gwamnatin tarayyar Najeriya, tare da sahalewar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta tabbatar da rushe Hukumomin kula da hada-hadar man fetur, DPR da PPPRA da kuma PEP. wato dai ta shafe su tas! Su Hukumomin kula da hada-hadar man fetur wani sashe ne na albarkatun man da yake da alhakin kula da farashi da kuma tattarawa tare da kasafta kuɗaɗen sashen albarkatun man fetur. Ministan albarkatun man fetur na Najeriya, Cif Timipre Sylva, shi ya bayyana haka a yayin wani taro na ƙaddamar da kwamitocin kula da hada-hadar…
Read More
Ko tashin gwauron zabin man fetur na duniya zai amfani Nijeriya?

Ko tashin gwauron zabin man fetur na duniya zai amfani Nijeriya?

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar juma'ar da ta gabata ne, aka sanar da farashi ma fi tsada da gangar man fetur ta yi. Abinda ya kai aka fara sayar da kowacce gangar mai a kan farashin Dalar Amurka Tamanin da biyar ($85) a kan kowacce ganga. Abinda masana da masu bincike suka bayyana cewa, rabon da farashin ya yi tashin gwauron zabi kamar haka tun shekaru uku baya. Wato tun a watan  Oktobar shekarar 2018. Hasali ma dai, wannan shi ne karo na farko da farashin ya taɓa haura dalar ta Amurka tamanin ($80) in ji Kamfanin Brent oil,…
Read More