Editor

9513 Posts
‘Yan Nijeriya 542,576 sun kammala matakin farko na rajista cikin mako 2 – Yakubu

‘Yan Nijeriya 542,576 sun kammala matakin farko na rajista cikin mako 2 – Yakubu

Daga UMAR M. GOMBE Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa jimillar 'yan Nijeriya 542, 576 ne su ka kammala matakin farko na yin rajistar katin zaɓe (CVR) a yanar gizo da ake gudanarwa yanzu ya zuwa ƙarfe 7 na safiyar ranar Litinin, 12 ga Yuli, wato mako biyu cif daga lokacin da aka fara aikin. Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, shi ne ya bayyana haka a ranar Talata lokacin da ya yi taro a Abuja da Zaunannun Kwamishinonin Zaɓe (RECs). Yakubu ya ce hukumar ta na farin ciki da nasarar da ake samu a matakin farko na yin rajista…
Read More
Itace tun yana ɗanye ake tanƙwara shi (3)

Itace tun yana ɗanye ake tanƙwara shi (3)

Ci gaba daga makon jiya. Daga BILKISU YUSUF ALI A yau ma ga mu a cikin filin naku mai albarka na Tarbiyya, kamar yadda mu ka saba a kowane mako. Za mu ɗora daga inda muka tsaya a makon jiya, amma kafin nan Ina so na daɗa yi wa iyaye nasiha akan rayuwar yaransu. Ita fa rayuwar nan dole sai an yi haƙuri an ajiye son zuciya an kuma dage da tilasta wa yara su san rayuwa. Duba da yadda komai ya kacacame mana iyaye, eh mana yanzu uwa ke tsoron ɗan da ta haifa a cikinta! Ƙiri-ƙiri uwa za…
Read More
Neja za ta soma rataye ɓarayin shanu da ‘yan leƙen asirin masu garkuwa da mutane

Neja za ta soma rataye ɓarayin shanu da ‘yan leƙen asirin masu garkuwa da mutane

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Neja kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta Tsakiya (NCSGF), Alhaji Abubakar Sani Bello, ya amince da wasu sabbin dokoki a jihar wanda ya yi daidai da sashe na 100(3) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima).  Dokokin sun haɗa da: Dokar garkuwa da mutane da satar shanu ta 2021, Dokar bijilanti ta 2021, Dokar Hukumar Kula da Majalisar Dokoki ta Jihar Neja ta 2020, Dokar ofishin babban jami'in bincike na jihar ta 2021, da kuma Dokar babban jami'in bincike na ƙananan hukumomi ta 2021. Da yake jawabi a wajen…
Read More
Ƙwaƙwalwar ɗan’adam

Ƙwaƙwalwar ɗan’adam

Daga MUSTAFA IBRAHIM ABDULLAHI ’Yan uwa masu karatu Assalam alaikum. Barkan mu da wannan lokaci; barkan mu da sake saduwa a wannan shafi mai albarka, wanda ke kawo muku bayanai game da jikin ɗan'adam, domin ku fa’idantu, kusan yadda jikinku ke aiki. Rubtun yau zai mayar da hankali ne akan ƙwaƙwalwar ɗan adam, baiwar da Allah yayi mata, da wasu daga cikin baye- bayenta. Ƙwƙwalwar ɗan adam tana waɗansu baye-baye da Allah yayi mata a jiki saboda muhimmancinta. Bari na kawo kaɗan daga ciki. Matsayi: Ƙwaƙwalwar ɗan adam ta kasance a mafi ɗaukakar bigire a jikin ɗan adam. Da Sarkin…
Read More
Ganduje ya shigar da sabuwar ƙara a kan Jaafar

Ganduje ya shigar da sabuwar ƙara a kan Jaafar

Daga WAKILINMU Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya sake maka mawallafin jaridar Daily Nigerian, Jaafar Jaafar, a kotu kan wani sabon ƙorafi. Ganduje ya sake shigar da ƙara kan Jaafar Jaafar ne tare da kamfanin Penlight Light Media Limited a wata Babbar Kotun Abuja inda da aika wa waɗanda lamarin ya shafa da takardar sammaci mai ɗauke da lamba CU/1598/2021 da kuma kwanan wata 15, Yuli, 2021. Wa'adin amfanin sammacen wata uku ne daga ranar da aka ba da shi, kamar dai yadda rajistaran Babban Kotun Abuja ya sanya hannu. Idan dai za a iya tunawa, a can baya Ganduje…
Read More
Mata guda 20 da maza ke gudu

Mata guda 20 da maza ke gudu

Daga AMINA YUSUF ALI Idan mai karatu bai manta ba, a makon da ya gabata mun kawo mu ku irin nauin mazajen da mata suka ƙi jinin su kasance a inuwa ƙaya da su. Kusan dukkan mata da wuya a samu mai auren waɗancan mazajen in dai har ta san da wannan halin kafin ta shiga gidansa. Kamar yadda a tsarin rayuwa aka so a dinga dukan jaki sannan a daki taiki, wannan mako kuma, za mu kawo mu ku matan da suka zama baragurbin mata waɗanda duk macen da ta kasance cikinsu, abar gudu ce a wajen mutane, idan…
Read More
Nijeriya na neman addu’ar kowa!

Nijeriya na neman addu’ar kowa!

Daga NASIR S. GWANGWAZO Mafi yawan talakawan Nijeriya sun yi tsammanin cewa, kawo yanzu ’yan ƙasar sun fita daga cikin halin ƙuncin da suka tsinci kansu a ƙarƙashin gwamnatocin baya, to amma har yanzu al’amura sun ƙi miƙewa, su tafi yadda ya kamata, duk da cewa, an zaɓo shugaban da ake da kyakkyawan zato a kansa, sannan kuma har kawo yanzu ba a taɓa zargin sa da aikata almundahana ko muna-muna da rashawa ba. To, amma duk da haka, baya ga tsananin halin talauci, fatara da ƙuncin rayuwa da talaka a Nijeriya ke fama da su, a yanzu dai kullum…
Read More
Mahara sun kashe Janar Ahmed a Abuja

Mahara sun kashe Janar Ahmed a Abuja

Daga UMAR M. GOMBE Wasu mahara sun kashe Manjo Janar Hassan Ahmed, tsohon Provost Marshal na Sojojin Najeriya a Abuja. An kashe Ahmed ne jiya Alhamis da daddare a yankin Abaji na Abuja. Maharan sun kuma sace 'yar uwar marigayin mai suna Safina Ahmed, wadda suka kuskure a matsayin matarsa. Wata majiya ta kusa da marigayin ta bayyana cewa, marigayin suna kan hanyarsu ta dawowa daga Okene ne inda maharan suka far musu. Majiyar ta ce 'yan bindigar sun buɗe wa motarsu wuta ne inda nan take Ahmed ya rasu, shi kuwa direban motar sai ya yi likimo kamar ya…
Read More
Bello ga ma’aikatansa: Ku rungumi noman shinkafa don kyautata rayuwarku

Bello ga ma’aikatansa: Ku rungumi noman shinkafa don kyautata rayuwarku

Daga BASHIR ISAH An yi kira ga ma'aikatan gwamnati na jihar Neja da su rungumi hanyoyin da za su taimaka musu wajen samun kuɗaɗen shiga fiye da albashin da suke samu domin samun madogara bayan sun yi murabus daga aiki. Gwamnan Jihar, Abubakar Sani Bello, shi ne ya yi wannan kira a wajen bikin ƙaddamar da Ƙungiyar Manoman Shinkafa ta Nijeriya (RIFAN) da aka gudanar ran Alhamis a Minna, babban birnin jihar don amfanin ma'aikatan gwamnatin jihar a wannan damina. Bello ya ce ƙaddamar da shirin cikar wani ɓangare ne na ƙudurin da yake fa shi kan ma'aikatan gwamnati na…
Read More