Babaji

5684 Posts

An tsaurara tsaro a Majalisar Dokokin Nijeriya yayin da mambobi ke zaman gaggawa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A yayin da ake shirye-shiryen fara zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya, ƴan majalisar dokoki suna gudanar da zama na gaggawa zauren Majalisar. Sakamakon haka ne aka tsaurara matakan tsaro a kewayen Majalisar, biyo bayan zargin zanga-zanga ka iya ɓarkewa da za ka iya haifar da dakatar da zaman. A ranar Lahadi ne ƴan Majalisar Dokokin su ka sanar da batun wanda hakan ya shafi kwanaki hutunsu na shekara da su ka fara a makonnin da su ka gabata. Wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan majalisar wakilai, Rotimi Akin ya fitar ta ce, zaman…
Read More

Zanga-zanga: Gwamnatin Katsina ta umarci a gaggauta rufe makarantu a jihar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnatin Jihar Katsina ta umarci a rufe dukkan makarantu a faɗin jihar. Sanarwar ta fito daga mai magana da yawun ma'aikatar ilimin ƙananan makarantu, Ɗanjuma Sulaiman inda ya ce gwamnatin ta ce a sanar da mutane musamman iyayen yara cewa hutun zai fara ne daga ranar Laraba. Ya ƙara da cewa, hutun shi ne mafarin hutun zango na uku, ɗaya daga cikin zango-zango da makarantun ke yi a shekarar. Ya yi kira ga iyayen da su ɗakko ƴaƴansu da ke karatu a makarantun kwana zuwa gidajensu, ya na mai cewa dokar ta shafi makarantun kuɗi da…
Read More

Gwamnan Kano ya gayyaci ƴan zanga-zanga gidan gwamnati, ya yi gargaɗin tashin-tashina

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnati ba za ta lamunci duk wani nau'in tashin-tashina ba yayin da ake gudanar da zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya. Gwamnan ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da shugabannin ƴan kasuwa, sarakunan gargajiya da malaman addini a Fadar gwamnatin jihar da ke Kano a ranar Laraba. Abba Kabir ya ce, "zanga-zanga babu inda za ta kai mu. Ina kira ga waɗanda su ke ƙoƙarin aiki da ƴancinsu na yin zanga-zanga da su kaucewa nuna kowace irin halayya da gurɓatattu zasu yi amfani da…
Read More

‘Yan zanga-zanga sun ƙi amincewa da buƙatar Sufeton ‘Yan sanda ta yi a keɓaɓɓun wurare saɓanin kan titina

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Talata ne waɗanda su ka shirya zanga-zangar 'EndBadGovernance' da za a yi a watan Agusta su ka ƙi amincewa da buƙatar Sufeton 'Yan sanda, Kayode Egbetokun, ta neman su gudanar da ita a keɓaɓɓun wurare madadin fitowa kan tituna. Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da tsare-tsaren yadda zanga-zangar za ta gudana, a wani zama da aka yi da jagororin tafiyar da rundunar ƴan sandan. Egbetokun ya ce "ba dai-dai ba ne a yi gangami a kan titi da nufin yin zanga-zanga. Wasu kuma na shirya yin tashin-tashina". Lauya Ebun-Olu Adegboruwa (SAN)…
Read More

Zanga-zanga: Gwamnatin Tinubu na buƙatar taimakon ƴan Nijeriya don tabbatar da ayyukanta, inji Shettima

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Mai girma Mataimakin shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya aika saƙon neman taimakon ƴan Nijeriya kan ƙaddamar da shirye-shirye da ayyukan Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya na mai cewa shugaban ƙasar na nufin al'umma da alkhairi. Ya ce, jita-jita a wasu wurare na cewa Shugaba Tinubu na adawa da cigaban Arewa ko Musulunci ba haka ba ne, ya mai buga misali da cewa hakan da zai nuna yayin raba manyan muƙamai da Tinubu ya yi na ma'aikatu, hukumomi da ofisoshin wasu ɓangarori. Shettima ya faɗi hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin tawagar ƴan jarida…
Read More

DA ƊUMI-ƊUMI: Masu shirya zanga-zanga sun sanar da wuraren haɗuwa

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI A ranar Talata, 30 ga watan Yuli, masu zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin Nijeriya su ka fitar da wuraren da za a haɗu wanda za a fara daga ranar 1 zuwa 10 ga watan Agusta. An samu bayanin ne cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun wani lauya mai suna Ebun-Olu Adegboruwa (SAN) wanda shi ne Antoni Janar na masu shirya zanga-zangar inda a ciki ta ke cewa, saƙo ne zuwa ga Sufeto Janar na 'Yan sanda, Kayode Egbetokun. Takardar, ta zayyano wuraren da za a yi zanga-zangar da kuma nuni ga muhimmancin hakan…
Read More

Hukumar ‘Yan sanda ta sanar da fara horar da sabbin jami’ai bayan rikici da rundunar

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar kula da ƴan sanda, PSC ta sanar da lokacin fara horar da sabbin jami'ai bayan sa'insa tsakanin ta da rundunar kan jadawalin waɗanda aka ɗiba. Yayin da PSC ta fitar da sanarwar ɗaukar sabbin jami'ai 10,000, a ranar 4 ga watan Yuni, rundunar 'Yan sanda ta ƙi amincewa da hakan, ta na mai cewa akwai rashawa da ƙin bin hanyoyin da su ka dace wajen ɗaukar ma'aikatan a cikin hakan. Duk da matsayar rundunar, PSC ta ƙi sauya jadawalin wanda hakan ya sa Ministan harkokin Ƴan sanda, Ibrahim Gaidam ya shiga cikin lamarin tare da…
Read More

Gwamnan Zamfara ya ƙaddamar da aikin titin Magami-Ɗansadau

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya sanya hannu kan fara aikin hanyar Magami zuwa Ɗansadau wacce za ta kai tsawon kilo mita 108. Gwamnan ya gabatar da hakan ne a yayin zama da Majalisar Zartarwar Jihar a Fadar gwamnatin Zamfara a ranar Litinin. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta ce, hakan na zuwa ne la'akari da ƙoƙarin da gwamnatin Jihar ke yi kan matsalolin tsaro da ya addabi mutanen yankin. Dauda Lawal, "ya ƙaddamar da ƙwantiragin aikin ga kamfanin Gini na Ɗantata da Sawoe kasancewar sa wanda ya…
Read More

EFCC ta gayyaci Shugaban NAHCON kan aikin Hajjin 2024

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Hukumar hana yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati, EFCC ta gayyaci Shugaban hukumar jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Malam Jalal Arabi zuwa ofishinta da ke Jabi a Abuja. Rahoto daga 'News Point Nigeria' ya ce, EFCC ta gayyaci Arabi ne domin yin bayani game da yadda ya sarrafa Naira biliyan 90 da gwamnati ta bayar na tallafi ga Alhazan Hajjijn 2024. Haka kuma EFCC za ta gabatar da tuhume-tuhume kan Arabi da NAHCON ciki har da zargin rashin karrama Alhazan yadda ya dace a ƙasar Saudiyya yayin aikin hajjin. Mai magana da yawun EFCC, Dele Oyewale ya…
Read More

Zanga-zanga: Jami’ar Bayero ta ce za ta cigaba da aiki yadda aka saba

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI Yayin da kwanakin zanga-zangar tsadar rayuwa ke ƙara kusantowa a Nijeriya, Hukumar gudanarwa ta Jami'ar Bayero ta Kano, ta ce za a cigaba da gudanar da harkokin makarantar kamar yadda aka saba. Mataimakin shugaban reshen kula da harkokin al'umma na jami'ar, Lamara Garba ya faɗi hakan cikin wata sanarwa da ke ɗauke da sanya hannunsa inda ya bayyana cewa su na sane da batut fara zanga-zangar a ranar 1 ga watan Agusta. Hukumar gudanarwar ta sanar da al'umma cewa, za a cigaba da harkoki a jami'ar kamar yadda aka saba, ya na mai shawartar ma'aikata da…
Read More