28
May
*Har yanzu rundunar sojan Nijeriya na ci gaba da taka-tsantsan*Shin ko Nijeriya za ta amfana da nasarar ISWA kan Boko Haram?*Janar Yahaya: Wane ne wanda Buhari ya saka magajin Attahiru? Daga NASIR S. GWANGWAZO, a Abuja A ranar Alhamis, 27 ga Mayu, 2021, rahotanni suka fantsama a cikin Nijeriya da ƙasashen duniya cewa, ɗaya da daga cikin waɗanda Nijeriya da Amurka ke kallo a matsayin manyan maƙiyanta kuma jagoran ƙungiyar masu tayar da ƙayar baya da aka fi sani da Boko Haram, wato Abubakar Shekau, ya rasa ransa a wani artabu tsakanin mabiyansa da mambobin ɗaya ƙungiyar ita ma mai…
