Editor

9513 Posts
Asabar mai zuwa za a yi muƙabala tsakanin Abduljabbar da malaman Kano

Asabar mai zuwa za a yi muƙabala tsakanin Abduljabbar da malaman Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnatin jihar Kano ta tsayar da Asabar mai zuwa a matsayin ranar da za a yi muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara da wasu malaman jihar. Bayanin haka ya fito ne daga bakin Kwamishinan Harkokin Addinai na Jihar, Muhammad Tahar Adamu wanda aka fi sani da Baba Impossible, yayin wata tattaunawa da BBC Hausa ya yi da shi a yau Alhamis. Kwamishinan ya ce za a gudanar da muƙabalar ce ranar Asabar, 10 ga Yulin da ake ciki a Hukumar Shari'a ta jihar Kano. Ya ce ya miƙa gayyatar yin muƙabalar ga malamin da malaman…
Read More
Daidai ne mulkin ƙasa ya koma Kudu a 2023 -Zulum

Daidai ne mulkin ƙasa ya koma Kudu a 2023 -Zulum

Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnan Jihar Barno, Babagana Zulum, ya jaddada kiransa kan batun miƙa mulkin ƙasa ga kudancin ƙasar nan wanda hakan ya nuna goyon bayan gwamnan ga gwamnonin Kudu waɗanda suka haɗe kansu wuri guda suna neman mulkin Nijeriya ya faɗo yankinsu ya zuwa 2023. A ranar Litinin da ta gabata gwamnonin Kudun suka yi wani taro a Legas inda suka cim ma matsayar cewa idan da adalci da kuma raba dai-dai ya kamata su ma a bari yankinsu ya ɗana shugabancin Nijeriya a 2023 lamarin da Zulum ya ce haka ya kamata. Zulum ya ce, "Na sha…
Read More
Harajin milyan $1: Nijeriya da Ghana sun soma tattaunawa don cim ma daidaito

Harajin milyan $1: Nijeriya da Ghana sun soma tattaunawa don cim ma daidaito

Daga WAKILINMU A matsayin wani mataki na ƙoƙarin kawo ƙarshen badaƙalar harjin Dala miliyan $1 da aka ƙaƙaba wa 'yan kasuwar Nijeriya a ƙasar Ghana, ƙasshen biyu sun soma wani zaman tattaunawa don fahimtar juna. A Larabar da ta gabata Shugaban Majalisar Wakilai na Nijeriya, Femi Gbajabiamila da takwaransa na Ghana, Rt. Hon. Kingsford Alban Bagbin sun yi wa 'yan majalisa bayani yayin zamansu a Abuja kan yadda Nijeriya da Gahana za su haɗa kai wajen magance matsalar kasuwanci a tsakanin ƙasashen biyu. Bayan kammala wani taron sirri da suka yi, jagororin biyu sun shaida wa manema labarai cewa nan…
Read More
Yaƙi da matsalar tsaro: A tsawaita wa’adin NYSC zuwa shekara 2 tare da ba su horon soji – Ishaku

Yaƙi da matsalar tsaro: A tsawaita wa’adin NYSC zuwa shekara 2 tare da ba su horon soji – Ishaku

Daga AISHA ASAS Gwamnan Jihar Taraba, Darius Ishaku, ya yi ra'ayin cewa donmin samun ƙarin matakan yaƙi da matsalolin tsaron ƙasar nan, zai kyautu a tsawaita wa'adin shirin yi wa ƙasa hidima, wato National Youth Service Corps (NYSC), zuwa shekara biyu tare da bai wa 'yan yi wa ƙasa hidimar horo irin na sojoji. Gwamna Ishaku ya bayyana haka ne yayin wani shiri da aka yi da shi a tashar ChannelsTV a jiya Laraba. Gwamnantin Tarayya ta ƙirƙiro shirin NYSC ne a 1973 da nufin ƙarfafa wa matasan da suka kammala karatu a manyan makarantu gwiwa wajen gina ƙasa. Ishaku…
Read More
Mansurah Isah ta ƙalubalanci DPO kan ƙin sauraron ƙorafin fyaɗe da suka kai masa

Mansurah Isah ta ƙalubalanci DPO kan ƙin sauraron ƙorafin fyaɗe da suka kai masa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Mansurah Isah, ta ƙalubalanci DPO na ofishin 'yan sanda na Hotoro a jihar Kano da ya yi aikinsa yadda ya kamata saboda a cewarta jama'a na kallonsa. Da alama dai kalaman Mansurah ba su rasa nasaba da yadda ɓatagarai ke lalata rayuwar ƙananan yara a jihar Kano ta hanyar yi musu fyaɗe da sauransu, inda ta ce iyaye da yawa na nan suna kuka saboda yadda aka ɓata wa yaransu rayuwa bayan an sace yaran an kuma sako su. Mansurah ta bayyana hakan ne a shafinta na Instagram a cikin wannan…
Read More
Buhari ya maƙala wa Yahaya sabon muƙaminsa

Buhari ya maƙala wa Yahaya sabon muƙaminsa

Daga UMAR M. GOMBE Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya maƙala wa Shugaban Rundunar Sojoji (COAS), Lt Gen Faruk Yahaya, sabon muƙaminsa a matsayin Lieutenant General. Buhari ya aiwatar da hakan ne tare da taimakon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo wanda ya gudana jim kaɗan kafin soma taron Majalisar Zartarwa na wannan makon da ya gudana a Larabar da ta gabata a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja. Da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala maƙala masa sabon muƙamin nasa, Yahaya ya yaba wa Shugaban Ƙasa bisa damar da ya ba shi don yi wa ƙasa aiki da kuma jagorancin rundunar…
Read More
Yadda shirin N-Power ke zaburar da miliyoyin matasa taka tudun dogaro da kai

Yadda shirin N-Power ke zaburar da miliyoyin matasa taka tudun dogaro da kai

Daga ALIYU ALI KAWAJI Shamsuddeen Surajo ya daɗe ya na gaganiyar yadda zai samu hanyar dogaro da kai, maimakon zaman jiran aikin da bai san ranar samu ba. Faɗi nan, tashi can, har Allah ya sa ya yi gamo-da-katar ɗin samun aikin N-Power. Ɗan alawus ɗin da ya riƙa samu bai almubazzarantar da su ba. Sai ya riƙa tara ƙudin sa a banki. Bayan wa'adin aikin sa ya ƙare, Shamsuddeen ya nemi ƙarin gudunmawa wajen abokan sa, inda ya buɗe shagon ɗinki a Hausawa, Kano. "Wato a baya idan Sallah ta zo ko ɗinki ba na iya yi wa kai…
Read More
Gwamnatin Tarayya ta ɗau ma’aikata 159 don sa ido kan Shirin Haɓaka Rayuwa a Kebbi da Ondo

Gwamnatin Tarayya ta ɗau ma’aikata 159 don sa ido kan Shirin Haɓaka Rayuwa a Kebbi da Ondo

Daga WAKILINMU Gwamnatin Tarayya ta ɗauki ma'aikata 159 tare da ba su horo don sa ido kan ayyukan Shirin Haɓaka Rayuwa, wato 'National Social Investment Programmes' (NSIP) a jihohin Kebbi da Ondo. A yayin da aka ɗauki mutum 70 a Kebbi, a Ondo an ɗauki mutum 89. Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar Farouq, ita ce ta bayyana haka a wajen tarurrukan raba takardun kama aiki da na'urorin aikin ga ma'aikata masu zaman kan su da aka horas waɗanda aka yi a Birnin Kebbi da kuma garin Akure. A taron Birnin Kebbi, ministar ta bayyana cewa…
Read More
Attajirai kaɗai ke cin moriyar tallafin mai – Minista

Attajirai kaɗai ke cin moriyar tallafin mai – Minista

Daga AISHA ASAS Ƙaramin Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Ƙasa, Clem Agba, ya jaddada buƙatar da ke akwai na duba fannin fetur don cire tallafin man baki ɗaya. Ministan ya faɗi haka ne saboda a cewarsa, a halin da ake ciki attajirai ne kaɗai ke amfana da tallafin amma ban da talakawa. Agba ya yi wannan bayani ne a wajen wani taro da aka gudanar kan batun shugabanci a Abuja a Talatar da ta gabata. Ya ce, "Wasu na ganin cewa wai idan aka cire tallafin fetur baki ɗaya talaka zai wahala, ta yaya zai wahala? Ai ba abu ne da…
Read More