Editor

9513 Posts
NAF ta tabbatar da faɗiwar jirgin samanta a Zamfara, an ceto matuƙin jirgin

NAF ta tabbatar da faɗiwar jirgin samanta a Zamfara, an ceto matuƙin jirgin

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya (NAF), ta tabbatar da faɗuwar jirgin samanta (Alpha Jet) a Zamfara wanda aka ce yana kan hanyarsa ta dawowa daga aikin shawo kan matsalar tsaro a tsakanin iyakokin Zamfara da jihar Kaduna ƙaddara ta faɗa masa. Daraktan Hulda da Jama'a da Yada Labarai na Rundunar Sojin Sama ta Nijeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai ran Litinin a Gusau kuma wadda Manhaja ta mallaki kwafinta. Jami'in ya ce lamarin ya faru ne a ranar 18 ga watan Yuli,…
Read More
Dalilan tsaro sun tilasta wa Masarautar Zazzau soke hawan Sallah

Dalilan tsaro sun tilasta wa Masarautar Zazzau soke hawan Sallah

Daga ABBA MUHAMMAD, a Kaduna Masarautar Zazzau a Jihar Kaduna, ƙarƙashin jagorancin Maimartaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu, ta bayyana soke hawan Babbar Sallah yayin bikin Idul Kabir na bana. Masarautar ta bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ta sami sa hannun Sakatarenta, Alhaji Barau Musa Aliyu (Sarkin Fulanin Zazzau). Tana mai cewa an soke hawan ne saboda dalilai na halin tsaro da kuma al'amarin cutar korona. ASanarwar ta ce an cim ma matsayar soke hawan ne yayin wani taro da majalisar masarautar ta gudanar. Sai dai masarautar ta bai wa jama'arta damar gudanar da Sallar Idi a dukkanin…
Read More
Bikin Babbar Sallah: Masarautar Kano ta soke hawan daushe saboda korona

Bikin Babbar Sallah: Masarautar Kano ta soke hawan daushe saboda korona

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Majalisar Masaurautar Kano ta ce ba za a gudanar da hawan Sallah ba yayin bikin Babbar Sallah na bana. Majalisar ta ce an soke hawan ne domin cika umarnin gwamnati wajen yaƙi da cutar korona duba da cewa cutar ta kunno kai a karo na uku. Madakin Kano, Alhaji Yusuf Nabahani ne ya sanar da hakan a wannan Litinin a  Kano. Alhaji Yusuf ya ce Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, shi ne ya ba da umarnin a sanar da batun soke hawan ga masu ruwa da tsaki na masarautar.Manhaja ta ruwaito Kwamitin Shugaban Kasa…
Read More
Yahaya ya miƙa saƙon goron sallah ga sojoji da iyalansu

Yahaya ya miƙa saƙon goron sallah ga sojoji da iyalansu

Daga AISHA ASAS Shugaban Sojojin Nijeriya, Lieutenant General Farouk Yahaya, ya miƙa saƙon taya murnar bikin Babbar Sallah ga sojojin Nijeriya da iyalansu. Cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu, Yahaya ya ce, "Ina farin cikin taya ɗaukacin sojojin Nijeriya da iyalansu murnar bikin Babbar Sallar 2021." Ya ce bikin Babbar Sallah lokaci ne da ke tunatar da al'umma game da biyayya da sadaukarwa wanda hakan na daga cikin kyawawan ɗabi'un kowane nagartaccen soja. Tare da yin godiya ga Allah Maɗaukaki bisa rahmarSa da kariyarSa a kansu yayin da suke ƙoƙarin sauke nauyin da ya rataya a kansuna na…
Read More
Har yanzu ba a sabunta wa kamfanin Airtel lasisin zamansa a Nijeriya ba – NCC

Har yanzu ba a sabunta wa kamfanin Airtel lasisin zamansa a Nijeriya ba – NCC

Daga UMAR M. GOMBE Hukumar Kula Sadarwa ta Nijeriya (NCC) ta ce har yanzu ba ta amince da sabunta wa kamfanin sadarwa na Airtel lasisin gudanar da harkokinsa ba a Nijeriya saɓanin iƙirarin da shugaban kamfanin a Nijeriya, Mr. Olusegun Ogunsanya, ya yi. Daraktan Sahen Hulɗa da Jama'a na NCC, Dr. Ikechukwu Adinde, shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Lahadin da ta gabata. NCC ta tabbatar da cewa lallai kamfanin Airtel ya aika da takardar neman sabunta lasisin zamansa a Nijeriya, amma hukumar ba ta amince da hakan ba tukuna. NCC ta ci gaba…
Read More
Ƙarancin alburushi ya sa ‘yan sanda yi wa Matawalle ihu a Gusau

Ƙarancin alburushi ya sa ‘yan sanda yi wa Matawalle ihu a Gusau

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau 'Yan bindiga sun kashe wasu 'yan sanda su 14 waɗanda aka girke a Magami a yankin ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara domin yaƙi da harkokin 'yan fashin daji. Bayanan wasu daga cikin 'yan sandan da suka tsallake rijiya da baya a lokacin ɗauki-ba-daɗin, sun nuna an shafe kusan awa guda ana musayar wuta tsakanin 'yan sanda da 'yan bindigar kafin daga bisani bindigogin 'yan sanda suka koma tamkar sanduna a hannunsu sakamakon ƙarewar alburusai. Sun ce ganin halin da suka tsinci kansu sai suka aika da saƙon gaggawa a kan a sanar da gwamna…
Read More
Bello ya ziyarci sansanin jami’an tsaro don ƙarfafa musu gwiwa

Bello ya ziyarci sansanin jami’an tsaro don ƙarfafa musu gwiwa

Daga BASHIR ISAH Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja ya yaba wa rundunar haɗin gwiwa ta jami'an tsaron da aka jibge a ƙwauyen Kundu da ke yankin ƙaramar hukumar Rafi a jihar bisa ƙoƙarin da suka yi wajen daƙile harin 'yan bindiga a yankin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar 'yan bindigar da dama da kuma jami'an tsaro biyu. Bello ya yi wannan yabo ne a lokacin da ya ziyarci jami'an tsaron a sansaninsu domin gane wa idanunsa irin ƙoƙarin da suke yi da kuma ƙarfafa musu gwiwa wajen dawo da lumana a yankin. Sanarwar da Sakatariyar Labarai ta Gwamnan,…
Read More
Abuja, Kano, Kaduna da Filato na fuskantar mummunan hatsarin Korona

Abuja, Kano, Kaduna da Filato na fuskantar mummunan hatsarin Korona

Daga BASHIR ISAH Kwamitin Shugaban Ƙasa Kan Yaƙi da Annobar Korona (PSC) ya ayyana wasu jihohi guda shida, ciki har da Birnin Tarayya, Abuja, da ke fuskantar mummunan hatsarin korona tare da cewa akwai buƙatar jihohin su matse ƙaimi dangane da sha'anin yaƙi da cutar korona yayin bikin Babbar Sallah. Kwamiti ya bayyana haka ne biyo bayan wani nau'in koronar da aka gano a jihar Delta da kuma yadda ake samu ƙaruwar masu harbuwa da annobar a faɗin ƙasa. Shugaban kwamitin  kuma Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, shi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da aka raba wa manema…
Read More