Editor

9513 Posts
Gobe RATTAWU za ta gudanar da babban taronta a Zamfara

Gobe RATTAWU za ta gudanar da babban taronta a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Kawo yanzu an kammala shirye-shirye tsaf don gudanar da taron wakilai na ƙasa na Ƙungiyar Ma'aikatan Rediyo, Talabijin da 'Yan Wasan Dandamali ta Nijeriya (RATTAWU) a Gusau Babban birnin jihar Zamfara da aka shirya gudanarwa a ranar Juma'a 16 ga Yuli, 2021. Da yake magana da manema labarai a Gusau a Yammacin yau Laraba, Shugaban RATTAWU na ƙasa, Kwamared Kabir Garba Tsanni, ya ce tuni wakilan jihohi 36 na shugabannin ƙungiyar sun fara sauka a Gusau don halartar taron ƙungiyar da za a yi gobe Juma'a. Tsanni ya bayyana ƙwarin gwiwa kan shirin da kwamitin…
Read More
Gangamin siyasa: Majalisar Zamfara ta gayyaci Mataimakin Gwamna kan zargin take doka

Gangamin siyasa: Majalisar Zamfara ta gayyaci Mataimakin Gwamna kan zargin take doka

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta gayyaci Mataimakin Gwamnan Jihar, Mahdi Aliyu Muhammad Gusau, tare da Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar, Hussaini Rabiu, da su bayyana a gabanta ya zuwa ranar Talata, 27 ga Yulin 2021. Majalisar ta cim ma matsayar aika gayyatar ne s zamanta na jiya Larabar. Dalilin gayyatar majalisar ya biyo bayan wani ikirarin gudanar da gangamin siyasa da Mataimakin Gwamnan ya yi a ranar Asabar din da ta gabata, yayin da wasu 'yan bindiga suka kai hari a kan al'ummomin ƙaramar hukumar Maradun a daidai lokacin da jihar ke jimami saboda addabar da…
Read More
Yau Buhari zai ziyarci Kano

Yau Buhari zai ziyarci Kano

A yau Alhamis Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai kai ziyarar aiki jihar Kano inda ake sa ran ya ƙaddamar da ginin sabon layin dogo daga Kano zuwa Kaduna. Layin dogon da Buhari zai ƙaddamar a Kano shi ne zai haɗe da na Kaduna zuwa Abuja zuwa Legas. Wannan na daga cikin ayyukan da gwamnatin Buhari ta ƙuduri aniyyar yi domin bunƙasa fannin tattalin arzikin ƙasa.
Read More
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da basarake a Kogi sun buƙaci fansar milyan N30

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da basarake a Kogi sun buƙaci fansar milyan N30

Daga WAKILINMU Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba sun yi garkuwa da Sarki Adogu na Eganyi, Alhaji Mohammed Adembe a yankin ƙaramar hukumar Ajaokuta da ke jihar Kogi. Bayanai sun nuna an sace basaraken ne da yammacin Talatar da ta gabata a kan hanyar Okene-Eganyi. Wannan al'amari na zuwa ne sa'o'i 72 da sako Sarkin Kajuru a jihar Kaduna, Alhaji Hassan Adamu, bayan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da shi tare da iyalansa. Kazalika, sace basaraken Kogin na zuwa ne kwanaki uku da sace babban manaja a kamfanin haɗa magunguna na AZECO Pharmaceutical,…
Read More
Ɗan jairida ya zo na biyu a gasar rubutattun waƙoƙin Hausa a Sakkwato

Ɗan jairida ya zo na biyu a gasar rubutattun waƙoƙin Hausa a Sakkwato

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau Ɗan jarida Bashir Yahuza Malumfashi ya samu nasarar zama na biyu a gasar rubutattun waƙoƙin Hausa da aka gudanar a Jami'ar Usman Ɗanfodiyo da ke Sakkwato. Bashir ya wallafa bayanin nasarar tasa ce a shafinsa na facebook da yammacin Laraba inda ya nuna farin cikinsa dangane da nasarar da ya samu. Ya ce, "A yau Laraba, 04-12-1442 (Hijriyya) daidai da 14-07-2021 (Miladiyya) aka gudanar da bikin Gasar Rubutattun Waƙoƙin Hausa da Sashin Hausa na Jami'ar Usman 'Danfodiyo Sakkwato ya shirya. "Allah da ikonSa na shiga gasar rubuta waƙa ta Gani-Ga-Ka, inda mu 42 muka fafata,…
Read More
Hajjin bana: Ɗaurin watanni 6 da tarar Riyal 50,000 ga direban da ya yi jigilar alhazai ba tare da shaidar izini ba

Hajjin bana: Ɗaurin watanni 6 da tarar Riyal 50,000 ga direban da ya yi jigilar alhazai ba tare da shaidar izini ba

Daga WAKILINMU Sashen kula da sha'anin fasfo na Ƙasar Saudiyya ya yi gargaɗin cewa, duk wanda aka kama yana jigilar mahajjata ba tare da shaidar izini ba za a yi masa hukuncin ɗaurin wata shida a gidan kaso har da ƙarin tarar Riyal 50,000. Baya ga wannan, sashen ya kuma ce za a bayyana sunayen masu laifin a kafafen yaɗa labarai na cikin gida tare da ƙwace abubuwan hawan da aka yi amfani da su wajen aikata laifin. Kazalika, hukumar ta ce duk wani mai aikin Hajjin da aka kama da laifin yin amfani da kan sarki (Stamp) na bogi…
Read More
Yanzu yanzu: Yadda bikin Makon Hausa ke gundana a Kwalejin Aminu Kano

Yanzu yanzu: Yadda bikin Makon Hausa ke gundana a Kwalejin Aminu Kano

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano A daidai wannan lokaci ana kan gudanar da bikin Makon Hausa da Sashen Koyar da Hausa na Kwalejin Shari'a da Addinin Musulunci ta Malam Aminu Kano ya saba gudanarwa duk shekara. Malaman kwalejin da ma takwarorinsu daga Jami'ar Bayero sun gabatar da lacca kan batutuwa daban-daban. Sannan an samu mawaƙan zamani irin su Isah Ayagi da Salhabilun Hausa da Abdul Kafinol da sauransu, sun nishaɗantar da taron. A kasance da Manhaja don samun cikakken rahoton bikin a fito ta Juma'a mai zuwa.
Read More
Yadda ‘yan bindiga suka halaka fitaccen ɗan kasuwa a Bauchi

Yadda ‘yan bindiga suka halaka fitaccen ɗan kasuwa a Bauchi

Daga WAKILINMU A Talatar da ta gabata wasu 'yan bindigar da ba a san ko su wane ne ba suka halaka wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Tasi’u Abdulkarim a garin Tilden-Fulani da ke yankin ƙaramar hukumar Toro a jihar Bauchi. Ƙanin marigayin, Isah Tilde, ya shaida wa manema labarai cewa 'yan bindigar sun far wa yayan nasa ne a shagonsa na sayar da magunguna (Pharmacy) da ke kasuwar Tilden-Fulani wajajen ƙarfe 10 na dare, inda suka raba shi da kuɗaɗe masu yawa da wayoyoyinsa kana suka yi gaba da shi. Ya ci gaba da cewa, daga bisani ɓarayin suka…
Read More
Sanatoci sun ƙi amincewa da naɗa Ononchie Kwamishinar INEC

Sanatoci sun ƙi amincewa da naɗa Ononchie Kwamishinar INEC

Daga AMINA YUSUF ALI Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da a naɗa Ms Lauretta Onochie a matsayin Kwamishinar Hukumar Zaɓe (INEC) mai wakiltar jihar Delta. Haka nan Majalisar ta amince da naɗin wasu da aka tura mata sunayensu don tabbatar da su a matsayin kwamishinonin INEC. Waɗanda Majalisar ta amince da naɗin nasu, su ne; Farfesa Muhammad Sani Kallah (daga Katsina), Farfesa Kunle Ajayi (daga Ekiti), Saidu Ahmad (daga Jigawa), Dr Baba Bila (daga shiyyar Arewa-maso-gabas), sai kuma Farfesa Abdullahi Zuru (daga shiyyar Arewa-maso-yamma). Naɗin nasu ya biyo bayan amincewa da Majalisar ta yi ne da rahoton da kwamitin tantance…
Read More