Editor

9513 Posts
Bayan kwana 42, an ceto mutum 100 da aka yi garkuwa da su a Zamfara

Bayan kwana 42, an ceto mutum 100 da aka yi garkuwa da su a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau. Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar ƙarƙashin Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar, ta samu nasarar kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su kimanin su 100 ba tare da wani sharaɗi ba waɗanda aka sace daga ƙauyen Manawa na Gundumar Mutunji da ke cikin masarautar Ɗansadau ta ƙaramar hukumar Maru a jihar. Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar, SP Muhammad Shehu ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Gusau ranar Laraba. Ya ƙara da cewar, waɗanda aka Yi garkuwan da…
Read More
Bikin Sallah: Yadda mutum 10 suka mutu a haɗarin mota a Kwara

Bikin Sallah: Yadda mutum 10 suka mutu a haɗarin mota a Kwara

Daga WAKILINMU Hukumar Kula da Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) reshen jihar Kwara, ta ba da bayanin wasu mutum 10 sun rasu sakamakon mummunan haɗarin da ya rutsa da su. Shugaban FRSC na Kwara, Mr Jonathan Owoade, shi ne ya tabbatar da aukuwar haɗarin ga manema labarai a Ilorin babban birnin jihar. Owoade ya ce haɗarin ya rutsa da wata mota ce ƙirar Toyota Hiace mai lamba LND 742 XK, a hanyar Oko Olowo/Oloru da ke yankin Iyemoja a Ilorin sakamakon gudun wuce misali da direban motar ya yi wanda hakan ya saɓa wa dokokin tuƙi. Haɗarin wanda ya yi ajalin…
Read More
Har yanzu Igboho na hannun hukuma a Kwatano

Har yanzu Igboho na hannun hukuma a Kwatano

Daga AISHA ASAS Saɓanin rahotannin da suka karaɗe sassa kan cewa an saki jagoran gwagwarmayar kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho wai har ya keta hazo zuwa ƙasar Jamus, bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna wannan ba gaskiya ba ne, saboda ya zuwa haɗa wannan labari Igboho na can tsare a hannun jami'an tsaro a Kwatano. Farfesa Wale Adeniran wanda shugaba ne na wata ƙungiyar Yarabawa, shi ne ya ta babbatar da cewa har yanzu Igboho na hannun hukuma a ƙasar Benin yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a dandalin zoom…
Read More
An kai wa Shugaban Ƙasar Mali hari a masallacin idi

An kai wa Shugaban Ƙasar Mali hari a masallacin idi

Daga WAKILINMU Bayanan da Manhaja ta samu da rana nan daga ƙasar Mali, sun nuna an kai wa Shugaban Ƙasar, Assimi Goïta, hari a masallacin idi yayin sallar Idul Kabir a yau. Wasu mutum biyu ne ɗauke da wuƙa suka kai wa shugaban hari a masallacin idi na Bamako, babban birnin ƙasar. Sai dai ya zuwa haɗa wannan rahoto, babu cikakken bayani kan ko shugaban ya ji rauni sakamakon harin, amma an yi nasarar ɗauke shi daga wurin. Idan ba a manta ba Colonel Goita shi ne wanda ya jagoranci juyin mulkin da ya faru a ƙasar a Agustan bara…
Read More
Barka da Sallah: Matawalle ya jaddada alƙawarin magance matsalar tsaro a Zamfara

Barka da Sallah: Matawalle ya jaddada alƙawarin magance matsalar tsaro a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na magance matsalolin rashin tsaro da ke addabar jihar sakamakon ayyukan 'yan fashin daji don maido da zaman lafiya a jihar. Gwamnan ya bayyana hakan ne ran jajibirin Babbar Sallah a wata sanarwa da ya gabatar ga al'ummar jihar kan bikin Idul Kabir na bana. A cewarsa, ƙalubalen rashin tsaron gwamnatinsa ta gaje shi ne daga tsohuwar gwamnati da ya gada shekaru biyu da suka gabata, yana mai jaddada cewa shirin sasanci, zaman lafiya da tattaunawa game da batun sulhu a tsakanin masu tayar da…
Read More
Bikin Sallah: Bukola Saraki ya yi wa ‘yan Nijeriya nasiha

Bikin Sallah: Bukola Saraki ya yi wa ‘yan Nijeriya nasiha

Daga WAKILINMU Tsohon Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya a Majalisa ta tara, Dr. Abubakar Bukola Saraki, ya taya ɗaukacin al’ummar Musulmi murnar zagayowar idin babbar sallah ta wannan shekara, inda ya yi kira ga musulmin Nijeriya da su ci gaba da jin tsoron Allah, don shi ne sinadarin bunƙasar ƙasa. Saraki ya bayyana haka ne a saƙon barka da sallah da ya fitar yau a garin Ilorin ta Jihar Kwara, wanda ke ɗauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Yusuph Olaniyonu. Ya ce, kamar dai shekarar da ta gabata, idin babbar sallah ta wannan shekara ma za…
Read More
Igboho ya faɗa a komar hukuma

Igboho ya faɗa a komar hukuma

Daga WAKILINMU Jami'an tsaro sun cafke jagoran fafutIkar ƙwatar wa Yarabawa 'yanci, Sunday Adeyemo wanda aka fi sani da Sunday Igboho. An cafke Igboho ne jiya Litinin da daddare a Kwatano da ke Tarayyar Benin yayin da yake ƙoƙarin tsallakewa ya bar Afirka. Wata majiya mai tushe ta bayyana cewa, Igboho ya bar Nijeriya zuwa Kwatano ne saboda shirin da yake da shi na sulalewa daga Afirka zuwa ƙasar Jamus don tsoron kamun hukuma amma ya zamana haƙarsa ba cim ma ruwa ba. Ya zuwa haɗa wannan labari, jami'an tsaron da ke riƙe da Igboho na shirye-shiryen dawo da shi…
Read More
Za mu iya tattara sakamakon zaɓe ta amfani da fasahar zamani – INEC

Za mu iya tattara sakamakon zaɓe ta amfani da fasahar zamani – INEC

Daga WAKILINMU Duk da ra'ayin da wasu 'yan majalisun tarayya suka yi kan cewa batun tattara sakamakon zaɓe ta hanyar amfani da fasahar zamani abu ne da ba zai yiwu ba saboda rashin hali ta ɓangaren Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) da kuma rashin wadatar netiwoki a wasu sassan ƙasa, sai ga shi Asabar da ta gabata aka ji INCE ɗin ta fito ta bayyana cewa lallai tana da halin da za ta attaro sakamakon zaɓe daga sassan ƙasa baki ɗaya ta hanyar amfani da fasahar zamani. Tun farko, sai da 'yan majalisun tarayya suka tafka zazzafar muhawara kan wannan…
Read More
Buhari ya ƙaddamar da shirin bunƙasa harkokin noma (NALDA) a Daura

Buhari ya ƙaddamar da shirin bunƙasa harkokin noma (NALDA) a Daura

Shirin buƙasa harkokin noma na ƙasa ko kuma Agricultural Land Development Authority (NALDA) a Turance, shi ne irin sa na farko da aka ƙaddamar a Nijeriya. A wannan Litinin Shugaba Buhari ya ƙaddamar da shirin a mahaifarsa Daura da ke jihar Katsina, kamar yadda hadimin Buhari kan sha'anin sabbin kafafen yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na facebook.
Read More