Editor

9513 Posts
Majalisa ta ƙara wa’adin sa’o’i 48 ga Mataimakin Gwamnan Zamfara ya bayyana a gabanta

Majalisa ta ƙara wa’adin sa’o’i 48 ga Mataimakin Gwamnan Zamfara ya bayyana a gabanta

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta tsawaita wa'adi da sa'o'i 48 ga Mataimakin Gwamnan Jihar Barr. Mahdi Aliyu Muhammad Gusau, ya bayyana a gabanta don amsa tambayoyi kan zargin aikata ba daidai ba. Hakan ya biyo bayan ƙudirin da Mataimakin Shugaban Jagoran Majalisar, Hon. Nasiru Bello lawal Bungudu ya gabatar a kan lamarin wan Hon Shafi'u Dama Wanke mai wakiltar mazaɓar Gusau ta biyu (2) a Majalisar ya mara wa baya. Idan dai za a iya tunawa, ƙudurin da Majalisar ta yanke a ranar Laraba 14 ga watan Yulin 202, ta yanke shawarar gayyatar Mataimakin Gwamnan…
Read More
Gazawa ce idan APC ta jajubo Jonathan a 2023 – Hon. Tasiu Danhajiya

Gazawa ce idan APC ta jajubo Jonathan a 2023 – Hon. Tasiu Danhajiya

Daga NASIR S. GWANGWAZO An bayyana cewa, ba ƙaramar gazawa ba ce ga jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya matuƙar ta yi kuskuren bai wa tsohon Shugaban Nijeriya, Dr. Goodluck Ebele Jonathan, takara a lokacin Babban Zaɓen shekara ta 2023 da ke tafe. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin Hon. Tasiu Sani Danhajiya, Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano da Kewaye kuma ɗan jam’iyyar APC. Idan dai za a iya tunawa, rahotanni na nuni da cewa, akwai wani tsari a ƙarƙashin ƙasa da ake yi tsakanin wasu jiga-jigan APC daga Arewacin Nijeriya na dawowar Mista Jonathan cikin…
Read More
Babbar Kotun Tarayya ta tafi hutu

Babbar Kotun Tarayya ta tafi hutu

Daga WAKILINMU A Litinin da ta gabata Babbar Kotun Tarayyar Nijeriya ta soma hutunta na shekara-shekara da ta saba tafiya. Cikin wata sanarwa wadda Babban Rajistaran kotun, Mr Emmanuel Gakko ya sanya wa hannu, hutun kotun zai ƙare ne a ranar 17 ga Satumba, sannan ta soma aiki ran 20 ga Satumba. A cewar Gakko, wasu kotuna a yankin Abuja da Legas da Fatakwal za su ci gaba da aiki domin sauraren ƙararrakin gaggawa a yayin da Babbar Kotun ke shan hutunta. Ya ƙara da cewa, duk masu buƙatar shigar da ƙara na iya yin hakan ta hanyar ziyartar kotu…
Read More
Majalisar Dokokin Kano ta buƙaci Ganduje ya sauke Muhyi

Majalisar Dokokin Kano ta buƙaci Ganduje ya sauke Muhyi

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Majalisar Dokokin jihar Kano, ta buƙaci Gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da ya sauke dakataccen shugaban Hukumar Karɓar Ƙorafi da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhyi Magaji Rimin Gado. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna majalisar ta buƙaci gwamnan ya ɗauki matakin ne bayan da kwamitinta na wucin-gadi da ta ɗora wa aikin gudanar da bincike kan ƙorafin da ofishin babban akantan jihar Kano ya shigar gaban Majalisar a kwanakin baya. Kazalika, ta ce yayin zaman Majalisar na yau Litinin, kwamitin ya gabatar wa Majalisar rahotonsa inda a ciki ya…
Read More
Bidiyo: Mamakon ruwan sama ya haifar da ambaliya a Keffi

Bidiyo: Mamakon ruwan sama ya haifar da ambaliya a Keffi

Daga BASHIR ISAH Sakamakon mamakon ruwan saman da aka samu a garin Keffi, jihar Nasarawa, hakan ya haifar da ambaliya a wasu sassan garin. Ruwan saman wanda aka soma da asubahin yau Litinin, an shafe sama da sa'o'i biyar ana tafkawa. Daga cikin wuraren da aka samu aukuwar ambaliyar har da fitacciyar gadar nan ta Antau, wadda ta cika ta batse da ruwa ta yadda ma amfani da ita ya gagari jama'a. Bayanan da Manhaja ta tattaro sun nuna ambaliyar Gadar Antau ta shafi wasu gidaje da ke yankin tare da lalata kayayyaki da dama amma ba a samu hasarar…
Read More
Fasahar marubuta waƙoƙin Hausa

Fasahar marubuta waƙoƙin Hausa

Daga AISHA ASAS Waƙa: HANKALITare da Khalid lmam Hankali gatan tunani,Jagora ne gare shi,Mai yin saiti wajen shi. Shi doki ban da shakka,Hawa nasa ko ga sarki,Sai da linzami ku lura. Shi tunani na fahimta,Yafi mai saƙa a tufka,Shi ka saƙa ko ya tufka. Hankali in ka yi dace,Shi kasa shi idan ya saƙa,Sai ya tufke in da khairan. In ba khairan a saƙar,Sai ya kunce ba hiyana,Saƙarsa ya ce ya sake. Hankali tsanin tunani,Shi hawa sama ko ga dogo,In da tsani yafi tabbas. Mai tunani mai basira,Hankali na taimakonsa,Rami ya gani ya kauce. Hankali baiwa ga Bawa,Shi kasa Bawa…
Read More
Yau Buhari zai tafi London

Yau Buhari zai tafi London

Daga UMAR M. GOMBE A wannan Litinin ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya tafi Landon don halartar wani babban taro na duniya kan batun ilimi, wato Global Partnership for Education (GPE) na 2021 zuwa 2025. Hadimin Buhari kan sha'anin yaɗa labarai, Mr. Femi Adesina, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar a safiyar Litinin. A cewar Adesina, taron wanda na haɗin gwiwa ne tsakanin Firam Ministan Birtaniya da Shugaban Ƙasar Kenya, Uhuru Kenyatta, ana sa ran ya haɗa kawunan shugabannin ƙasashen duniya da gwamnatoci da masu ruwa da tsaki har ma da…
Read More
Hoto: Yadda jana’izar Bantex ta gudana a Kaduna

Hoto: Yadda jana’izar Bantex ta gudana a Kaduna

A wannan Lahadin aka gudanar da jana'izar tsohon mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Architect Barnabas Yusuf Bala da aka fi sani da Bala Bantex. Jana'izar ta samu halartar manyan baƙi na kusa da nesa, 'yan siyasa, jami'an gwamnati da sauransu. Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai na daga cikin waɗanda suka halarci jana'izar, wanda bayan kammalawa ya nuna godiyarsa a madadin Gwamnatin Kaduna ga ɗaukacin waɗanda suka halarci jana'izar kamar dai yadda ya wallafa a shafinsa na facebook.
Read More
An tsawaita wa’adin shirin sadar da lambar shaidar ɗan ƙasa da layukan sadarwa zuwa Oktoba

An tsawaita wa’adin shirin sadar da lambar shaidar ɗan ƙasa da layukan sadarwa zuwa Oktoba

Daga AISHA ASAS Gwamnatin Tarayya ta ƙara wa’adin shirin shigar da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) cikin bayanan mallakar layin waya (SIM) ya zuwa 31 ga Oktoban 2021. Gwamnati ta bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ta sami sa hannun manyan jami’ai biyu, wato Dr. Ikechukwu Ainde na Hukumar Sadarwa ta Nijeriya da kuma Mr Kayode Adegoke na Hukumar Kula da Shaidar Ɗan Ƙasa. Sanarwar ta ce an ɗauki matakin tsawaita wa’adin shirin ne sakamakon buƙatar hakan da masu ruwa da tsaki suka nuna domin bai wa shirin damar kaiwa ga jama’ar da ke gefen birane, baƙi mazauna ƙasa…
Read More