05
Aug
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Rundunar 'yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da yin garkuwa da mahaifi da kishiyar mahaifiyar Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Nasiru Muazu Magarya, a wani hari da 'yan bindigar suka kai a ƙauyen Magarya da ke cikin ƙaramar hukumar Zurmi a jihar Mai magana da yawun rundunar, SP Shehu Muhammd, shi me ya tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar, Hussaini Rabiu ya tura isassun jami'an tsaro da nufin ceto mutanen da aka sace. Sai dai wani mazaunin yankin mai suna Muhammadu Lawali, ya shaida wa wakilin MANHAJA ta waya…
