18
Jul
Daga AMINA YUSUF ALI Babbab Sufeton 'Yan Sanda Mr Usman Baba, ya ba da umarnin a inganta sha'anin tsaro a faɗin ƙasa albarkacin bikin Babbar Sallah na bana. Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda na ƙasa, Mr Frank Mba, shi ne ya bayyana hakan cikin sanarwar da ya fitar ran Lahadi a Abuja. Baba ya buƙaci kwamishinonin 'yan sanda a faɗin ƙasa da mataimakansu da su tabbatar an bi umarnin nasa sau da ƙafa. Ya ce an ɗauki wannan mataki ne domin hana aukuwar kowane irin akasi a sassan ƙasa a lokacin bikin sallah. Don haka ya bai wa…
