Editor

9513 Posts
Saraki ga ‘yan Nijeriya: Ramadan makaranta ce, mu siffantu da darussan da muka koya

Saraki ga ‘yan Nijeriya: Ramadan makaranta ce, mu siffantu da darussan da muka koya

Daga Aisha ASAS, Abuja Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa ta Nijeriya, Dr. Abubakar Bukola Saraki ya taya ɗaukacin al’ummar musulmin Nijeriya murnar kammala azumin Ramadana na wannan shekara ta 2021, tare kuma da yi musu barka da sallah. Saraki a wata takardar manema labarai, mai ɗauke da sa hannun shugaban sashen ofishin watsa labaransa, Yusuph Olaniyonu ya shawarci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da neman kusanci ga Allah tare da yin addu’ar samuwar mafita ga Nijeriya. Ya ƙara da cewa, watan azumin Ramadana ba kawai ya taƙaita ga kyautata halaye na tsawon kwanaki 30 ba ne, lokaci ne da ya kamata mu…
Read More
Gwamna Uzodinma ya sauke kwamishinoni 20

Gwamna Uzodinma ya sauke kwamishinoni 20

Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo, ya sauke kwamishinoninsa 20 sannan ya rushe majalisar zartarwa ta jihar. An bada sanarwar hakan ne jim kaɗan bayan kammala taron majalisar a Laraba a Owerri, babban birnin jihar. Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Declan Emelumba, ya shaida wa manema labarai cewa dalilin rushe majalisar shi ne, don sake wa gwamtin jihar tsare-tsaren gudanar da ayyukanta yadda ya kamata bayan da Gwamna Uzodinma ya cika shekara ɗaya da soma mulkin jihar. Ya ƙara da cewa, daga cikin kwamishinoni 28 da jihar ke da su guda 8 ne kawai suka tsira. Waɗanda…
Read More
Tsoron kamun hukuma: Nnamdi Kanu ya tsere daga Landon

Tsoron kamun hukuma: Nnamdi Kanu ya tsere daga Landon

Daga WAKILINMU Rahotanni daga Tarayyar Turai sun nuna jagoran tsagerun IPOB, Nnamdi Kanu, wanda ya yi gudun neman mafaka, ya tsere daga Landan gudun kada hukuma ta kama shi. A cewar jaridar The Will Nigeria, Kanu ya tsere ne bayan da ya samu labarin Gwamnatin Nijeriya ƙarkashin shugabancin Muhammadu Buhari, ta yinƙura domin ta kamo shi a can inda ya tafi neman mafaka. Kimanin makonni biyu da suka gabata, Gwamnatin Nijeriya ta aike da takardar neman kama Kanu zuwa Tarayyar Turai ta Ma'aikatar Harkokin Wajen. Samun masaniya a kan haka aka ce Kanu ya hanzarta tattara komatsansa ya bar Landan…
Read More
Rundunar sojoji ta soma bincike kan zargin kashe mai tallar kankana a Zamfara

Rundunar sojoji ta soma bincike kan zargin kashe mai tallar kankana a Zamfara

Daga UMAR M. GOMBE Biyo bayan zargin kashe wani mai sayar da kankana da aka yi cewa wani soja ya yi a Zamfara, Rundunar Sojoji ta Nijeriya ta ce ta soma bincike domin gano gaskiyar lamari. Rundunar ta ce muddin ta bincika ta gano cewa zargin da aka yi ya tabbata gaskiya, za ta hukunta jami'in da ta samu da hannu cikin badaƙalar daidai da doka. Rundunar ta bayyana haka ne cikin sanarwar da da ta fitar a Talatar da ta gabata ta hannun Daraktan Sashenta na Hulɗa da Jama'a, Brigadier General Mohammed Yerima. A cikin wannan makon ne labari…
Read More
Almundahana: EFCC ta sake raba Diezani da Dala milyan $153

Almundahana: EFCC ta sake raba Diezani da Dala milyan $153

Daga WAKILINMU Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC), ta sanar da ƙwato Dala milyan $153 daga hannun tsohuwar ministar man fetur, Diezani Alison Madueke, wadda ta tsere zuwa Ƙasar Birtaniya a 2015. Jaridar Vanguard ta ambato shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa yana cewa sun ƙwace aƙalla kadarori 80 da kudinsu ya kai Dala milyan $80. A cewar Abdulrasheed, “Muna fatan ganin lokacin da, wataƙila, za ta shigo ƙasar nan, kuma tabbas za mu yi nazari kan abubuwan da ta yi, sannan mu san matakin da za mu ɗauka nan gaba. Tabbas ba mu yi…
Read More
Sheikh Ɗahiru Bauchi ya gabatar da sallar idi

Sheikh Ɗahiru Bauchi ya gabatar da sallar idi

Daga MU'AZU HARƊAWA Yayin da galibin al'ummar musulmin Nijeriya ke cika azumi 30 a yau Laraba sannan a tashi da salla gobe Alhami, shi kuwa Sheikh Dahir Bauchi da mabiyansa yau take salla a gare sun inda tuni Sheikh da mabiyansa a Bauchi suka gabatar da sallar Eidul Fitr a. wannan Laraba. Yayin huɗubarsa, malamin ya ja hankalin mutane da su zauna da juna lafiya, tare da cewa a bar kowa kan ra'ayinsa. Bayanai daga sakatarorin shehun malamin sun ce Sheikh da mabiyansa sun yi sallarsu a yau ne saboda ganin wata da ya tabatta wanda a cewarsu abin da…
Read More
Mazauna Abuja ku gabatar da sallar Idi a masallatan Juma’ar yankunanku – Hukuma

Mazauna Abuja ku gabatar da sallar Idi a masallatan Juma’ar yankunanku – Hukuma

Daga AISHA ASAS Hukumar Birnin Tarayya, Abuja, ta ce a masallatan Juma'a ne mazauna birnin za su gabatar da sallar Idi ƙarama. Hukumar ta cim ma wannan matsaya ne yayin wani taro da Ministan Abuja, Malam Muhammad Musa Bello tare da tawagar majalisar malaman Abuja ƙarƙashin jagorancin Imam (Dr) Tajudeen M.B Adigun, suka gudanar Litinin a Abuja don tattauna yadda za a gabatar da sallar Idi mai zuwa. Da yake jawabi, Ministan ya nuna godiyarsa ga malaman game da irin haɗin kan da suke bayarwa a fagen yaƙi da cutar korona a birnin tarayya. Ministan ya ce bisa la'akari da…
Read More
Ba a ga watan Shawwal a Nijeriya ba

Ba a ga watan Shawwal a Nijeriya ba

Kwamitin Duban Wata na Ƙasa ya ce babu wata alamar ganin watan Shawwal a Nijeriya a yau Talata, 11 ga Mayu, don haka gobe Laraba, 12 ga Mayu shi ne 30 ga Ramadan. Kwamitin ya ce nan gaba kaɗan Mai Martaba Sarkin Musulmi zai yi wa al'umma jawabi.
Read More
Gwamnonin Kudu sun haramta kiwo barkatai a yankinsu, sun buƙaci a sake fasalin ƙasa

Gwamnonin Kudu sun haramta kiwo barkatai a yankinsu, sun buƙaci a sake fasalin ƙasa

Yayin wani taro da suka gudanar a ranar Talata a Asaba babban birnin jihar Delta, gwamnonin Kudu sun yi ittifaƙi kan haramta kiwo barkatai a yankinsu. Cim ma wannan matsaya da gwamnonin suka yi hakan ba ya rasa nasaba da matsalar tsaron da suka ce yankin nasu na fama da ita. Kazalika, yayin taron nasu gwamnonin sun ƙalubalanci Gwamnatin Tarayya a kan ta gaggauta sake fasalin ƙasa domin magance matsalolin tsaron da ke ci gaba da cinye wa ƙasa tuwo a ƙwarya.
Read More
Kalu ya yi tir da harin da aka kai wa ofishin INEC a Abiya

Kalu ya yi tir da harin da aka kai wa ofishin INEC a Abiya

Daga WAKILINMU Tsohon gwamnan Jihar Abiya wanda kuma shi ne mai tsawatarwa a Majalisar Dattawa, Dakta Orji Uzor Kalu, ya yi Allah-wadai da harin da wasu ɓatagari su ka kai wa ofishin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa na Ƙaramar Hukumar Ohafia da ke jihar. Shi dai ofishin na INEC, wasu waɗanda ba a san ko su waye ba ne su ka banka masa wuta a ranar Lahadi, inda su ka lalata kayayyakin zaɓe da wasu kadarorin. A yayin da ya ke bayyana harin da cewa ya saɓa wa tsarin dimokiraɗiyya kuma rashin wayewa ne, Kalu ya yi kira ga jami'an tsaro…
Read More