ukarofi

12504 Posts
Kwamishinan Gombe ya ƙaddamar da sabon tsarin sa ido kan ƙananan hukumomi

Kwamishinan Gombe ya ƙaddamar da sabon tsarin sa ido kan ƙananan hukumomi

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Kwamishinan ma'aikatar ƙananan hukumomi da raya al’umma ta Jihar Gombe, Barrista Sani Ahmed Haruna, ya ƙaddamar da wani sabon tsari na sa ido kan ayyukan ƙananan hukumomi, inda ya umarci sashen bincike, saka Ido da tantance ayyuka na ma’aikatar da ya riƙa gabatar da rahotannin bincike a duk wata. Ya bayyana cewa matakin na da nufin ƙarfafa sa ido kan yadda ƙananan hukumomi ke gudanar da ayyukansu, bunƙasa gaskiya da riƙon amana, tare da inganta isar da ayyukan gwamnati ga al’umma. Kwamishinan ya bayyana hakan ne yayin taronsa na farko da ma’aikatan sashen, inda ya…
Read More
FIFA ta kira taron gaggawa yayin da matsin lamba ke ƙaruwa kan buƙatar tsige Infantino

FIFA ta kira taron gaggawa yayin da matsin lamba ke ƙaruwa kan buƙatar tsige Infantino

Shugaban Hukumar ƙwallon ƙafa ta Duniya (FIFA), Gianni Infantino, ya kira taron gaggawa na manyan jami’an hukumar a birnin Rabat na ƙasar Moroko, yayin da ake ci gaba da fuskantar matsin lamba kan ya sauka daga muƙaminsa saboda wata taƙaddama da ta shafi shirin shigar da masu zuba jari masu zaman kansu cikin harkokin gudanar da gasar FIFA. Taron na ranar Laraba ya haɗa da Sakatare Janar na FIFA, Mattias Grafstrom, da mambobin kwamitin gudanarwar hukumar domin nazarin rikicin da ya biyo bayan shirin kafa kamfanin FIFA Forward Enterprise (FFE), wanda daga bisani aka soke. Wannan na zuwa ne a…
Read More
Sayen Vinicius babban haɗari ne ga Arsenal – Given

Sayen Vinicius babban haɗari ne ga Arsenal – Given

Tsohon mai tsaron ragar Newcastle United, Shay Given, ya gargaɗi Arsenal cewa yunƙurin sayen tauraron Real Madrid, Vinicius Junior, na iya jawo wa ƙungiyar babban haɗari. Rahotanni sun bayyana cewa Arsenal na nazarin yiwuwar ɗaukar ɗan wasan na Brazil a wata yarjejeniya mai tsadar gaske, inda ake zargin kocin ƙungiyar, Mikel Arteta, ne ke jagorantar ƙoƙarin ganin an kawo shi zuwa arewacin birnin Landan. An ce wannan yunƙuri na nuna sabon matsayi da Arsenal ta kai bayan lashe gasar Firimiya ta Ingila, tare da nuna irin ƙarfin kuɗin da ƙungiyar ke da shi a kasuwar musayar 'yan wasa. Sai dai,…
Read More
Yadda Salah ya samu gagarumar tarba a Trabzonspor

Yadda Salah ya samu gagarumar tarba a Trabzonspor

ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Trabzonspor ta Turkiyya za ta tabbatar da sayen Mohamed Salah yayin da magoya bayanta suka yi masa tarba ta karamci a lokacin da ya isa Turkiyya. ɗaruruwan magoya baya sun taru a wajen filin jirgin saman Ataturk da ke Istanbul ranar Laraba yayin da Salah ya fito sanye da kaya masu launukan Trabzonspor. ɗan wasan gaban mai shekarA 34 ya bar Liverpool a ƙarshen kakar wasa da ta gabata bayan shekara tara a Merseyside, inda ya zura ƙwallaye 257. Ba a tabbatar da albashin da Salah zai samu a Trabzonspor ba, amma tunda shi ɗan wasa…
Read More
An bai wa Vozinha izinin amfani da laƙabinsa a Colo-Colo

An bai wa Vozinha izinin amfani da laƙabinsa a Colo-Colo

Hukumar ƙwallon ƙafa ta Chile (ANFP) ta amince ta bai wa mai tsaron ragar Cape Verde, Vozinha, damar sanya sunan da aka fi saninsa da shi a bayan rigarsa ta ƙungiyar Colo Colo. Dan wasan mai shekaru 40 ya rattaba hannu kan kwantiragin watanni shida da ƙungiyar ta Chile (Liga de Primera) a ranar Litinin, bayan ya samu yabo a duniya saboda rawar da ya taka a gasar cin kofin duniya. A bisa ƙa'idojin gasar, ya kamata ya buga wasa da sunansa na asali, wato Josimar Jose Evora Dias, kasancewar dokokin ANFP sun tanadi cewa "ba a yarda a sanya…
Read More
 ‘Yan bindiga sun sake kai sabon hari a Sakkwato, ana fargabar an kashe mutane da dama

 ‘Yan bindiga sun sake kai sabon hari a Sakkwato, ana fargabar an kashe mutane da dama

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ana fargabar mutuwar mutane da dama tare da sace wasu 37 a sabbin hare-haren da 'yan bindiga suka kai a ƙananan hukumomin Kebbe, Sabon Birni da Shagari na Jihar Sakkwato, yayin da wani Mataimakin Sufeton 'Yan Sanda (ASP), Bala Wakili, ya rasa ransa a fafatawa da maharan. Rahotanni sun nuna cewa marigayi ASP Bala Wakili, wanda ke aiki da Rundunar 'Yan Sandan Kebbe, ya mutu ne ranar Litinin bayan wata arangama mai zafi tsakanin jami'an tsaro da 'yan bindiga a yankin Kebbe. Majiyoyi sun ce maharan sun kai farmaki ƙauyukan Girkau da Zugu da…
Read More
Gwamnatin Kaduna ta bai wa mijin matar da aka ƙone da ranta gida, kuɗi da guraben karatun  yaransa

Gwamnatin Kaduna ta bai wa mijin matar da aka ƙone da ranta gida, kuɗi da guraben karatun  yaransa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kaduna ta bai wa Aliyu, mijin matar da ta mutu bayan wasu fusatattun mutane sun ƙone ta da ranta a Marabar Jos, kyautar gida, tallafin kuɗi da kuma guraben karatu kyauta ga iyalansa. Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ne ya miƙa mukullin gidan ga Aliyu a ranar Talata a Fadar Gwamnatin jihar, inda ya bayyana cewa gwamnati na da alhakin tallafa wa iyalan da suka faɗa cikin irin waɗannan munanan hare-hare. Tallafin ya biyo bayan mummunan lamarin da ya faru a Marabar Jos, inda wasu fusatattun mutane suka kashe matar Aliyu…
Read More
Sojoji sun ayyana shugaban ISWAP da mataimakinsa a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo

Sojoji sun ayyana shugaban ISWAP da mataimakinsa a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar Sojojin Nijeriya ta ayyana shugaban ƙungiyar Islamic State West Africa Province (ISWAP), Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa (Wali), da mataimakinsa, Amirul Jaish Muhammad Jidda, a matsayin waɗanda ake nema ruwa a jallo, bayan bayanan sirri da aka samo daga na'urorin fasaha da aka ƙwato a hare-haren da aka kai kan ƙungiyar a yankin Tafkin Chadi. Muƙaddashin Jami'in Yaɗa Labarai na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai (OPHK), Kyaftin Muhammed Goni, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba. Ya ce an gano shugabannin ne bayan…
Read More
AIG Garba Ahmed ya yi wa Jami’ar KHAIRUN alƙawarin cikakken goyon bayan ‘yan sanda

AIG Garba Ahmed ya yi wa Jami’ar KHAIRUN alƙawarin cikakken goyon bayan ‘yan sanda

Daga RABIU SANUSI a Kano Mataimakin Sufeto Janar na 'Yan Sanda (AIG) mai kula da Shiyya ta Daya da ke Kano, Garba Ahmed, ya tabbatar wa Jami'ar Khalifa Isyaku Rabiu (KHAIRUN) da ci gaba da ba ta cikakken goyon baya domin tabbatar da ingantaccen tsaro da samar da yanayi mai kyau na koyarwa, koyo da ci gaban al'umma. AIG Ahmed ya bayyana hakan ne yayin da Mataimakin Shugaban Jami'ar, Farfesa Abdulrashid Garba, ya jagoranci tawagar jami'ar zuwa hedikwatar Shiyya ta Daya da ke Kano domin ziyarar girmamawa. A jawabinsa, Farfesa Abdulrashid Garba ya ce jami'ar na da kyakkyawar alaƙa da…
Read More
Ana ci gaba da addu’a da tunawa da Malam Adamu Direba shekaru 11 bayan rasuwarsa

Ana ci gaba da addu’a da tunawa da Malam Adamu Direba shekaru 11 bayan rasuwarsa

Daga MUHAMMAD MUJITABA a Kano An ci gaba da gudanar da addu'o'i da tunawa da marigayi Malam Adamu, tsohon direba da aka bayyana a matsayin mutum mai kyakkyawar mu'amala, zaman lafiya da kuma bayar da gudunmawa ga al'umma, shekaru 11 bayan rasuwarsa. Iyalan marigayin, 'yan uwa da abokan arzikinsa sun ce har yanzu ba su manta da shi ba, kuma suna ci gaba da yi masa addu'a tare da tuna kyawawan halayensa. An haifi Malam Adamu a ranar 2 ga Fabrairu, 1920, sannan ya rasu a ranar 17 ga Janairu, 2015. Da yake jawabi a wajen taron addu'ar, shugaban masu…
Read More