Editor

9513 Posts
Matawalle ya sake naɗa wasu daga cikin mashawartansa da ya kora

Matawalle ya sake naɗa wasu daga cikin mashawartansa da ya kora

Daga Sanusi Muhammad, a Gusau A Litinin da ta gabata, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sake naɗa mutum takawas daga cikin masu ba shi shawara na musamma da ya sauke kwanan nan. Bayanin sake naɗa masu bai wa gwanan shawara na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun Babban Sakataren Harkokin Majalisar Gwamnan, Yakubu Haidara, a madadin sakataren riƙo na gwamnatin jihar, Alhaji Kabiru Balarabe Waɗanda naɗin ya shafa su ne; Aminu Abdullahi-Alkali, Ahmed Muktar-Mohammed, Junaidu Aminu-Kaura, Ibrahim Ma’aji-Gusau, Dr Aslam Aliyu, Yusuf Abubakar-Zugu, Danyaro Abdullahi-Wuya, da kuma Abubakar Musa (Mainera). Sanarwar ta nuna naɗin nasu…
Read More
‘Yan Majalisar Wakilai huɗu daga Zamfara sun koma APC

‘Yan Majalisar Wakilai huɗu daga Zamfara sun koma APC

Daga Sanusi Muhammad, a Gusau Wasu 'yan Majalisar Wakilai su huɗu daga jihar Zamfara sun sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC. 'Yan majalisar sun bayyana sauya sheƙar nasu a hakumance ne yayin zaman majalisar a yau Talata a Abuja. Waɗanda lamarin ya shafa su ne; Bello Shinkafi mai wakiltar Shinkafi/Zurmi; Ahmed Bakura mai wakiltar Bakura/Maradun; Ahmed Shehu mai wakiltar Bungudu/Maru; da kuma Suleiman Gummi mai wkiltar Gummi/Bukkuyum. An ji Shugaban Majalisar, Femi Gbajabiamila, ya karanto wasiƙar 'yan majalisar ta barin PDP zuwa APC a lokacin zaman majalisar. Idan dai ba a manta ba, Manhaja ta rawaito yadda Gwamnan Zamfara,…
Read More
Sojoji sun kama kayayyakin Boko Haram a Barno

Sojoji sun kama kayayyakin Boko Haram a Barno

Daga AISHA ASAS A wani shirin tsaftace yankin Muna daga harkokin 'yan ta'adda a jihar Barno, rundunar bataliya ta 195 na shirin Operation HADIN KAI (OPHK), tare da haɗin gwiwar Civilian Joint Task Force (CJTF) ta kama 'yan Boko Haram biyu tare da ƙwace tarin kayayyakin da aka tanada don amfanin 'yan Boko Haram. Kayayyakin da sojojin suka kama sun haɗa da gatari, kekuna guda biyar, wayar salula biyu, man fetur, ƙwayoyin ƙara kuzari, kayan abinci da dai sauransu. Yayin samamen sojojin sun lalata sansanonin 'yan ta'addan da dama tare da tsaftace yankin daga harkokin 'yan bindiga. Cikin sanarwar da…
Read More
Za a yi wa Magu ƙarin girma duk da mummunan rahoton da kwamitin Salami ya shirya a kansa

Za a yi wa Magu ƙarin girma duk da mummunan rahoton da kwamitin Salami ya shirya a kansa

*Fadar Shugaban Ƙasa ta nuna damuwarta kan lamarin Daga BASHIR ISAH Bayanan da Manhaja ta samu na nuni da Hukumar Aikin Ɗan Sanda (PSC) na shirin yi wa tsohon shugaban riƙo na Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗ'i, Ibrahim Magu, ƙarin girma a bakin aiki zuwa muƙamin Mataimakin Babban Sufeto (AIG). Sai dai Fadar Shugaban Ƙasa ta nuna damuwarta kan lamarin, saboda a ganinta tamkar PSC ta bijire wa mummunan rahoton da kwamitin bincike ƙarƙarshin Ayo Salami ya shirya a kan Magu ɗin ne, lamarin da ka iya ɗaukar hankalin 'yan ƙasa ya kuma…
Read More
Gwamnati za ta shigar da ƙarin yara miliyan 5 a shirin ciyar da ‘yan makaranta kafin 2023, inji Minista

Gwamnati za ta shigar da ƙarin yara miliyan 5 a shirin ciyar da ‘yan makaranta kafin 2023, inji Minista

Daga UMAR M. GOMBE Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Hajiya Sadiya Umar-Farouq, ta bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar ƙara yawan ɗalibai guda miliyan biyar cikin shirin ciyar da yara 'yan makaranta, wato 'National Home Grown School Feeding Programme' (NHGSFP) daga yanzu zuwa shekarar 2023. Hajiya Sadiya ta faɗi haka ne a lokacin taron da masu ruwa da tsaki su ka yi kan tantance masu amfana da shirin don haɓaka shi wanda aka yi a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara. A sanarwar da mai taimaka mata ta musamman kan harkar yaɗa labarai, Halima Oyelade, ta fitar a…
Read More
Waiwaye: Allah Ya kama ni idan na koma APC, cewar Matawalle a 2019

Waiwaye: Allah Ya kama ni idan na koma APC, cewar Matawalle a 2019

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau A ranar Talata, 29 ga Yunin da ya gabata gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Gwamnan ya ba da sanarwar komawsrsa APC neyayin wani ƙasaitaccen gangami da aka shirya don karɓar sa a APC ƙarƙashin jagorancin shugan jam'iyyar na ƙasa, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe. Matawalle, ya zama gwamnan Zamfara ne a 2019 biyo bayan wani hukunci da Kotun Ƙoli ta yanke kan rikicin cikin gidan da APC ta yi fama da shi a lokacin zaɓen fidda gwani a 2019. Yayin gangamin an ji Matawalle na…
Read More
Majalisa ta dakatar da Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa a Kano

Majalisa ta dakatar da Shugaban Hukumar Yaƙi da Rashawa a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU Majalisar Dokoki ta jihar Kano ta dakatar da Shugaban Hukumar Jin Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Rashawa ta Jihar, Muhuyi Magaji Rimin Gado. Binciken Manhaja ya gano cewa an dakatar da Magaji ne saboda ƙin karɓar wani akawun da Akanta Janar na jihar ya tura hukumar. 'Yan majalisun sun ce sun samu takardar ƙorafi daga ofishin Akanta Janar na Jihar daga Ma'aikatar Kuɗi ta Jihar bisa ƙin yarda da Magaji ya yi ya karɓi jami'in da aka tura hukumarsa a matsayin Babban Jami'in Kuɗi na hukumar.
Read More
An sake kwashe ɗalibai a wata makarantar Kaduna

An sake kwashe ɗalibai a wata makarantar Kaduna

Daga AISHA ASAS 'Yan bindiga sun sake kwashe ɗalibai a wata makarantar Kaduna da ke yankin ƙaramar hukumar Chikun a safiyar yau Litinin. Binciken Manhaja ya gano cewa 'yan bindigar sun shiga makarantar Bethel Baptist ne da sanyin safiyar Litinin inda suka yi ta harbin bindiga a sama sannan suka kwashi na kwasa daga cikin ɗalibai. Bayanai daga yankin sun nuna wasu mutum biyu sun rasu sakamakon harin, kuma wasu daga cikin ɗaliban sun samu zarafi sun tsere daga hannun barayin. Wannan shi ne karo na huɗu a tsakanin watanni shida da suka gabata inda 'yan bindigar ke shiga Kaduna…
Read More
Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da an samu fashewar wani abu a Kaduna

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da an samu fashewar wani abu a Kaduna

Daga WAKILINMU Rundunar 'yan sanda ta jihar Kaduna ta tabbatar cewa an samu fashewar wani abu a yankin Badarawa a jihar a ranar Asabar da ta gabata. Bayanan 'yan sanda sun nuna fashewar ta auku ne sakamakon wani makamashi da aka sarrafa cikin wasu gorunan madarar Viju guda uku. Rundunar ta ci gaba da cewa, wasu yara su uku sun ɗauki waɗannan goruna a matsayin abin wasa a bisa rashin sani inda suka yi ta bugawa kamar ƙwallo wanda a ƙarshe gorunan suka fashe tare da ji wa yaran rauni. Yaran da lamarin ya shafa su ne; Abubakar Aminu da…
Read More