Editor

9513 Posts
Buhari ya tsumu da ta’azzarar watsi da filayen noma a Nijeriya

Buhari ya tsumu da ta’azzarar watsi da filayen noma a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar jajiberen Babbar Sallah, wato Litinin ɗin da ta gabata, ne Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana tsumuwarsa da mamakinsa ga yadda aka bar filayen noma baja-baja ba tare da an nome su ba a faɗin ƙasar. A cewar Shugaban, kimanin kashi biyu da rabi kacal ce a cikin ɗari na ƙasar Najeriya aka nome. Shugaban ya bayyana hakan ne a gidansa da ke garin Daura na Jihar Katsina.  jim kaɗan bayan saukowa daga idin babbar sallar nan. Shugaban ya ƙara da kira ga al'ummar Najeriya da su ƙara ƙanƙame sana'ar noma hannu bi-biyu. Babban…
Read More
Makomar Arewa ta fi 2023, inji Gwamna Matawalle

Makomar Arewa ta fi 2023, inji Gwamna Matawalle

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Muhammad Bello, Matawallen Muradun, ya bayyana cewa, lokaci ya yi da ’yan Arewa za su dawo su yi wa kansu karatun ta-natsu, a ajiye ƙiyayya da hassada da kwa]ayi da tsoro tsakanin juna, a fuskanci babba barazanar da ke ƙara raba makomar yankin na Arewa; wato sha'anin tsaro, talauci da lalaci, ba wai batun manyan zaɓukan 2023 ba da ba su zo ba. Haka nan ya ce, dattawan Arewa da masu riƙe da madafun iko da ke ganin su ne sitiyarin samar da ci gaba ko makoma ga ’yan Arewa suna da…
Read More
Haɗarin mota ya ci mutum 5 a Neja

Haɗarin mota ya ci mutum 5 a Neja

Daga BASHIR ISAH An samu aukuwar mummunan haɗari a safiyar Alhamis a babbar hanyar Lambata zuwa Kwakuti da ke yankin ƙaramar hukumar Gurara a jihar Neja wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutum 5 da jikkata mutum 3. Wasu da lamarin ya auku a gabansu sun bayyana cewa, haɗarin ya auku ne sakamakon taho-mu-gama da aka yi tsakanin wata Golf 3 mai lamba KTU 506BK da kuma Salon Mazda 326 mai fenti ruwan ɗorawa, wanda duka motocin biyu na kasuwa ne. Kazalika, sun ce haɗari na da nasaba da ruwan saman da aka samu a yankin da kuma yadda motocin suke…
Read More
Chaina ta soma aikin shimfiɗa bututun mai daga Nijar zuwa Benin

Chaina ta soma aikin shimfiɗa bututun mai daga Nijar zuwa Benin

Daga WAKILINMU Da alama Nijeriya ta rasa damar samun kwangilar bilyoyin Dala na aikin shimfiɗa bututun mai da ƙasar Chaina ta ɗauri aniyar aiwatarwa bayan da masu zuba jari na Chaina suka sauya ra'ayin karkatar da akalar kwangilar zuwa maƙwabciyar Nijeriya, wato Nijar. Bayanai sun nuna Kamfanin China Petroleum Pipeline Engineering Co. Ltd. (CPP) wanda ɓangare ne na Kamfanin Fetur na Ƙasar Chaina (CNPC), ya soma aikin shimfiɗa bututun mai wanda za a riƙa tura ɗanyen mai daga Tarayyar Nijar zuwa matattarar mai da ke Seme-Krake a ƙasar Benin. Bayanai sun ce aikin wanda ya samu tsaiko na wasu watanni…
Read More
Buhari ya tabbatar da sauke Hadiza Bala-Usman a matsayin shugabar NPA

Buhari ya tabbatar da sauke Hadiza Bala-Usman a matsayin shugabar NPA

Daga AMINA YUSUF ALI Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar da sauke Hajiya Hadiza Bala-Usman a matsayin Shugabar Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Nijeriya (NPA). Buhari ya tabbatar da hakan ne a ranar 12 ga Yuli cikin wata takardar kotu a Legas sakamakon ƙararar da babban jami''i na kamfanin Maritime Media Limited, Asu Beks, ya shigar a kansa da kuma wasu mutum biyu. Ƙarar mai ɗauke da lamba FHC/L/CS/485/2021, wanda ya shigar da ita ya ƙalubalanci ikon da Buhari ke da shi na kafa hukumar gudanarwa na NPA tare da ɗora babban darakta ba a bisa dokar NPA ba. Kazalika,…
Read More
Masarautar Uke ta naɗa Kola a matsayin Kuyambana Babba

Masarautar Uke ta naɗa Kola a matsayin Kuyambana Babba

Daga BASHIR ISAH A matsayin wani mataki na ci gaba da ƙarfafa wa matasa wajen yi wa al'umma hidima, Masrautar Uke da ke yankin ƙaramar hukumar Karu a jihar Nasarawa, ta naɗa Mr Slomon Aliyu Kola (FCIA) a matsayin Kuyambana Babba na masarautar. Naɗin Kuyanmbana Babba ya gudana ne a fadar Maimartaba Sarkin Uke, Alh. Dr. Ahmed Abdullahi Hassan (KOBA) (Yakanajen Uke) a ranar Larabar da ta gabata. Da yake jawabi yayin naɗin, Sarkin Uke, Alh. Dr. Ahmed Abdullahi Hassan, ya ce masarautarsa a shirye take ta tafi tare da duk wani mai son cigaban al'umma ba tare da la'akari…
Read More
Brisbane ta samu gurbin ɗaukar nauyin Wasannin Olympic na 2032

Brisbane ta samu gurbin ɗaukar nauyin Wasannin Olympic na 2032

Daga UMAR M. GOMBE Kwamitin Shirya Wasannin Olympic na Ƙasa da Ƙasa ya bayyana birnin Brisbane na ƙasar Australia a matsayin birnin da zai ɗauki nauyin gudanar da Wasannin Olympic na 2032. Da wannan sasarar da Brisbane ya samu, ya sanya Australia ta zama ƙasa ta biyu a duniya bayan ƙasar Amurka da suka samu damar ɗaukar nauyin gudanar da Wasannin Olympic fiye da sau biyu a birane daban-daban. Da farko, Australia ta soma ɗaukar nauyin Olympic ne a Melbourne a 1956, sannan Sydney a 2000, sai kuma na ukun kenan ake sa ran gudanarwa a Brisbane ya zuwa 2032.…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe basarake, sun ƙona gidaje 50 a Binuwai

‘Yan bindiga sun kashe basarake, sun ƙona gidaje 50 a Binuwai

Daga BASHIR ISAH Wasu 'yan bindiga da ba a kai ga gano ko su wane ne ba sun kai wa yankin ƙaramar hukumar Oju na jihar Binuwai hari inda suka halaka sarkin ƙauyen Ochoro, Chief Okpe Denis Ijoko. Bayanai sun nuna baya ga kashe Sarki Ijoko, 'yan bindigar sun kuma ƙona gidaje sama da 50 tare da lalata ɗimbin dukiyoyi a ƙauyen a Ukpute yayin harin. Sai dai ya zuwa haɗa wannan labari, da aka nemi jin ta bakin Jami'ar Hulɗa da Jama'a ta 'Yan Sandan Jihar, Anene Sewuese Catherine, ta ce labarin harin bai riga ya iso gabansu ba.…
Read More