18
Oct
Daga AMINA YUSUF ALI Barkan ku da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Manhaja. Rubutun wannan makon na maza ne! Muna tafe da bayanai a kan yadda namiji zai nema wa kansa girma da ƙima a wajen mata ko matansa har ma da 'ya'yansa. Me ya sa na ce haka? Saboda in dai har za ka samu wannan girmamawar daga matarka, lashakka za ka samu daga yaranka. Domin su yara suna kwaikwayon uwarsu ne. Ita wannan girmamawar a aure tana da matuƙar muhimmanci. Idan iyalinka ba sa girmama ka, ba za ka ji daɗin rayuwar auren yadda ya kamata…
