19
Jun
Wani sashen babban kantin nan na Ado Bayero ya kama da wuta. Duk da cewar har yanzu ba a samu cikakken bayanin dalilin da yasa wutar ta kama ba, amma ma'aikatan kashe gobara sun halarci wurin. An hana mutane zirga zirga a sashen da wutar ta kama har sai ma'aikata sun gama aikinsu.
