03
Aug
Daga WAKILINMU Maiɗakin Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar, Hajiya Titi Amina Abubakar, ta ƙaryata wani saƙo da aka yi ta yaɗawa a soshiyal midiya wanda ya shafi lissafin wasu 'yan siyasa a PDP da aka ce daga wajenta saƙon ya fito. Titi ta musanta fitowar saƙon daga wajenta, inda ta ce "Ba na amfani da shafukan sadarwa na zamani, abin da aka danganta da ni a facebook labarin ƙarya ne." Ta ce baya ga ƙaryata batun, haka nan tana shaida wa jama'a ba ta amfani da irin wannan salon wajen tura irin wannan saƙo, kuma ba ta umarci wani…
