Editor

9513 Posts
Kotun Kano ta ɗaure ɓarawon yara shekara 104 a kurkuku

Kotun Kano ta ɗaure ɓarawon yara shekara 104 a kurkuku

Daga AMINA YUSUF ALI A Juma'ar da ta gabata Babbabar Kotun Kano ta 2, ta yanke wa Paul Owne hukuncin zaman kurkuku na shekara 104 bisa laifin kitsa sace wasu yara a jihar. Alƙalin kotun, Jastis Zuwaira Yusuf ita ce ta yanke hukuncin haka, tare da ba da umarnin garƙame Paul ba tare da wani zaɓin biyan tara ba. Haka nan, duk da yanke masa hukuncin zama a gidan gyaran hali, kotun ta kuma buƙaci Paul ya biya kuɗi har N100,000 kafin a jefa shi kurkuku. Paul dai ya amsa aikata laifuffuka 38 da lauyan mai gabatar da ƙara ya…
Read More
‘Yan bindiga sun farmaki asibitin Zamfara

‘Yan bindiga sun farmaki asibitin Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau 'Yan bindigar da suka addabi sassan jihar Zamfara sun kai hari a Babbar Asibitin da ke Ɗansadau a yankin Ƙaramar Hukumar Maru da ke jihar a Juma'ar da ta gabata. Shugaban Ƙungiyar Likitoci ta Ƙasa reshen Jihar Zamfara, Dr. Mannir Bature, shi ne ya tabbatar wa manema labarai da harin a wata sanarwa da ya fitar ran Asabar a Gusau. Dr. Bature ya ce maharan sun shigo ne da nufin kwashe likitoci da malaman jinya da ke aiki a asibitin, sakamakon bincike da aka gudanar hakan ya hana haƙarsu cim ma ruwa, sai dai sun…
Read More
Dalilin da ya sa Gwamnantin Kaduna ta sake maka El-Zakzaky a kotu

Dalilin da ya sa Gwamnantin Kaduna ta sake maka El-Zakzaky a kotu

Daga AISHA ASAS Gwamnatin jihar Kaduna ta sake shigar da sabbin tuhume-tuhume na ta’addanci da laifin ja da dokokin hukuma kan jagoran Harkar Musulunci a Nijeriya, Ibrahim El-Zakzaky. Idan ba a manta ba, a Larabar da ta gabata Babbar Kotun Kaduna ƙarƙashin Jastis Gideon Kurada ta wanke El-zakzaky da matarsa Zinat daga tuhume-tuhume guda takwas saboda rashin cancanta. Sai dai da alama hukuncin da kotun ta yanke bai gamsar da gwamnatin Kaduna ba wanda hakan ya sa tuni ta sake shirya wasu sabbin tuhume-tuhume guda bakwai a kan El-Zakzaky a Babbar Kotun Tarayya a Alhamis da ta gabata. Daraktan Gabatar…
Read More
Ganduje ya amince da kashe Naira miliyan 160 don gina ofishin ‘yan sanda a Getso

Ganduje ya amince da kashe Naira miliyan 160 don gina ofishin ‘yan sanda a Getso

Daga WAKILINMU A matsayin wani mataki na matse ƙaimi game da yaƙi da 'yan ta'adda da harkokinsu, masu garkuwa da mutane da sauran muggan laifuka a jihar Kano, Gwamnan Jihar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ba da kwangila ta Naira milyan 160 domin gina ofishin 'yan sanda irin na zamani a yankin Ƙaramar Hukumar Gaya da ke jihar. Ofishin wanda bayan kammalawa za a zuba masa ingantattun kayan aiki na zamani, an ɗauki matakin gina shi ne don daƙile matsalolin 'yan ta'adda a jihar da kuma kwararar masu aikata manyan laifuka daga wasu jihohi zuwa Kano. Idan dai za a…
Read More
Za a yi wa yara milyan 3 rigakafin shan-inna a Kano

Za a yi wa yara milyan 3 rigakafin shan-inna a Kano

Daga HAMISU IBRAHIM Yara 'yan ƙasa da shekara 5 su sama da miliyan uku ake sa ran za a yi wa rigakafin cutar shan inna (polio) da sauran cututtuka masu kassara yara ƙanana a jihar Kano daga ran 31 ga Yuli zuwa 3 ga Agustan 2021. Wannan bayanin ya fito ne daga bakin Kwamishinan Lafiya na Jihar, Dr Aminu Tsanyawa, sa'ilin da yake jawabi a wajen taron bita tare da 'yan jarida a Kano game da shirin yaƙi da cutar. Dr. Aminu wanda Babbar Sakatariya Amina Aliyu Musa ta wakilta a wajen taron, ya ce za a gudanar da yaƙi…
Read More
El-Zakzaky: Aikin gama ya gama, cewar lauya

El-Zakzaky: Aikin gama ya gama, cewar lauya

*Sarƙaƙiyar da ke cikin shari’ar*Za mu ɗaukaka ƙara, inji Gwamnatin Kaduna*Mu diyya za mu nema, cewar ’yan Shi’a*Bulandar da ta sa kotu sakin malamin Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja An bayyana cewa, hukuncin da Babbar Kotun Jihar Kaduna ta yanke game da shari’ar da aka gudanar kan jagoran ƙungiyar ’yan uwa Musulmi ta IMN, wacce a ke kira da ’yan Shi’a, wato Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, ba za a iya sake ta ba. Don haka aikin gama ya gama. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin wani }wararren lauya mazaunin Kano, Barista Nazir Adam, wanda ya ce, bisa la’akari da…
Read More
Ƙwaƙwalwar ɗan’adam (2)

Ƙwaƙwalwar ɗan’adam (2)

Daga MUSTAFA IBRAHIM ABDULLAHI 'Yan uwa masu karatu assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkanmu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo mu ku bayanai game da jikin ɗan adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Barkanmu da Sallah! Fatan Allah ya maimaita mana,  Amin.A satin da ya wuce, na kawo wasu daga cikin baiwar da Ubangijin halittu ya yi wa ƙwaƙwalwar ɗan Adam.  Yau kuma in sha Allah za mu ga yadda ƙwaƙwalwar take a siffa, da kuma wasu daga cikin ayyukanta. Ƙwaƙwalwar mutum guda ɗaya ce amma tana da ɓangarori uku.…
Read More
Makarantun tsangaya (Almajirci) gyars kaɗan suke buƙata ba haramta su ba

Makarantun tsangaya (Almajirci) gyars kaɗan suke buƙata ba haramta su ba

Daga ABUBAKAR SANI Karatun tsangaya wani irin karatu ne wanda ake yi a makaratun koyar da addinin musulunci a ƙasar Hausa shekaru da dama da suka wuce. Karatun ana yin sa ne ta hanyar yin rubutu a allo da kuma alƙalami. Ma fi yawan waɗanda suke yin wannan karatun su ne suke ciyar da kansu ta hanyar yin bara domin su samu abinci. Masu yin wannnan karatun yawancin su karatun Alƙur'ani kaɗai suke yi babu ruwansu da karatun boko. Haka kuma ma fi yawancin su ba su cika yin sana'a ba sai dai bara, wanda ake kira da almajiranci. A…
Read More
Taɓarɓarewar surukuta a ƙasar Hausa: Ina Mafita?

Taɓarɓarewar surukuta a ƙasar Hausa: Ina Mafita?

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanmu da jimirin karatun jaridarku mai farin jini ta Manhaja.  Za mu ci gaba daga inda muka tsaya a kan dalilan da suke kawo lalacewar alaƙa tsakanin surukai, ta yadda surukuta a ƙasar Hausa ta zama kamar gaba a tsakaninsu. Kowa kishi da hassada yake wa ɗanuwansa. Ga rainin wayo, abin ba a magana. A wancan makon mun kawo wasu daga cikin dalilan da suka sa hakan take faruwa domin masu karatu su yi al}alanci su gano wai shin ma laifin wanene? To a yanzu za mu ci gaba da kwararo muku bayani a kan wasu…
Read More
Me ya sa Gwamnatin Tarayya ke son jihohi su kashe mutum 3,008?

Me ya sa Gwamnatin Tarayya ke son jihohi su kashe mutum 3,008?

Daga NASIR S. GWANGWAZO A ranar Juma’a, 23 ga Yuli, 2021, ne dai Ministar Kula da Harkokin Cikin Gida na Nijeriya, Alhaji Rauf Aregbesola, ya yi kira ga gwamnonin jihohin ƙasar daban-daban da su gaggauta sanya hannu kan hukunce-hukuncen kotuna a faɗin tarayyar ƙasar na hukuncin kisa kan waɗanda a yanzu haka su ke jiran a aiwatar mu su da hukunci. Ministan, wanda ya ke magana a Osogbo, Babban Birnin Jihar Osun, lokacin da ya ke ƙaddamar da sabon ginin gidan gyaran hali a jihar, ya ce, akwai kafatanin mazauna gidajen yari kimanin 3,008, da ke jiran a aiwatar mu…
Read More