Editor

9513 Posts
Har yanzu makarantu 10 na rufe saboda matsalar tsaro a Neja – Kwamishina

Har yanzu makarantu 10 na rufe saboda matsalar tsaro a Neja – Kwamishina

Kwamishinar Ilimi ta Jihar Neja, Hanatu Jibrin Salihu, ta bayyana cewa har yanzu makarantu 10 daga cikin makarantun sakandare na kwana guda 56 da ake da su a jihar Neja na ci gaba da kasancewa a rufe saboda matsalar 'yan bindiga, tare da cewa 'yan aji shida na makarantun da lamarin ya shafa an sahale musu rubuta jarrabawar kammalawa a wasu makarantu. Kwamishinar ta bayyana hakan ga manema labarai ne jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwa a Alhamis da ta gabata a Minna, babban birnin jihar. Ta ce 25 daga cikin makarantu suna aiki, kana ɗaliban makarantun da ke…
Read More
INEC ta fitar da jadawalin ranakun rajistar masu zaɓe

INEC ta fitar da jadawalin ranakun rajistar masu zaɓe

Daga WAKILINMU Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana ranaku da abubuwan da za a yi dangane da rajistar masu jefa ƙuri'a da ake gudanarwa a yanzu. Idan kun tuna, an fara aikin ne daga ranar 28 ga Yuni, 2021 kuma za a ci gaba da yin sa har zuwa ranar 11 ga Yuli, 2022. A sanarwar da sashen yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe na hukumar ya fitar, an nuna cewa za a yi aikin a watanni uku na farko da watanni uku na biyu na wannan shekarar da mu ke ciki. A baɗi kuma za a…
Read More
Dakta Maryam Ibrahim Shettima: A mahangar gwagwarmaya da kishin ƙasa

Dakta Maryam Ibrahim Shettima: A mahangar gwagwarmaya da kishin ƙasa

Daga BASHIR ABDULLAHI EL-BASH Tun farkon kafuwar Duniya har zuwa yau, a cikin kowane ƙarni, a ciikin kowace al'umma, a kowane zamani, Allah Ya na fito da wasu mata 'yan gwagwarmaya da su ke taimakon al'umma, Allah Ya bayyanar da Hajiya Maryam Shetty a wannan zamani namu. A fannin gwagwarmayar siyasa da ba da gudunmawa ga masu mulki, Hajiya Maryam Shetty ta na kamanceceniya da Sarauniya Raziya Shamsuddeen Iltutmish, wacce ta rasu shakaru 780 da suka gabata. Jarumar Mace ce wacce ta gaji mahaifinta a Birnin Delhi lokacin Indiya da Pakistan na haɗe, ta taimaki shugabancin Mahaifinta a sarari da…
Read More
Shin ragwanci ke haddasa ta’addanci?

Shin ragwanci ke haddasa ta’addanci?

Daga NASIR ADAMU EL-HIKAYA Da mamaki ainun a iya zayyana 'yan ta'adda da ragwage don ko banza suna himma wajen aikata miyagun ayyuka. Wasunsu ma ba sa barci ido biyu rufe ko kuma su kan sha ƙwaya a yawanci lokuta don kar barci ko kasala ta ɗauke su wasu abokan hamayya ko ma jami'an tsaron gwamnati su cim masu. Kazalika, wasu mutanen kan iya zama ragwage a wasu lamuran da ba sa ƙauna ko son zuciyar su ya saɓa da abun da a ke so su yi na addini ko al'ada. Misali a nan kamar tafiya masallaci don sallah, gaida…
Read More
Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa sun sha rantsuwar kare sirri

Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa sun sha rantsuwar kare sirri

Daga UMAR M. GOMBE Babban Sakataren Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, Tijjani Umar, ya gargaɗi ma'aikatan Fadar kan cewa bayyana wa duniya bayanan sirrin Fadar Shugaban Ƙasa ba tare da izinin hukuma ba laifi ne babba wanda ke tattare da hukunci ga duk wanda aka kama ya aikata hakan kamar yadda yake ƙunshe cikin dokokin aikin gwamnati. Umar ya wannan gargaɗi ne a lokacin da yake rantsar da ma'aikata masu kula da muhimman bayanai a Fadar Shugaban Ƙasa a Talatar da ta gabata. Ya ce, "Sakamakon sauya wa jami'ai wurin aiki da kuma murabus da wasunsu suka yi, ya…
Read More
Sufeto-Janar ya yi wa manyan jami’an ‘yan sanda 24 sauyin wajen aiki

Sufeto-Janar ya yi wa manyan jami’an ‘yan sanda 24 sauyin wajen aiki

Daga AISHA ASAS A matsayin wani mataki na ƙoƙarin bunƙasa jami'an 'yan sandan Nijeriya, Babban Sufeton 'Yan Sanda, IGP Usman Alkali Baba, ya amince da sauya wajen aiki ga Mataimakan Sufeto Janar su 24 zuwa ofisoshin shiyya. Sanarwar da Mai Magana da Yawun Rundunar na Ƙasa, CP Frank Mba, ya fitar a ranar Talata ta nuna yadda IGP ya bai wa ƙasa tabbacin cewa sauye-sauyen wurin aikin da aka yi wa manyan jami'an hakan zai taimaka gaya wajen ƙarfafa wa rundunar ci gaba da sauke nauyin da ya rataya a kanta wajen yi wa ƙasa hidima yadda ya kamata. Mba…
Read More
An kafa dokar hana fita a Balanga saboda rikicin ƙabilanci

An kafa dokar hana fita a Balanga saboda rikicin ƙabilanci

Daga WAKILINMU A Talatar da ta gabata Gwamnatin Jihar Gombe ta kafa dokar hana zirga-zirga na sa'o'i 24 a wasu ƙauyukan jihar da suka haɗa da Nyuwar, Jessu, Heme, Yolde Gelentuku, Sikam, Wala-Lunguda da kewaye. Matakin sanya dokar ya biyo bayan sabon rikicin ƙabilancin da ya ɓarke ne tsakanin ƙabilar Lunguda da Waja da ke yankin Ƙaramar Hukumar Balanga ran Talata. Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, shi ne ya ba da sanarwar kafa dokar, tare da cewa buƙatar kafa dokar ta taso ne don dawo da zaman lafiya a yankunan da rikicin ya shafa. Ya ce tuni an…
Read More