Neja za ta soma rataye ɓarayin shanu da ‘yan leƙen asirin masu garkuwa da mutane

Daga BASHIR ISAH

Gwamnan Jihar Neja kuma Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta Tsakiya (NCSGF), Alhaji Abubakar Sani Bello, ya amince da wasu sabbin dokoki a jihar wanda ya yi daidai da sashe na 100(3) na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima). 

Dokokin sun haɗa da: Dokar garkuwa da mutane da satar shanu ta 2021, Dokar bijilanti ta 2021, Dokar Hukumar Kula da Majalisar Dokoki ta Jihar Neja ta 2020, Dokar ofishin babban jami’in bincike na jihar ta 2021, da kuma Dokar babban jami’in bincike na ƙananan hukumomi ta 2021.

Da yake jawabi a wajen taron amincewa da dokokin a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Minna, Gwamna Bello ya ce Dokar garkuwa da mutane da satar shanu ta 2016 aka yi wa kwaskwarima ta yadda za ta ba da damar yin hukunci mai tsanani a kan ‘yan leƙen asirin masu garkuwa da mutane da dukkan masu taimaka wa harkokin satar mutane da shanu a jihar.

Da wannan cigaban da aka samu, Bello ya ce daga yanzu hukuncin ɗan leƙen asirin masu garkuwa da mutane da masu taimaka wa harkokinsu da ɓarayin shanu a jihar, duk wanda aka kama da aikata wannan laifi rataye shi za a yi baina jama’a har ya mutu kamar yadda doka ta tanadar.

Gwamnan ya ci gaba da cewa, ɗaukar wannan mataki abu ne da ya zama wajibi duba da yadda matsalar tsaro ke ci gaba da yi wa zaman lafiyar jihar barazana.

Bello ya nuna takaicinsa kan yadda harkar ‘yan leƙen asirin ɓatagarin a jihar ya yi tasiri wajen haifar da cikas ga ƙoƙarin da jami’an tsaron jihar ke yi wajen yaƙi da matsalolin tsaro. Wanda a cewarsa, hakan na daga cikin dalilan samar da Dokar ‘yan banga wadda za ta ƙarfafa wa ‘yan bangar gwiwa wajen ba da gudunmawarsu ga sha’anin yaƙi da manyan laifuka a faɗin jihar.

Duka waɗannan bayanai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Sakatariyar Yaɗa Labarai ga Gwamnan, Mary Noel-Berje, ta fitar a ranar Juma’a.