Editor

9513 Posts
Hajjin 2021: Saudiyya ta tabbatar za a yi Hajji amma cikin matakai na musamman

Hajjin 2021: Saudiyya ta tabbatar za a yi Hajji amma cikin matakai na musamman

Daga WAKILINMU Ma’aikatar harkokin Hajji da Umura ta Ƙasar Saudiyya ta bada tabbacin cewa za a gudanar da Hajjin bana amma cikin matakan kariyar lafiya sakamakon annobar korona. A wata sanarwar da ta fitar a Lahadi, ma'aikatar ta ce za a yi Hajjin na bana ne bayan da aka tanadi matakai na musamman game da sha'anin tsaro da kuma kariya ga lafiyar mahajjata. “Hukumar lafiya ta Saudiyya za ta ci gaba da yin nazari a kan yanayin domin ɗaukar ƙwararan matakai don ganin cewa an kare lafiyar al’umma", in ji sanarwar. Ma’aikatar ta ce nan gaba kaɗan za ta bayyana…
Read More
IPOB ta yi kira ga Biden kada ya saurari buƙatar Buhari

IPOB ta yi kira ga Biden kada ya saurari buƙatar Buhari

Daga UMAR M. GOMBE Masu Fafutukar Kafa Biafra (IPOB) sun aika wa Shugaban Ƙasar Amurka, Mista Joe Biden, wasiƙa ta musamman inda suka yi kira ga gwamnatin Amurka da kada da yardar da buƙatar agajin da Shugaba Muhammadu Buhari ya nema a wajenta na ta shigo ta taya shi yaƙi da matsalar tsaron ƙasa. A cikin wasiƙar mai ɗauke da kwanan wata 1 ga Mayu, 2021 wadda ta samu sa hannun jagoran tsegerun, Nnamdi Kanu, IPOB ta shaida wa Shugaban Amurka cewa duk wani makami da Amurka za ta saida wa Nijeriya ƙarkashin mulkin Buhari, babu abin da zai ƙara…
Read More
Sojoji sun kama wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne a wani masallacin Kano

Sojoji sun kama wasu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne a wani masallacin Kano

Daga UMAR M. GOMBE Sojojin Nijeriya sun kai samame a wani masallaci da ake zargin na 'yan Boko Haram ne da ke Hotoro a Kano, inda suka cafke wasu mutum 10. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna an yi kamen ne da yammacin Asabar da ta gabata. Haka nan cewa sojojin sun aiwatar da aikinsu ne cikin ƙwarewa ba tare da ɗaga hankali kowa ba da ke yankin. Rahotanni sun suna wasu da suka yiwo gudun hijira daga Barno zuwa Kano a dalilin rikicin Boko Haram ne suka kafa masallacin. Ya zuwa haɗa wannan labari, da aka nemi jin…
Read More
Ƙungiyar Arewa ta yi takaicin milyoyin Naira da aka biya wajen kuɓutar da ɗaliban Kaduna

Ƙungiyar Arewa ta yi takaicin milyoyin Naira da aka biya wajen kuɓutar da ɗaliban Kaduna

Daga AISHA ASAS Ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF) ta bayyana damuwarta dangane da yadda akan biya kuɗaɗen fansa wajen kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su a hannun 'yan bindiga. Ƙungiyar ta bayyana damuwarta ne a wani bayanin da Sakatarenta na Hulɗa da Jama'a na Ƙasa, Emmanuel Yawe, ya fitar Asabar da ta gabata a Kaduna. ACF ta yi amfani da wannan dama wajen jinjina wa duka waɗanda suka sadaukar da ransu wajen tattaunawa da 'yan fashin dajin domin kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwa da su, musamman ma ɗaliban Jami'ar Greenfield, Kaduna. Ta ce “Mun gode wa Allah…
Read More
A nemi watan Shawwal ranar Talata, in ji Sarkin Musulmi

A nemi watan Shawwal ranar Talata, in ji Sarkin Musulmi

Daga FATUHU MUSTAPHA Majalisar Ƙoli ta Harkokin Musulunci ta Nijeriya (NSCIA), ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi kuma Sultan na Sakkwato, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III, ya buƙaci al'ummar Musulmi na ƙasa baki ɗaya su nemi jinjirin watan Shawwal a ranar Talata. Mataimakin Babban Sakataren NSCIA, Farfesa Salisu Shehu, shi ne ya sanar da hakan Asabar da ta gabata. A cewarsa, biyo bayan shawarar Kwamitin Neman Wata na Ƙasa (NMSC), a Talata mai zuwa, wato 11 ga Mayu 2021 wanda ya yi dai da 29 ga Ramadan, 1442, a wannan rana za a nemi watan Sahawwal. Majalisar ta ce idan Allah Ya…
Read More
An kashe ‘yan sanda 7 a hare-haren Rivers

An kashe ‘yan sanda 7 a hare-haren Rivers

Daga UMAR M. GOMBE Rundunar 'yan sanda ta jihar Rivers ta tabbatar da mutuwar wasu jami'anta su bakwai sakamakon hare-haren da 'yan bindiga suka kai a jihar. Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, SP Nnamdi Omoni, shi ne ya tabbatar da hakan A cewar jami'in, "Maharan sun kashe jami'ansu biyu a shingen binciken abubuwan hawa a ƙauyen Choba da ke tsakanin ƙaramar hukumar Obio/Akpor da ƙaramar hukumar Emohua, sannan suka banka wa wata mota mallakar ɗaya daga cikin jami'an da lamarin ya shafa." Kazalika, ya ce 'yan bindigar sun sake kai wa ofishin 'yan sanda hari a garin Rumuji…
Read More
Allah ya yi wa ‘Maman Taraba’, Sanata Aisha Al-Hassan rasuwa

Allah ya yi wa ‘Maman Taraba’, Sanata Aisha Al-Hassan rasuwa

Daga WAKILINMU Tsohuwar Ministar Harkokin Mata, Sanata Aisha Jummai Al-Hassan, wacce aka fi sani da suna Mama Taraba, ta rasu a wata asibitin ƙasar Masar, 7 ga Mayu, 2021. Wata majiya daga ahalin marigayiyar ce ta tabbatar wa Dateline Nigeria batun rasuwar. A halin rayuwarta, Jummai ta yi takarar kujerar gwamanan jihar Taraba a ƙarƙashin jam'iyyar APC a 2015. Ta riƙe muƙamin minista a gwamnatin Buhari. An haifi marigayiyar ce a Jalingo, a ranar 16 ga Satumban 1959.
Read More
Za a iya sace kowa a Arewa?

Za a iya sace kowa a Arewa?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Ba mamaki a iya sace kowa musamman in dai mutum na yawo a sassan arewacin Nijeriya da dare ne ko ma da rana tsaka. Wannan lamari na satar mutane don neman kuɗin fansa ta zama babbar masana'antar samun kuɗaɗe ga miyagun irin daji dama watakila wasu a cikin gari. Wata dabara ma da matafiya tsakanin Abuja da Kaduna ke yi ita ce bin jirgin ƙasa don kauce wa gamuwa da ɓarayin a titi a yankin nan na Rijana. Wannan dabarar ma akwai lokacin da ba ta ɓullewa don akwai labarin an sace mutane bayan sun sauka…
Read More