Editor

9513 Posts
Kasuwanci da aikin gwamnati shirya wa rayuwar bayan ritaya ne – Sumayyah Sarina

Kasuwanci da aikin gwamnati shirya wa rayuwar bayan ritaya ne – Sumayyah Sarina

Daga AMINA YUSUF ALI Sumayyah Ibrahim Sarina ma’aikaciyar gwamnatin Jihar Kano ce sannan a lokaci guda kuma ’yar kasuwa. A tattaunarwata da Wakiliyar Manhaja, Amina Yusuf Ali, ta bayyana wa shafinmu na Kasuwanci hikimarta ta haɗa gudu da susar ɗuwawu. Ga yadda tattaunawar ta kasance: Za mu so ki gabatar da kanki.Sunana Sumayyah Ibrahim Sarina, Asalin iyayena 'yan ƙauyen Sarina ne da ke Ƙaramar Hukumar Garko da ke nan jihar Kano. Na yi makarantar Allo, Islamiya da kuma firamare duk a cikin  ƙwaryar birnin Kano. Bayan Kammala karatun firamare ɗi na, na wuce sakandiren gwamnatin tarayya ta kwana da ke minjibir,…
Read More
“Ni ne shugaban APC na gaskiya,” inji kowa!

“Ni ne shugaban APC na gaskiya,” inji kowa!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA A makon da ya gabata ne wannan shadarar ta karaɗe kafafen yaɗa labarai, inda 'yan APC a Jihohi daban-daban ke cewa su aka zaɓa su zama shugabannin jam'iyyar na matakin Jiha. Wannan ya zama ruwan dare don kama daga jihohin da APC ke da gwamna zuwa inda ma ba ta da gwamna an samu taruka biyu na jam'iyyar da fitar da shugabanni biyu inda kowanne daga ciki ke cewa shi ne sahihin shugaban jam'iyya. Haƙiƙa wannan na nuna ɓangarorin siyasa a cikin jam'iyyar na da muradu ko muradi iri ɗaya da ke kawo neman fito-na-fito don…
Read More
Gangamin bukukuwan Maulidi

Gangamin bukukuwan Maulidi

Al'ummar Musulmi da dama a Nijeirya sun bi sahun sauran ’yan uwansu a faɗin duniya wajen murna da zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (Tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi.) Musulmai da dama sun yi amannar cewa a watan Rabiu'l Awwal, aka haifi Annabi Muhammad (SAW). A irin wannan rana ce Allah (SAW), ya yi wa halittarsa kyautar da ta fi kowacce irin kyauta daraja wato Manzon Allah SAW, kamar yadda Musulunci ya bayyana. Al'ummar Musulmai dai kan yi hidima a wannan lokaci, kamar a Nijeriya musamman a jihohin arewacin ƙasar, makarantun allo ko na Islamiyya kan shirya…
Read More
Babakeren Ganduje ya yi yawa, inji Malam Shekarau

Babakeren Ganduje ya yi yawa, inji Malam Shekarau

Daga BASHIR ISAH  Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano), ya ce, sun shigar da kukansu ga uwar jam’iyyarsu ta APC a mataki na ƙasa ne kan yadda a ke gudanar da harkokin jam’iyyar tasu ba tare da sako su ciki ba daga ɓangaren jihar a ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdulllahi Umar Ganduje, inda suka zargi ɓangaren gwamnan da yin babakere a cikin jam’iyyar. Shekarau ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar wadda Manhaja ta samu kwafinta. Cikin sanarwar, Shekarau ya soma ne da miƙa godiya…
Read More
Fasahar marubuta waƙoƙin Hausa

Fasahar marubuta waƙoƙin Hausa

Waƙa: WAƘATare da KHALID IMAM DA AMINU LADAN ALA Da karanbani da naci,Yaro kan koyi keke,Wataran ko sai ya tuƙaBabur mota da jirgi. Dagiya naci da koyo,Mai waƙa ke buƙata,Da azanci har zalaƙa,Da harshe mai balaga. Ƙafiya kuwa in kana so,Sassaƙa du a baiti,Waƙa na ƙara zaƙi,In akwai hikima azanci. Waƙa tamkar kitso ce,Sai da tsifa har da taza,Kafin a kitsa a zana,Cikin harshe na Hausa. Ɗangon waƙa mu lura,Yana da awo ma'auni,Muryar waƙa aboki,Saita ta ake a rera. Waƙa tilas a auna,Mai rerawa ya karya,Muryarsa da kyau a waƙe,Cikin rauji ya rera. Ko makaho na rabewa,Hanyar jirgi da mota,Haka…
Read More
Rashin sha’awar iyali da dalilansu (5)

Rashin sha’awar iyali da dalilansu (5)

Daga BILKISU YUSUF ALI Ci gaba daga makon da ya gabata kan abubuwan da suke sa sha'awa ga ma'aurata ko bayan babu ita ko kuma idan ta yi rauni. Maganganu masu taushi:Kissa da kisisina da maganganu masu taushi da daɗi da motsa sha’awa suna taimakawa ma’aurata kuma suna kusanto da sha’awa. Kowacce mace ita ta san yadda take tafiyar da mijinta da yadda take juyo da hankalinsa da zuciyarsa. Hatta a gun namiji shi ma ire-iren wannan lallashin da tausasa murya da maganganu mai daɗi suna taimaka masa wajen tada sha’awar matarsa har ta kai an samu abin da ake…
Read More
Matsalolin da ke tattare da aikin jarida a wannan lokacin – Abdulkarim Mohammed

Matsalolin da ke tattare da aikin jarida a wannan lokacin – Abdulkarim Mohammed

“Dole ne ɗan jarida ya san mene ne buƙatar ƙasa a aikinsa” Daga MUKHTAR YAKUBU, a Kano A wannan lokaci aikin jarida ya shiga wani yanayi da a ke ganin yana cike da ƙalubale ta ɓangarori da dama, ta yadda a ke kasa gane labarin gaskiya da na ƙarya da sauran matsaloli masu tarin yawa. Abdulkareem Mohammed tsohon ma'aikacin jarida ne a fannin rediyo da talbijin, wanda ya shafe sama da shekaru 40 yana gudanar da aikin. A yanzu shi ne shugaban kamfanin ‘Movie Image’ da ya ke gudanar da harkokin yaɗa labarai. Wakilin mu a Kano Mukhtar Yakubu ya…
Read More
Sanata Shekarau ya koka kan mayar da su saniyar ware a harkokin APC ta Kano

Sanata Shekarau ya koka kan mayar da su saniyar ware a harkokin APC ta Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata mai ci, Sanata Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano), ya ce sun shigar da kukansu ga uwar jam'iyyarsu ta APC kan yadda ya ce ana gudanar da harkokin jam'iyyar tasu ba tare da sako su ciki ba. Shekarau ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar wadda Manhaja ta samu kwafinta. Cikin sanarwar, Shekarau ya soma ne da miƙa godiya ga Allah da kuma salati ga Manzon Allah (SAW) albarkacin bikin Maulidi, kana daga bisani ya bayyana halin da ya ce jam'iyyar APC ta Kano ke ciki. A cewarsa, "Ni Sanata Ibrahim Shekarau, na…
Read More
Tsohon gwamnan Ekiti, Fayose ya ɗare acaɓa a Legas

Tsohon gwamnan Ekiti, Fayose ya ɗare acaɓa a Legas

A wani mataki don gudun kada jirgin sama ya baro shi a tasha, ya sanya tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose, ya hau acaɓa zuwa babban filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas. Wani hoton gwamnan da ya karaɗe kafafen sadarwa, ya nuna yadda tsohon gwamnan tare da dogarinsa suka hau acaɓa guda don a kai su filin jirgin. Tsohon gwamnan shi da kansa ya soma yaɗa hoton a shafinsa na facebook inda ya nuna matsalar cunkoson abubuwan hawa a Legas babu ruwanta da ko kai waye, wanda ala tilas ya zaɓi hawa acaɓa son jada ya rasa…
Read More