Editor

9513 Posts
Anjima Buhari zai gana da sanatoci a fadarsa

Anjima Buhari zai gana da sanatoci a fadarsa

Ya zuwa ƙarfe 8 na dare na wannan Talatar ake sa ran Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai gana da sanatoci su 109 a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja. Sanarwar ganawar na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa da Fadar Shugaban Ƙasar ta aika wa sanatocin wanda Shugaban Majalisar, Ahmad Lawan, ya karanta ta yayin zaman majalisar. A ranar 27 ga Afrilun da ya gabata ne sanatocin suka cim ma matsayar neman ganawa da Buhari domin ba su damar tattauna matsalar tsaron ƙasa da shi.
Read More
Buhari ya miƙa tutar jam’iyya ga gwamnonin da suka sauya sheƙa zuwa APC

Buhari ya miƙa tutar jam’iyya ga gwamnonin da suka sauya sheƙa zuwa APC

A Litinin da ta gabata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya karɓi baƙuncin gwamnonin Cross River daZamfara da suka sauya sheƙa zuwa APC kwanan nan a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja Sun yi ziyarar ne ƙarƙashin jagorancin shugaban APC na ƙasa, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe. Yayin ziyarar, Buhari ya miƙa wa Gwamnan Cross River, Farfesa Ben Ayade da takwaransa na Zamfara, Bello Matawalle, tutar jam'iyyar APC a matsayin wani mataki na yi musu maraba da zuwa APC.
Read More
Kaftin ɗin Super Eagles ya ƙara aure

Kaftin ɗin Super Eagles ya ƙara aure

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Fitaccen ɗan wasan ƙwallon ƙafa kuma Kaftin na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasa Super Eagles, Ahmed Musa, ya ƙara aure. Musa mai shekaru 29, wannan shi ne aurensa na uku, tun bayan da ya rabu da matarsa ta farko Jamila a 2017 wanda nan take ya maye gurbinta da Juliet kuma suke tare har yanzu. A halin da ake ciki dai yanzu sabuwar amaryar tasa mai suna Maryam ita ce matarsa ta biyu. Jarumi a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu, shi ne ya wallafa bayani da hotunan auren a shafinsa na Instagram inda ya taya Ahmad…
Read More
APC ta tsayar da ranar soma tarurrukanta

APC ta tsayar da ranar soma tarurrukanta

Daga AISHA ASAS Jam'iyyar (APC) ta tsayar da ranar 31 ga Yuli, 2021 a matsayin ranar da za ta soma gudanar da tarurrukanta don zaɓen shugabannin jam'iyya a faɗin ƙasa. Cikin wata wasiƙa da ta aike wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) mai ɗauke da kwanan wata, 11 Yuli, 2021, APC ta nuna za ta soma tarurrukan nata ne a ranar 31 ga watan Yuni inda za a soma da matakin unguwanni kafin ƙananan hukumomi da jihohi su biyo baya. Kafin wannan lokaci, APC ta aika wa INEC da wasiƙa a kan ɗage tarurrukan nata da ta shirya gudanarwa da…
Read More
An sako Sarkin Kajuru

An sako Sarkin Kajuru

Daga ABBA MUHAMMAD, a Kaduna Bayanai daga jihar Kaduna sun nuna Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu, ya samu 'yanci bayan sako shi da 'yan bindigar da suka yi garkuwa da shi suka yi. Babban ɗan Sarkin kuma Madakin Kajuru, Alhaji Musa Alhassan Adamu, shi ne ya tabbatar da labarin sakin sarkin. Ya ce suna zaune a gida da rana, kwatsam sai suka ga sarkin ya shigo. Sai dai ya ce ba a sako ragowar mutum 13 da aka yi garkuwa da su tare da sarkin ba. Ya ce cikin ƙoshin lafiya mahaifin nasu ya komo gida. Amma cewa an garzaya…
Read More
Nijeriya ta ware wa Hukumar NIA Naira biliyan 4.87 don leƙen asirin WhatsApp

Nijeriya ta ware wa Hukumar NIA Naira biliyan 4.87 don leƙen asirin WhatsApp

Daga UMAR M. GOMBE Majalisar Tarayya ta amince da kasafin Naira bilyan N4.87 da aka ware don amfanin Hukumar Tattara Bayanan Sirri ta Ƙasa (NIA) wajen bibiyar kiraye-kiraye da saƙonni a wayoyi haɗa da Thuraya da manhajar WhatsApp. Kuɗaɗen wani ɓangare ne na ƙarin kasafin Naira biliyan N895.8 da Shugaba Buhari ya nema a watan jiya wanda Majalisar Dattawa da ta wakilai suka amince da shi a makon jiya bayan da suka cilla kasafin da ƙarin biliyan N87. A cewar Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Rabon Kasafi, Sanata Barau Jibrin, za a yi amfani da ƙarin kasafin ne wajen samar…
Read More
‘Yan bindiga sun buƙaci fansar milyan N200 kafin su saki Sarkin Kajuru

‘Yan bindiga sun buƙaci fansar milyan N200 kafin su saki Sarkin Kajuru

Daga ABBA MUHAMMAD, a Kaduna Kawo yanzu, 'yan fashin dajin da suka yi garkuwa da Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu, sun buƙaci a ba su fansar milyan N200 kafin su saki sarkin. Idan dai za a iya tunawa, Manhaja ta ruwaito yadda aka sace basaraken tare da wasu ahalinsa su 13, ciki har da jikokinsa da safiyar Lahadin da ta gabata a gidansa da ke garin Kajuru a jihar Kaduna. Mai magana da yawun Masarautar Kajuru, Dahiru Abubakar, shi ne ya bayyana batun kuɗin fansar da 'yan bindigar suka nema a ranar Litinin. Haka nan, Abubakar ya ce 'yan bindigar…
Read More
An kama sojan da ya kashe ɗalibi a Kalaba

An kama sojan da ya kashe ɗalibi a Kalaba

Daga WAKILINMU Rundunar Sojoji ta Nijeriya ta bayyana cewa ta kama wani sojan da aka tura aiki a Gidan Yarin Calabar bisa zargin kashe wani ɗalibi da ke ajin ƙarshe a Jami'ar Kalaba mai suna Mr Gray Agbesu a ranar Juma'a, 9 ga Yuli 2021. Daraktan sashen hulɗa da jama'a na rundunar, Brig.- Gen Onyema Nwachukwu, cikin wata sanarwa da ya fitar a Lahadin da ta gabata, ya ce an cafke sojan ne a daidai lokacin da ya yi ƙoƙarin arcewa gudun kada a kama shi. Ya ce yanzu haka sojan na tsare a hannun 'Yan Sandan Sojoji kuma an…
Read More
2023: Zan janye aniyata ta neman shugabancin ƙasa idan APC ta miƙa tikiti ga yankin Kudu – Yerima

2023: Zan janye aniyata ta neman shugabancin ƙasa idan APC ta miƙa tikiti ga yankin Kudu – Yerima

Daga BASHIR ISAH Tsohon Gwamnan Zamfara, Ahmed Yerima, ya bayyana cewa zai janye aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2023 muddin jam'iyyar APC ta miƙa tikitin takarar Shugaban Ƙasa ga yankin Kudu. Yerima ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Abuja a Lahadin da ta gabata. Tsohon sanatan ya ce duk da matsayar da gwamnonin Kudu suka cim ma a wani taronsu da suka yi a Legas, bai ga dalilin da zai sanya shi janyewa daga takarar neman shugabancin ƙasa ba. Ya ce, “Ina mai tabbatar muku da cewa idan Allah Ya…
Read More