12
Jul
12
Jul
Daga WAKILINMU Biyo bayan bayyana Lahadi, 11 ga Yuli a matsayin 1 ga watan Zul-Hijja 1442AH da Mai Martaba Sultan na Sakkwato kuma Shugaban Majalisar Ƙoli na Harkokin Musulunci na Nijeriya (NSCIA), Alhaji Sa’ad Abubakar III ya yi, ya tabbata cewa Talata, 20 ga Yuli ita ce ranar da Musulmin Nijeriya za su yi Babbar Sallah ta bana. Sultan ya bayyana sabon watan ne cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun Shugaban Kwamitin Bai wa Majalisar Sultan Shawara kan Sha'anin Addini, Farfesa Sambo Junaidu, a Lahadin da ta gabata a Sakkwato. Sanarwa ta nuna cewa, "Kwamitin bai wa Majalisar…
11
Jul
Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna Allah Ya yi wa tsohon mataimakin gwamnan jihar Kaduna, Yusuf Barnabas Bala, da aka fi sani da Bantex, rasuwa. Bayanan na Manhaja ta kalato sun nuna Bantex ya rasu ne da safiyar Lahadi. Marigayin ya riƙe muƙamin mataimakin gwamnan jihar ne a 2015 da 2019, yayin wa'adin farko na Gwamna Nasir El-Rufai. A 2019 ne Bantex ya saki muƙamin nasa a matsayin mataimakin gwamna don neman kujerar sanata a shiyyar Kaduna ta Kudu inda abokin takararsa na PDP, Danjuma La’ah, ya kada shi. Gwamna El-Rufai ya ce ya yi matuƙar kaɗuwa da samun labarin rasuwar…
11
Jul
Daga SUNUSI MUHAMMAD, a Gusau. An sami ruɗani a Kwalejin Nazarin Harkokin Gona da Kimiyyar Dabbobi ta Bakura da ke hedikwatar ƙaramar hukumar Bakura a jihar Zamfara a ranar Asabar yayin da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su wane ne ba suka sace shugaban Kwalejin Nazarin Harkokin Gona mallakin gwamnatin jihar Zamfara, Malam Habib Mainasara a cikin gidansa da ke makarantar. Da yake yi wa wakilinmu ƙarin haske ta waya, mataimakin rajistara na kwalejin, Malam Aliyu Atiku Bakura, ya ce 'yan bindigar sun yi wa gidan shugaban makarantar ƙawanya ne da misalin ƙarfe 2:30 na tsakar daren…
11
Jul
Daga ABBA MUHAMMAD a Kaduna Wasu 'yan bindiga a jihar Kaduna sun kai hari a masarautar ƙaramar hukumar Kajuru, inda su ka sace sarkin garin, Alhaji Alhassan Adamu da wasu daga cikin iyalansa. An sace Sarkin tare da iyalan su 13 a harin da 'yan bindigar suka kai da tsakar daren Lahadi. Binciken Manhaja ya gano an sace Sarkin mai shekara 85 tare da matansa uku, jikokinsa biyu, ma'aikatansa uku da kuma ƙarin mutum biyar. Bayanai sun nuna cewa Sarkin ya gudanar da taro ranar Juma'a a kan yadda za a shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi yankinsa. Wannan…
11
Jul
Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Muƙabalar da aka daɗe ana jira tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano an yi ta a safiyar jiya Asabar a Hukumar Shari'a da ke Unguwar Nassarawa, Kano, Tun da farko dai malaman sun bijiro da wasu tambayoyi da ba su ne suka kai wa gwamna ba, inda nan take Malam Abduljabbar ya yi ƙorafi ya ce lallai sai an kawo haƙiƙanin murya (audio) da aka kai wa gwamna ƙorafi a kai, inda ya tabbatar da cewa matuƙar ba a kawo wancan ba to ba zai ƙara amsa tambaya ko ɗaya ba. Daga nan ne shugaban…
10
Jul
Daga IBRAHIM MANDAWARI Kamar yadda wasu suka sani wasan kwaikwayo a Arewacin Nijeriya ya samo asali ne tun lokacin Mulkin Mallaka, wato lokacin da Turawan Ingila ke mulkin wannan ƙasa tamu Nijeriya. Hakan kuwa ya samo asali ne daga fuskoki guda uku; wato: Fuska ta ɗaya, wasannin kwaikwayo domin wayar da kai ga talakawa a fannoni daban-daban na rayuwa, misali wayar da kai a kan bunƙasa aikin gona musamman noman gyaɗa da auduga (Shirin Baban Larai), da kuma shiri a kan wayar da kai domin a ƙyale mata masu ciki su dinga halartar ƙananan asibitoci don haihuwa (Mama Learns a…
10
Jul
Daga IBRAHIM HAMISU a Kano A daidai lokacin da aka gab da fara muƙabal tsakanin Sheikh Abduljabbar Kabara da malaman Kano, an bayyana sunayen malaman da zai fafata da su. Malam da ake sa ran za su yi zaman muƙabala da Sheikh Jabbaru a yau Asabar, su haɗa da; Malam Abubakar Mai Madattai daga ɓangaren Tijjaniyya da Malam Kabir Bashir Ƙofar Wambai daga ɓangaren JIBWIS da Dr Rabi'u Umar Sani Rijiyar Lemo daga ɓangaren Salafiyya, sai kuma Malam Mas'ud Hotoro daga ɓangaren Ƙadiriyya. Shugaban Jami'ar Istiƙama da ke Kano, Farfesa Salisu Shehu, shi ne alƙalin muƙabalar. Mal. Abubakar Mal. Kabir…
09
Jul
Daga WAKILINMU Hukumar Binciken Haɗurra (AIB) ta ba da sanarwar cewa nan da mako guda za ta fitar sakamakon binciken farko dangane da haɗarin jirgin saman da ya yi sanadiyyar mutuwar Shugaban Rundunar Sojoji , Lt. Gen. Ibrahim Attahiru, tare da wasu mutum 10. Babban Jami'in Hukumar, Akin Olateru, shi ne ya bayyana hakan ran Alhamis da ta gabata a Abuja yayin da yake bayyana rahotannin da hukumar ta shirya kan haɗurran jirgin sama da suka auku har guda takwas. Sai dai, jami'in ya ce bayan miƙa rahoton nasu, zaɓi ya rage ga Rundunar Mayaƙan Sama na Nijeriya (NAF), ko…
09
Jul
Daga BASHIR ISAH 'Yan Sandan Ƙasar Haiti sun kama wasu mutum 28 dukkansu baƙi da aka yi zargin suna da hannu cikin badaƙalar kashe Shugaban Ƙasar, Jovenel Moïse, a farkon wannan makon. Bayanan 'yan sandan sun nuna cikin waɗanda aka tsaren wasunsu sun taɓa yin aikin soja, kuma an kama yawancinsu ne bayan ɗauki ba daɗin da aka da aka yi na musayar wuta a wani gida da ke Port-au-Prince, babban birnin ƙasar. An gabatar da waɗanda ake zargin ga manema labarai jina-jina a ran Alhamis da ta gabata tare da wasu makamai da aka samu aka ƙwace a hannunsu.…
