ukarofi

12345 Posts
KPF ta yi Allah-wadai da sake ɓullar ƙalubalen tsaro a jihar Kano

KPF ta yi Allah-wadai da sake ɓullar ƙalubalen tsaro a jihar Kano

Daga Ibrahim Hamisu, Kano Kungiyar ƴan kishin Kano tsantsa wato Kano Patriotic Front (KPF) ta bayyana matukar kaɗuwar ta tare da yin Allah-wadai da yadda matsalar tsaro ta sake kunno kai a jihar Kano, musamman hare-haren Ƴandaba da ke haddasa asarar rayuka da dukiyoyi. A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban ƙungiyar Manjo Janar Ibrahim Sani (mai ritaya)da mataimakinsa Alh. Ahmed Shehu Yakasai, ƙungiyar ta buƙaci gwamnatin jihar Kano da jami’an tsaro da su kara zage damtse wajen ganin an kawo ƙarshen hare-haren da ake kaiwa ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.Dakarun kishin…
Read More
Kano a shirye take ta tunkari ɓarkewar kwalera da sauran cututtuka – Darakta Janar na KNCDC

Kano a shirye take ta tunkari ɓarkewar kwalera da sauran cututtuka – Darakta Janar na KNCDC

Daga Ibrahim Hamisu, Kano Кari ga shawarwarin da Kwamishinan Lafiya na Jihar Kano ya bayar kan yadda al’ummar jihar Kano za su yi ta’ammali da ruwan sama, Cibiyar Daƙile Cututtuka Masu yaɗuwa ta Jihar Kano (KNCDC) ita ma ta bayar da shawarwarin yadda mutane za su kare kansu daga kamuwa da cutar ta kwalara. Darakta Janar na Cibiyar, Farfesa Muhammad Abbas ya ja hankalin al’ummar jihar Kano da kada su ɗauki lamarin cutar kwalara da wasa, saboda mummunan abin da take tattare da shi ga al’umma. A wata sanarwar manema labarai da jami'in hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Lafiya Ibrahim…
Read More
DA ƊUMI ƊUMI: Gobara ta tashi a matatar Dangote

DA ƊUMI ƊUMI: Gobara ta tashi a matatar Dangote

Gobara ta kama wani sashen matatar mai na Ɗangote dake kusa da Lekki jihar Legas. Masu bada agajin gaggawa sun hallara wurin kan lokaci domin kashe wutar wanda suka yi nasara. Sai dai ba wanda ya rasa rai kuma kawo yanzu ba a son dalilin da ya jawo gobarar ba. A halin yanzu har an fara bincike domin a gano dalilin tashin gobarar. A wata sanarwa da kamfanin matatar man ya fitar sunce ba wani abun damuwa bane, don har ma an fara bincike domin gano abinda ya faru har gobarar ta tashi.
Read More
Rubutun adabi na samun bunƙasa sosai a Nijar – Mrs Sadauki 

Rubutun adabi na samun bunƙasa sosai a Nijar – Mrs Sadauki 

"Yadda lamarin aurena ke watsewa da zarar an soma zance ya sa nake kiran kaina matar Sadauki" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  A Jamhuriyar Nijar ma ana da marubutan littattafan Hausa na zamani da dama, wasu daga cikinsu har duniya ta shaida ƙoƙarin su, inda suka taka rawar gani a gasar Hikayata ta BBC Hausa. Chamsiya Laouali Rabo, na daga cikin matasan marubuta masu hazaƙa da basirar rubutu mai cike da darussa da yawa. Idan kai mai tsoron karanta labaran aljanu ne ko matsafa da masu ƙungiyar asiri to, ka guji karanta littattafan Chamsiya da daddare, don kuwa gwana ce wajen…
Read More
Ina da kyakkyawar fatan yin nasara a aikin fim ɗin da zan yi – Furodusa Kabiru Lawan

Ina da kyakkyawar fatan yin nasara a aikin fim ɗin da zan yi – Furodusa Kabiru Lawan

Daga MUKHTAR YAKUBU A 'yan kwanakin da suka gabata ne aka yi wani taro na tantance jaruman da za su fito a wani sabon fim da Kamfanin Mai'atamfa Warure Mutimidia yake shirin fara aikin sa nan da ɗan lokaci mai zuwa.  Taron tantancewa da aka gudanar a ofishin kamfanin Mai'atamfa Warure Mutimidia da ke Ƙofar Dukawuya a kan titin zuwa Tsohuwar Jami'ar Bayero a cikin garin Kano, ya ɗauki wani sabon salon da ba a saba ganin irin sa ba a duk lokacin da aka shirya taron tantancewa Jaruman da ake son shigar su cikin wani fim. Domin kuwa aƙalla…
Read More
Abdulkareem zai isa Ƙasar Lithuania don halartar bita kan hana cin hanci

Abdulkareem zai isa Ƙasar Lithuania don halartar bita kan hana cin hanci

Daga AISHA ASAS  Ƙwararren mai shirya finanninai, kuma mai kula da shirye-shirye a kampanin moving image limited, mazaunin Kano, Abdulkareem Mohammed zai wuce Ƙasar Lithuania don halartar bita ta ƙasa da ƙasa kan hana cin hanci (IACC)  na 2024. Yayin magana da Nigerian Kicker ranar Juma'a a ofishinshi da ke cikin garin Kano, Mohammed, wanda ake sa ran zai bar Nijeriya a ranar Asabar ya bayyana cewa, aƙalla ana tsammanin mutane 1000 zasu halarci wannan taro daga ƙasashe 120. Ana sa ran zai yi sharhi mai taken Yammacin Labarai: Magance Rashawa Ta Hanyar Hakokkki a sahen su na yamma wanda…
Read More
Mawaƙi Rema ya kafa tarihi a duniyar waƙa

Mawaƙi Rema ya kafa tarihi a duniyar waƙa

Daga AISHA ASAS  Mawaƙi Rema ya kafa tarihi a duniyar waƙoƙi ko in ce a mawaƙan Afrika, inda waƙarsa ta 'Baby Calm Down' ta zama waƙar Afirka da aka fi sauraro a Amurka. Waƙar Calm Down ta mawaƙin Najeriya, Rema ta ci gaba da kafa tarihi, inda ta zamo ta ɗaya a cikin waƙoƙin ƴan Afirka (Afrobeats) da aka fi sauraro a Amurka. Haka nan ta zamo waƙar ƴan Afirka ta farko a tarihi da aka saurara sama da sau biliyan ɗaya a Amurka, kamar yadda shafin lura da waƙoƙi na Chart Data ya bayyana a shafinsa na X. Ko…
Read More
Aikin gwamnati akwai ƙalubale a ciki musamman ga ‘ya mace – Laure Maso Kano

Aikin gwamnati akwai ƙalubale a ciki musamman ga ‘ya mace – Laure Maso Kano

"Burina na kafa gidauniya don taimaka wa mata" Daga ABUBAKAR A. BOLARI, a Gombe  Hajiya Laure Umaru Masokano, tsohuwar malamar makaranta ce a garin Nguru ta Jihar Yobe a Arewa maso gabas na tarayyar Nijeriya kuma 'yar kasuwa, gogaggiyar ma’aikaciyar gwamnati wacce ta yi ilimin ta a ɓangaren ilimin shari’a da na arabiya, wato Islamic studies. A zantawarta da shafin Gimbiya na jaridar Manhaja, ta bayyana tarihin rayuwar ta da ma wasu ɓangarori daban. Ku biyo mu ku sha karatu: MANHAJA: Za mu so ki gabar da kanki ga masu karatunmu. HAJIYA LAURE: Sunana Hajiya Laure Umaru Masokano ni haifaffiyar…
Read More
Salman Dogo ya kama aiki a matsayin sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano

Salman Dogo ya kama aiki a matsayin sabon Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano

Salman Dogo ya kama aiki a matsayin sabon Kwamishinan 'Yan Sandan Kano a matsayin kwamishina na 46 ga jihar. An haife shi 21 ga watan Yuli 1966 a Illorin, jihar Kwara. Salman Dogo ya fi shekara 30 da shiga aikin ɗan sanda. Salman Dogo ya shiga aikin ɗan sanda a shekarar 1992, ya riƙe mukamai da dama a ƙasar nan kamar jagorancin sashen da ke kula fashi da makami na rundunar yan sanda wanda ake kira "Anti robbery squad". Ya taɓa rike muƙamin Area Commander a jihohin Legas, Kaduna da kano. Yayi mataimakin kwamishina a jihar Anambra da Bauchi. A…
Read More
‘Ƴan ta’adda na amsar harajin miliyan N20 a Benuwai

‘Ƴan ta’adda na amsar harajin miliyan N20 a Benuwai

Wasu 'ƴan bindiga dake zaune a yankin karamar hukumar Ukum ɗin jihar Benuwai sun fara amsar haraji daga ƙauyukan dake cikin ƙaramar hukumar. Wani dan garin da ke bayani, yace yan bindigar sun fara ɗorawa gidaje harajin miliyan N20. Ya cigaba da bayani yana cewa, yanzu halin da ake ciki kowanne gida an yanke masa abinda zai rinka biya domin a samu a haɗa kuɗin harajin kafin watan ya ƙare. Ya ƙara da cewa babu wanda ya isa a garin yanzu haka yayi jayayya ko kuma sanar da hukuma halin da ake ciki, saboda waɗannan 'ƴan ta'addan sunyi karfi. Sunan…
Read More