Editor

9513 Posts
Ilimin ‘ya’yan Fulani na da muhimmanci a wannan zamani – Hauwa Umar Aliyu

Ilimin ‘ya’yan Fulani na da muhimmanci a wannan zamani – Hauwa Umar Aliyu

Daga ABUBAKAR TAHEER a Haɗeja Mai karatu wannan tattaunawa ce ta musamman da Hauwa Umar Aliyu, matar da ta fito daga rugar Fulani, kuma mai taimakon mata da marasa galihu. Ta fito daga garin Birniwa na Jihar Jigawa. Ta yi gidauniya mai suna Iya Hauwa Foundation. A sha karatu lafiya: MANHAJ: Mu fara da jin tarihinki a taƙace Sunana Hauwa Umar Aliyu. 'Yar Ƙaramar Hukumar Birniwa ce a Jihar Jigawa. Ni Bafilatana ce daga riga, saboda ban ma iya Hausa ba a lokacin da yayar Mahaifina da ke zaune a Kano ta ɗauke ni ta tafi da ni Kanon. Kafin…
Read More
Ruwan Jiki (3)

Ruwan Jiki (3)

Daga MUSTAPHA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan uwa masu karatu Assalamu alaikum. Barkanmu da wannan lokaci, barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai ilmintarwa, da ke zayyano muku bayanai game da duniyar jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu kuma ku ilmintu, kuma ku san yadda Jikinku ke aiki. Har yanzu dai muna magana akan ruwan jikin ɗan Adam. A satikan da suka gabata, na kawo yadda ruwa yake a jikin mutum, guraren da ake samun sa, da muhimman ayyukansa da tasirinsa a jikin bil adama.  Na faɗa cewa: Ruwan jikin ɗan Adam cibiya ce ta musayar sinadarai, saƙonni, da kuma…
Read More
Masarautar Wukari da Jukunawa

Masarautar Wukari da Jukunawa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Kamar dai yadda kowa ya fi saninta da suna Wukari, ta kasance hedikwatar masarautar Wukari. Asalin sunanta shi ne Ukari, wacce kuma kalma ce ta Jukunanci, wacce ke da ma’ana ta ‘ka fifita’. Masarauta ce da aka kafa ta a shekarar 1596 bayan rushewar Daular Kwararrafa. Tushe:Bayan rushewar Daular Kwararrafa wacce ke da hedikwata a Api, sai Jukunawa waɗanda su ke tun asali su ne ke shugabanta waccar daula ta Kwararrafa suka matsa gaba zuwa wannan bigire, suka kafa garin da a yanzu ake kira Wukari. Ita kuwa wannan kalma ta Wukari, asalinta shi ne Ukari,…
Read More
Babbar jikar Sardauna, Hajiya Hadiza Shehu Kangiwa ta rasu

Babbar jikar Sardauna, Hajiya Hadiza Shehu Kangiwa ta rasu

Daga IBRAHEEM HAMZA MNUHAMMAD Allah Ya yi wa Hajiya Hadiza Shehu Kangiwa, babbar jikar jikar Sardauna, Ahmadu Bello rasuwa. Aminiyar marigayiyar, Hajiya Binta Tafawa Balewa ta shaida wa Manhaja cewa, "Hajiya Hadiza Shehu Kangiwa, wacce mata ce ga marigayi tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato ta da, Alhaji Shehu Kangiwa. "Ta kasance babbar jikar marigayi Sardauna Ahmadu Bello, kuma 'yar fari ga Hajiya Inno Ahmadu Bello. "Marigayiyar ita ce 'yar marigayi Wamban Kano, Abubakar Ɗan Maje, kuma babban ɗa ga marigayi Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na 1. "An haife ta ne a shekarar 1960, ta rasu ran Talata a Sakkwato, ta bar…
Read More
Sojoji sun gasa wa mayaƙan Boko Haram/ISWAP gyaɗa a hannu a Wulgo

Sojoji sun gasa wa mayaƙan Boko Haram/ISWAP gyaɗa a hannu a Wulgo

Daga BASHIR ISAH Bayanai daga babban ofishin sojojin Nijeriya da ke Abuja, na nuni da cewa sojojin rundunar 'Operation Haɗin Kai' da ke aikin haɗin gwiwa da sojojin Kamaru a yankin Arewa-maso-gabas, sun kakkaɓe wasu mayaƙan Boko Haram da ISWAP a yankin Wulgo. Cikin wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na facebook mai ɗauke da sa hannun Daraktan Hulɗa da Jama'a na Rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, rundunar ta ce a ranar Litinin da ta gabata sojojin suka samu wannan nasarar a kan 'yan ta'addan inda suka yi fatafata da su. Sanarwar ta ce 'yan bindigar sun cimma…
Read More
Noma da kiwo ne babbar hanyar cigaba, inji Hon. Kibiya a taron ƙungiyar OWSI

Noma da kiwo ne babbar hanyar cigaba, inji Hon. Kibiya a taron ƙungiyar OWSI

Daga MUHAMMADU MUJITABA Tsohon kwamishinan al'amuran gona a Kano a 1999 zuwa 2003, Honarabul Yusuf Ado Kibiya, ya bayyana cewa, a kullum addu’a muke yi man fetur ya ƙari domin shi ne ya kawo mana koma baya a harkar noma da kiwo a Nijiriya wanda kafin man fetur, Arewa da ma Nijiriya na alfihiri da kayan gona a matsayin arzikinmu mai ɗorewa, wanda yake daga gano man fetur abun ya koma baya kuma barin noma a kama wani abu matsala ce wanda kuma wannan matsala ce babba a wajen cigaban ƙasa. Hon. Yusuf Ado Kibiya ya yi wannnan bayanin ne…
Read More
Ƙungiyar iyayen yara ta yaba wa ƙoƙarin Kwalejin Sheikh Khalifa Isyaka Rabiu

Ƙungiyar iyayen yara ta yaba wa ƙoƙarin Kwalejin Sheikh Khalifa Isyaka Rabiu

Daga MUHAMMADU MUJITABA Shugaban ƙungiyar iyayen yara da malaman makaranta na rukunonin makarantun Sheikh Khalifa Isyaka Rabiu, Alhaji Abubakar Jibrin Madigawa ya yaba wa wannan makaranta ne kan shirya wa ɗalibai 180 walimar kammala makarantu sakandire da firamare, a makarantar ƙarƙashin shugabancin babban jami’in tsare-tsare na makarantun khalifa, Malam Ibrahim Bashir Dodo kan ƙoƙarinsa na tsara irin wannan walimar irinta na farko don inganta walwala da ƙwaƙalwar ɗalibai da ƙarfafa musu gwiwa bayan kammala karatun na wannan lokaci. Shugaban ƙungiyar iyayan da malaman makarantar Abubakar Jibrin Madigawa ya bayyana haka ne a lokacin bikin walimar da makaranatar khalifa Isyaka Rabiu…
Read More
Ko mun san ma’anar Tarbiyya?

Ko mun san ma’anar Tarbiyya?

Assalamu alaikum. Tarbiyya kalma ce da ta samo asali daga Harshen Larabci. Tarbiyya wani ɓangare ne ko jigo a rayuwar ɗan Adam. Manufar Tarbiyya shine, gina mutum ya tashi cikin kyawawan halaye da ɗabi’u. Tarbiyya a Hausa na nufin, cikakken Mutum wanda ya ke da halaye da ɗabi’u masu inganci. Akan alaƙanta mutum mai nutsuwa, mai girmama na gaba, mai sanin ya kamata, mai iya kalami, mai kyakkyawar mu’amula da suna mai Tarbiyya. A taƙaice, mutum na samun cikakkiyar daraja da mutumtaka a idon jama’a idan ya kasance mai Tarbiyya. Jigon masu bada tarbiyya ga ɗan Adam su ne; Iyaye…
Read More
Ya kamata gwamnati ta waiwaye mu, cewar ƙungiyar masu sana’ar kifi

Ya kamata gwamnati ta waiwaye mu, cewar ƙungiyar masu sana’ar kifi

Daga MOHAMMED ALI GOMBE Ƙungiyar masu sana’ar kifi ta Jihar Gombe, ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta waiwaye su, ta sa su a cikin waɗanda za su mori gajiyar tallafin da za ta bai wa ‘yan kasuwa duk lokacin da tsarin bada tallafin ya taso nan gaba. Ƙungiyar wanda a turance, ana kiran ta ‘Nigeria Union Of Fish Sellers’, Gombe State Branch’ wanda kuma mambobin ta sun haura sama da mutum dubu ashirin (20, 000) a duk faɗin jihar , ta yi kukan cewa, tunda ake raba wa ‘yan kasuwa masu sana’o’i iri-iri da ke cikin jihar tallafi…
Read More
Akwai dalilanmu na shirya wa ɗaliban firamare muhawara kan Korona – Ƙungiyar CAGSI

Akwai dalilanmu na shirya wa ɗaliban firamare muhawara kan Korona – Ƙungiyar CAGSI

Daga MUHAMMADU MUJITABA Shugabar ƙungiyar CAGSI ta ƙasa da ke da ofishi a Kano, Hajiya Maryam Garba Usman ta bayyana cewa, akwai dalilai masu yawa da yasa suka shirya muhawara kan cutar korona ga ɗaliban makarantun firamare takwas da suka zaɓo daga ƙananan hukumomi huɗu a cikin ƙwaryar birinin Kano wanda aka gabatar a ranar Litinin ta makon jiya a harabar ɗakin taro na hukumar Ilimi bai ɗaya a Kano. A farko shugabar ƙungiyar ta CAGSI ta ce, ganin yadda wannan cuta ta ɓullo wa duniya a ƙarshen shekarar 2019 ta kuma mamaye duniya ya sa aka yi ta wayar…
Read More