02
Aug
Daga WAKILINMU A sakamakon gargagaɗin da sashin kula da sha'anin abinci na Majalisar Ɗinkin Duniya ya fitar ranar 29 ga Yuli game da yiwuwar fuskantar ƙarancin abinci a Arewacin Nijeriya, Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar ya ce ya zama wajibi gwamnati ta farga. Gargaɗin na Majalisar Ɗinkin Duniya wani sabon tsari ne na kwarmata bayanai wanda ya kamata Gwamnatin Tarayya ta fuskanta kasancewar Arewacin ƙasar nan shi ne yankin da galibi ke samar da abinci da ake amfani da shi a faɗin ƙasa da ma wasu sassan Afirka. Atiku ya ce halin ko-in-kula da gwamnati ke nunuwa game da…
