Bayan kwana 42, an ceto mutum 100 da aka yi garkuwa da su a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau.

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar ƙarƙashin Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar, ta samu nasarar kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su kimanin su 100 ba tare da wani sharaɗi ba waɗanda aka sace daga ƙauyen Manawa na Gundumar Mutunji da ke cikin masarautar Ɗansadau ta ƙaramar hukumar Maru a jihar.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, SP Muhammad Shehu ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da aka raba wa manema labarai a Gusau ranar Laraba.

Ya ƙara da cewar, waɗanda aka Yi garkuwan da sun, an sako su ne bayan shafe kwanaki 42 a hannun ‘yan ta’addar ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, CP Hussaini Rabiu, ya gargaɗi ‘yan ta’addar da su daina aikata laifuka sannan su rungumi zaman lafiya ko kuma su gamu da fushin doka.

Rundunar ta yi kira ga al’ummar Zamfara da su taimaka wa ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro da sahihan bayanai game da maɓoyar ‘yan ta’adda da sauran ayyukan masu aikata manyan laifuka.

Manhaja ta bayar da rahoton cewa, a ranar 8 ga Yunin 2021 wasu ‘yan bindiga sun afka wa ƙauyen Manawa suka yi awon gaba da mutune 100 ciki har da mata masu shayarwa da maza da ƙananan yara.