17
Jun
"Akwai ƙalubale ga matasan marubutan da suka dogara ga rubutu" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Mata marubuta sun daɗe suna ba da gagarumar gudunmawa a ɓangaren cigaban adabi da harkokin rayuwa, saboda burin su na ganin sun kawo gyara a cikin al'umma da irin damar da suke da ita. Safna Aliyu Jawabi wata fitacciyar marubuciyar yanar gizo ce, daga Jihar Neja, wacce ta yi suna wajen fitar da littattafai da ke cike da darussa masu muhimmanci. A zantawarta da wakilin Manhaja a Jos, , Safna ta shaida masa cewa, burinta na amfani da muryarta wajen kawo sauyi a rayuwar al'umma shi…
