Editor

9513 Posts
Mutum 11 sun halaka a harin makaranta a Rasha

Mutum 11 sun halaka a harin makaranta a Rasha

Daga UMAR M. GOMBE Rahotanni daga Ƙasar Rasha sun nuna a ƙalla mutum 11 waɗanda galibinsu yara ne, suka mutu a harin da aka kai wata makaranta da ke yammancin Kazan a ƙasar. Kamfanin dillancin labarai na RIA da ke ƙasar, ya ruwaito cewa a ƙalla yara 16 zuwa 12 da kuma wasu mayan su 4 ne aka kwantar a asibiti bayan harin a Talatar da ta gabata. A cewar kamfanin dillancin labarai na Interfax, wasu 'yan bindiga biyu ne suka buɗe wa makarantar wuta inda suka yi ta harbin kan mai uwa dawabi. Hoton bidiyon harin da aka yaɗa…
Read More
Bayan shekara 38 da kammalawa, Minista Dare ya ziyarci tsohuwar makarantarsu a Jos

Bayan shekara 38 da kammalawa, Minista Dare ya ziyarci tsohuwar makarantarsu a Jos

Ministan Harkokin Matasa da Wasannin Motsa Jiki, Sunday Dare, ya ziyarci sakandaren da ya yi karatu a Jos shekaru 38 da suka gabata. Dare ya ziyarci Baptist High School ne don halartar bikin cika shekara 60 da kafuwar makarantar. A saƙonsa da ya wallafa a shafinsa na twita, ministan ya ce ziyarar da ya kai makarantar ta tuna masa baya, sannan ɗalian sun cika da murnar ganin sa a tsakaninsu. An ga ministan a tsakanin ɗalibai sa'ilin da yake yi musu jawabi da kuma lokacin da yake ɓarje rawarsu ta gargajiya tare da wasu daga cikin ɗaliban.
Read More
Yaƙi da korona: Gwamnati ta dawo da dokar taƙaita zirga-zirga

Yaƙi da korona: Gwamnati ta dawo da dokar taƙaita zirga-zirga

Daga AISHA ASAS Gwamnatin Tarayya ta dawo da dokar taƙaita zirga-zirga a faɗin ƙasa daga ƙarfe 12 na dare zuwa 4 na asuba na kowace rana a matsayin wani mataki na ci gaba da yaƙi da cutar korona. A cewar Dr Mukhtar Mohammed wanda mamba ne a Kwamitin Shugaban Ƙasa kan yaƙi da annobar korona, wannan doka ta soma aiki ne daga tsakar daren Litinin, 10 ga Mayu, 2021. Kazalika, Mohammed ya ce daga ranar Talata, 11, Mayu, 2021, an haramta buɗe wuraren shaƙatawa (nihgt clubs), gidajen motsa jiki da sauaransu, har sai abin da Allah Ya yi. Ya ƙara…
Read More
Ɓarayi sun yi yinƙurin shiga gidan Ibrahim Gambari a Abuja

Ɓarayi sun yi yinƙurin shiga gidan Ibrahim Gambari a Abuja

Daga FATUHU MUSTAPHA Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da cewa ɓarayi sun yi yinƙurin shiga gidan Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ibrahim Gambari, da ke fadar shugaban ƙasa a Abuja da subahin Litinin da ta gabata. Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, ya ce wannan yinƙuri ne mara kan gado da ɓarayin suka yi wanda ba su kai ga cim ma manufarsu ba. A wani mai kama da wannan, Shehu ya ce a halin da ake ciki 'yan sanda sun bazama neman wani ɓarawo ruwa a jallo wanda shi ma ya yi yinƙurin shiga gidan Maikano Abdullahi…
Read More
Wanda ya tsara tutar Nijeriya ya cika shekara 85 da haihuwa

Wanda ya tsara tutar Nijeriya ya cika shekara 85 da haihuwa

A bana Chief Michael Taiwo Akinkunmi, OFR, ya cika shekara 85 da haihuwa. Akinkunmi shi ne talikin da ya tsara tutar Nijeriya kamar yadda ake ganin ta a yau. Tuni 'yan ƙasa suka shiga yi masa fatan alheri bisa zagayowar ranar haihuwarsa tare da yaba wa fasaharsa wajen samar wa Nijeriya tuta mai tsari wadda ta samu karɓuwa da tagomashi a faɗin duniya.
Read More
Buhari ya jajanta wa iyalan waɗanda haɗarin jirgin ruwa ya ratsu da su a Neja

Buhari ya jajanta wa iyalan waɗanda haɗarin jirgin ruwa ya ratsu da su a Neja

Daga FATUHU MUSTAPHA Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya nuna alhinisa dangane da haɗarin jirgin ruwan da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 28 a jihar Neja. Kamar yadda hadiminsa kan sabbin kafafen yaɗa labarai, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na twita a wannan Litinin, Shugaba Buhari ya nuna tausayawarsa kan ibtila'in, kana ya jajanta wa ahalin waɗanda suka rasu a haɗarin da ma waɗanda suka ji rauni. A cewar Buhari haɗarin abin tashin hankali ne musamman ma kasancewar wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa 'yan gudun hijira ne masu neman mafaka. Buhari ya yaba da ƙoƙarin duka waɗanda suka…
Read More
Gwamnati ta bada hutun kwana biyu albarkacin bikin sallah

Gwamnati ta bada hutun kwana biyu albarkacin bikin sallah

Daga BASHIR ISAH Gwamnatin Tarayya ta bayyana Laraba 12 da Alhamis 13 ga Mayu, 2021, a matsayin ranakun hutu na gama-gari domin bikin ƙaramar sallah na bana. Ministan Harkokin Cikin Gida, Ogbeni Rauf Aregbesola, shi ne ya sanar da hakan a ranar Litinin a Abuja a madadin Gwamnantin Tarayya. Aregbesola ya yi amfani da wannan dama wajen kira ga Musulmi 'yan Nijeriya na gida da ƙetare, da su yi amfani da wannan dama wajen yi wa Nijeriya addu'ar samun zaman lafiya mai ɗorewa da daidaiton tattalin arzikin ƙasa yayin bikin na Idul Fitr. Ministan ya ce babu yadda za a…
Read More
Haɗarin jirgin ruwa ya ci mutum 28 a Neja

Haɗarin jirgin ruwa ya ci mutum 28 a Neja

Daga AISHA ASAS A ƙalla mutum 28 ne aka ruwaito sun mutu a wani haɗarin jirgin ruwa da ya auku a yankin ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja. Darakta Janar na Hukumar Bada Agajin Gaggawa na Jihar, Ahmed Inga ne ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) da aukuwar hakan a Minna, a Lahadin da ta gabata. A cewar Inga, fasinjojin da lamarin ya rutsa da su sun fito ne daga Zumba da nufin zuwa ƙauyen Tija a yankin ƙaramar hukumar Munya da ke jihar. Ya ci gaba da cewa haɗarin ya auku ne da yammacin Asabar da…
Read More
Hajjin bana: Muna jiran tabbaci daga bakin Saudiyya – NAHCON

Hajjin bana: Muna jiran tabbaci daga bakin Saudiyya – NAHCON

Daga WAKILINMU Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta bayyana jin daɗin ta game da bayanin da ya fito daga ƙasar Saudiyya cewa za a yi aikin Hajjin bana, tare da cewa bayanin wani albishir ne gare ta da ma al'ummar Musulmin duniya baki ɗaya. A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Babbar Jami'ar Hulɗa da Jama'a ta hukumar, Hajiya Fatima Sanda Usara, NAHCON ta bayyana cewa, duk da dai Saudiyya ba ta ambata cewa ko ƙasashen duniya za su yi aikin Hajjin na bana ba a taƙaitacciyar sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, hukumar na fatan cewa Hadimin Masallatan…
Read More
Bikin Sallah: Buhari ya buƙaci a kiyaye dokokin korona, ya soke gaisuwar sallah

Bikin Sallah: Buhari ya buƙaci a kiyaye dokokin korona, ya soke gaisuwar sallah

Daga UMAR M. GOMBE Shugaba Muhammadu Buhari ya kira ga 'yan Nijeriya da a kula tare da lura a lokacin bikin ƙaramar sallah na bana duba da cewa har yanzu annobar korona na ci gaba da yi wa duniya barazana. Mai magana da yawun Shugaban Ƙasa, Malam Garba Shehu, ya ce a bisa dalilai na annobar korona ya sa a bana Shugaba Buhari tare da iyalansa da manyan jami’an gwamnatinsa za su gudanar da sallar Idi a cikin Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, suna masu kiyaye dokikin da aka shata din yaƙi da cutar korona. Sanarwar da Garba Shehu…
Read More