“Ni ne shugaban APC na gaskiya,” inji kowa!

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

A makon da ya gabata ne wannan shadarar ta karaɗe kafafen yaɗa labarai, inda ‘yan APC a Jihohi daban-daban ke cewa su aka zaɓa su zama shugabannin jam’iyyar na matakin Jiha. Wannan ya zama ruwan dare don kama daga jihohin da APC ke da gwamna zuwa inda ma ba ta da gwamna an samu taruka biyu na jam’iyyar da fitar da shugabanni biyu inda kowanne daga ciki ke cewa shi ne sahihin shugaban jam’iyya. Haƙiƙa wannan na nuna ɓangarorin siyasa a cikin jam’iyyar na da muradu ko muradi iri ɗaya da ke kawo neman fito-na-fito don gane wanda damtsensa ke samun qarfi daga kashi ɗaya.

Ni tun Ina ɗaukar abun da wasa ne har na saduda don aƙalla kowane ɓangare na da magoyin baya daga wani ɗan majalisar dattawa ko wakilai ko kuma wani minista ko wanda ya ke ikirarin fara siyasa tun duniya na zaune lafiya. Idan a cikin jam’iyya ɗaya za a samu rikicin cikin gida haka to yaya in an je ga babban zaɓe? Shi ya sa ba a taɓa zaɓe a Nijeriya wanda dukkan sassa su ka amince da sakamakon 100%. Kazalika in hakan ka ga ya munana a jam’iyya ɗaya to ba shakka an taru ne a inuwa ɗaya amma ba bisa manufa ɗaya ba sai dai don wa imma neman biyan buƙatar lashe zaɓe ta hanyar tasirin gwamnati ko kuma irin ‘yan siyasar nan da ba sa iya rayuwa a adawa don haka duk dabarar da za su yi sai sun kasance a tabarmar gwamnati mai mulki.

Zaɓen da a ka gudanar na shugabannin APC mai mulki a Nijeriya a jihohi da dama ya bar baya da ƙura. Ita kuwa ƙurar nan ba mai kwantawa don ɗan yayyafi ba ne sai in an samu zuba ruwan sama kamar da bakin ƙwarya. Aƙalla dai an samu waɗanda su ka ayyana kansu a matsayin shugabanni bibbiyu a wasu Jihohin da su ka haɗa da Kano da Bauchi. Sauran sun haɗa da Neja, Kwara da wasu sassa na kudu maso yamma. Zaɓen dai wanda zai share hanyar gudanar da babban taro na kasa na jam’iyyar a nan gaba, ya zama zakaran gwajin dafi na yadda makomar jam’iyyar zai iya kasancewa a zaben 2023.

Tuni har babbar jam’iyyar adawa ta PDP ta yi gatse ga APC kan abun da ta ke ganin gazawar APC ta gudanar da tarukan Jiha ta tsarin amintacciyar dimokraɗiyya ta cikin jam’iyya. Da alamu PDP ta ruɗe ido kan dambarwar da ta ke cikin ta na shugabanci da ma muradi kan masu son takarar Shuagban ƙasa tsakanin ‘yan kudu da Arewa. An fahimci hakan a taron majalisar ƙoli na jam’iyyar inda manyan ta su ka yi bayanai masu nuna tsoratarwa.

In mun koma APC wannan na nuna takun ta lokacin da shugaba Buhari zai kammala wa’adin mulkin sa. Wannan lokacin ba shakka za a samu sauyin tsari don ba batun adawar Buhari ta shekaru 12 ko neman zarcewar PDP bayan shekaru 16. Wannan lokacin za a gane wanda ya iya karatu ya wanke allon sa ko ya zama mai muhimmanci in mutum ya iya ruwa ya kuma iya laka. Na ji talakawa na cewa an yi walqiya sun ga kowa kuma idon su ya buɗe daga yaudara da fakewa da son zuciya wajen zaɓe. Duk da haka akwai waɗanda gari bai waye ba a birnin zuciyar su.

A Kano da ke samar da ƙuri’a miliyan 2 ga ɗan takarar shugaban ƙasa, an samu mafi tsanantar rabuwar kawuna inda manyan ‘yan jam’iyyar da su ka haɗa da tsohon gwamna Ibrahim Shekarau, Sanata Barau JIbrin, ɗan majalisar wakilai Sha’aban Sharada da sauran su, su ka yi bara’a da tazarcen shugaban jam’iyyar Abdullahi Abbas inda su ka yi taro da zabar Alhaji Haruna Danzago. Ra’ayin sabon shugaban ɓangaren, Danzago kan Abbas da ke da goyon bayan gwamna Ganduje ‘ba yawan magana ba ne iya siyasa amma samar da nasara da tafiya da jama’a.’

An saba jin shugaban jam’iyyar Abdullahi Abbas na kalamai masu tsauri misali, ‘ko da tsiya-tsiya…’ duk da haka magoya bayan sa na ƙaunarsa kuma hakan na ƙara mu su azamar aiki ga jam’iyyar ta lashe zaɓe kamar yadda a ka kammala zaɓe a zagaye na biyu a 2019 tsakanin gwamna Ganduje da ya zarce da ɗan takarar PDP Abba Gida-Gida.

Bauchi kuma wasu ‘yan jam’iyyar sun ƙi amincewa da wanda manyan ‘yan jam’iyyar a matakin tarayya ƙarƙashin Ministan Ilimi, Adamu Adamu, suka miƙa sunansa, Babayo Ali Misau. Wasu ma cewa su ka yi an taru kawai sai a ka bugo waya a ka buɗe lasifa a ka sanar da waɗanda su ka samu nasara. Na ga faifan bidiyo inda a ka karanta sunayen waɗanda su ka samu nasara a jerin sunayen da a ka canko ba tare da kaɗa ƙuri’a ba, wato ma’ana ta hanyar amincewa daga jiga-jigan jam’iyyar. Waɗanda sunayen su, su ka fi fitowa sunaye minista Adamu Adamu da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara.

Hakan ya sa wani ɓangare ya bayyana da ayyana sunan Sunusi Kunde a matsayin sabon shugaba wanda har ma ya zaga gari don alamta shi ne shugaban APC. Jigon jam’iyyar Hassan Sharif ya ce, ba za su amince da irin wannan zaɓen ba don haka ya zama wajibi a sake sabon lale.

Sharif ya ƙara da cewa, gadarar wasu ƙalilan ne da ke da hulɗa da fadar Aso Rock ke kawo ɗauki ɗora a jam’iyyar wanda ya ce haka ya faru a zaɓen da a ka gudanar a baya har jam’iyyar ta sha kaye.

Duk da wannan dambarwar, a Gombe ba a samu wani ɓangare ba, don shugaban da ke kujera Mr. Nitte Amangal ne ya zarce. Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya ya nuna na’am da yanda lamarin ya kasance. Za a jira matakin da kwamitin sulhu na APC ƙarƙashin Sanata Abdullahi Adamu zai ɗauka don daidaita Danladi da Danladidi da duk a ka haifa ranar lahadi.

Dimokraɗiyya a Nijeriya ta ƙasa tsira da muradun wasu masu son dauwama kan mulki da ‘ya’yansu da jikokinsu Hakanan sai tsarin uban gida a siyasa da zai yi wuya talakan talak ya tsaya kujera ya samu nasara ba tare da sa hannun wani madugu ba. Madugu kuma kan zama tsohon gwamna, gwamnan da ke mulki ko wani tsohon ministan ma’aikata mai tasiri. Irin waɗannan iyayen gida su ke jera sunayen waɗanda su ke so kuma su ɗora su kan kujera ko da mutane ba sa son su. Ma’ana tsarin nan na kowa ya bi in ma ka ƙi bi to an bi ma ka.

Gaskiya da sauran siyasar Nijeriya daga samun ‘yanci ko kuma ya zama waɗanda ke darewa madafun iko su zama wakilan jama’a ne ba wakilan aljifan su da muƙarrabansu ba.