Editor

9513 Posts
Abinda ya haɗa ni rigima da Baturen ‘Yan Sandan Hotoro – Mansurah Isah

Abinda ya haɗa ni rigima da Baturen ‘Yan Sandan Hotoro – Mansurah Isah

Daga MUKHTAR YAKUBU a Kano A sati biyun da su ka gabata ne tsohuwar jaruma Mansurah Isah ta yi wata sanarwar ɓatan wata yarinya wadda har ta zargi Baturen 'Yan Sanda na Hotoro da cewar ya na neman ya ɓoye gaskiyar abin da ya faru, kuma hakan ya sa maganar ta yi tsayi har ta je ga ofishin Kwamishinan 'Yan sanda na Jihar Kano. Don haka ne muka nemi jin ta bakin Mansurah Isah don jin yadda maganar ta samo asali. Wakilin Manhaja a Kano ya samu damar tattaunawa da Mansura don kawo wa masu karatun mu gaskiyar zancen, domin…
Read More
Marubuta su kasance masu zurfafa bincike – Shugaban Ƙungiyar Mikiya

Marubuta su kasance masu zurfafa bincike – Shugaban Ƙungiyar Mikiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙungiyar Marubutan Jihar Kaduna, wadda aka fi sani da 'Mikiya Hausa Writers', Kwamared Sani Shehu Lere ya yi kira ga ɗaukacin marubuta da su kasance masu zurfafa bincike kafin aiwatar da rubutun su. Sani ya yi wannan kiran ne a wani taron ƙara wa juna sani da ƙungiyar ta shirya kuma ta gabatar a makon jiya. A cikin jawabin sa Shugaban ƙungiyar, Sani Shehu ya ce yin bincike bayan samuwar jigon yin kowane irin rubutu na hikaya abu ne mai muhimmancin gaske, musamman wajen kauce wa kura-kurai na zahiri da kowa zai iya…
Read More
Ƙarin girma: Hukumar ’Yan Sanda ta yi wancakali da Magu

Ƙarin girma: Hukumar ’Yan Sanda ta yi wancakali da Magu

…Biyo bayan rahoton Ayo Salami, an ciyar da ’yan sanda da dama gaba Daga NASIR S. GWANGWAZO, a Abuja Hukumar Kula da Aikin ’Yan Sanda a Nijeriya (PSC) ta yi wancakali da batun ƙara wa tsohon Shugaban Hukumar Yaƙi da Ta’annatin Kuɗi da Tattalin Arziki ta Ƙasa (EFCC), Ibrahim Magu, biyo bayan rahoton Kwamitin Mai Shari’a Ayo Salami, wanda ya zargi Magun da aikata ba daidai ba a lokacin da ya ke shugabantar hukumar ta EFCC. Kazalika, Hukumar PSC ta yi ƙarin girma ga manyan 'yan sanda guda uku zuwa muƙamin Muƙaddashin Babban Sufeton ’Yan Sanda na Ƙasa (DIGs), yayin…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe mutum 39 a harin ramuwar gayya a Zamfara

‘Yan bindiga sun kashe mutum 39 a harin ramuwar gayya a Zamfara

Daga SUNUSI MUHAMMAD, a Gusau Aƙalla mutane 39 ne 'yan bindiga suka kashe a wani harin ramuwar gayya a Faru da ke ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara. A wata tattaunawa ta wayar tarho da wani mazaunin Faru mai suna Malam Lawali Ahmad Faru, ya ce, "'Yan bindigar sun afka wa garin ne da misalin ƙarfe 4:30 na yammacin ranar Alhamis inda suka fara harbin kan mai uwa da wabi da bindigogi a cikin mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, wanda hakan ya yi ajalin mutane 39 wanda galibinsu maza ne." Ya ce 'yan taddan sun…
Read More
Ko dai Arewa ce kaɗai Nijeriya?

Ko dai Arewa ce kaɗai Nijeriya?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Tambayar da kwanan nan ke shigowa dodon kunne na ita ce "Shin Arewa ce kaɗai Nijeriya?." Amsar tambayar na buƙatar a duba abu uku, na farko tarihin haɗe kudanci da arewacin Nijeriya a 1914 da yadda gimbiyar Babban Gwamna Lord Luggard ta raɗa wa Nijeriya sunan. Na biyu za a duba yadda wasu sassan masar ke cewa su na son ɓallewa don kafa ƙasar kan su duk da ba kowa ne ke da ra'ayin ba. Na uku za a duba yadda 'yan Arewa su ka sadaukar da kai wajen yaƙin basasa har dakaru su ka ci…
Read More
Itace tun yana ɗanye ake tanƙwara shi (2)

Itace tun yana ɗanye ake tanƙwara shi (2)

Mu ɗora inda muka tsaya a makon jiya. Daga SADIYA GARBA YAKASAI Yana da kyau mu kula da irin abokan da yaran mu ke mu'amala da su. A yanayi na rayuwa, bai kamata mu sa wa yara ido suna mu'amala da kowa ba. Yana da kyau uwa ta la}anci wa yaranta ke kulawa. Da zarar kin ga yanayin yaran da yaranki ke harkar da su, to mataki na bincike za ki fara ɗauka. Idan ki ka bari yaron ki ko yarinyar ki na kai wa dare a waje ko ƙaryan biki ko zuwa fati, to ki shirya rugujewar rayuwar ɗan…
Read More
Mazaje 16 da mata ba sa ƙauna!

Mazaje 16 da mata ba sa ƙauna!

Daga AMINA YUSUF ALI Barkanku da da jimirin karatun jaridarku mai farin jini, Manhaja. A wannan mako, za mu kawo muku irin jerin mazajen da mata suke ƙyamar su haɗa inuwa ɗaya da su a zamantakewa ta aure. Duk da dai a ɗabi'ance ana ganin halitta da iya lafazin namiji yana rinjayar da soyayyarsa a zuciyar mace. Amma akwai wasu abubuwa ko halayen da duk namiji mai su yakan zama abin ƙyama da gudu kuma a wajen mace. Waɗanda ko ƙwarewar namiji wajen kalaman jan hankalin ba za su iya tasiri wajen kawar da hakan ba. Sai dai ta zauna…
Read More
Shin da gaske ne Gwamnatin Buhari na zuba dukiya a harkokin tsaro?

Shin da gaske ne Gwamnatin Buhari na zuba dukiya a harkokin tsaro?

Daga NASIR S. GWANGWAZO A yanayin halin da Nijeriya ta tsinci kanta a ciki yanzu, ba kowa ne ya sani ko zai iya gane ƙoƙarin Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan sha’anin tsaro ba, saboda yadda ake ci gaba da samun tangarɗa da cikas wajen shawo kan lamarin tsaro, wanda ya addabi al’umma, amma ko babu komai, za a iya cewa, haƙiƙanin ta’addanci da Boko Haram ta miƙe ƙafa ta na yi a gwamnatin baya, yanzu ya zama tarihi. A yanzu babu ƙaramar hukuma ko guda ɗaya a hannun Boko Haram, duk da cewa, gwamnatin baya ta sadar wa ƙungiyar ƙananan…
Read More
Ina sane da halin da ku ke ciki – Buhari ga sojoji

Ina sane da halin da ku ke ciki – Buhari ga sojoji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya bayyana bikin Ranar Sojoji a matsayin wani abin da ke ci gaba da bai wa 'yan ƙasa kyakkyawar fata da ƙwarin gwiwa a hanƙoron su na rayuwa cikin zaman lafiya irin na al'ummar da ke rayuwa ƙarƙashin tsari na dimokraɗiyya. Rundunar Sojin Nijeriya wacce ke da dogon tarihi na shekaru 185 da ta somo daga Turawan mulkin mallaka, ta taka rawa na musamman a yaƙin duniya na farko da na biyu da kuma yaƙin basasar haɗa kan Nijeriya. Shugaba Buhari wanda Ministan Tsaro Bashir Magashi ya wakilce shi, ya…
Read More
Matawalle ya sanya wa dokar cin gashin kai na ɓangaren sharia da Majalisar Dokoki hannu

Matawalle ya sanya wa dokar cin gashin kai na ɓangaren sharia da Majalisar Dokoki hannu

Daga SANUSI MUHAMMAD, a GUSAU Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya ba da damar aiwatar da ƙudirin dokar cin gashin kai ga ɓangaren shari'a da majalisar dokokin jihar Zamfara. Babban Daraktan Wayar da Kan Jama'a da Sadarwa, Yusuf Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Gusau ranar Alhamis. A cewarsa, Gwamnan ya rattaba hannu kan dokokin ne a wani takaitaccen biki wanda aka gudanar a Fadar Gamnatin jihar da ke Gusau, biyo bayan mahimmancin da gwamnan ya bai wa dokokin biyu, ya ce ba zai jira wani babban biki da za…
Read More