24
Jun
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani jigo a Jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Buba Galadima, ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya yi taka-tsan-tsan wajen tsoma baki a siyasar jihar Kano. Galadima ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Arise a ranar Litinin. Ya ce, “Ya kamata gwamnatin tarayya da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu su yi taka-tsan-tsan da shiga siyasar Kano. Zai lalata shugabancinsa.” Ya yi Allah wadai da goyon bayan da gwamnatin tarayya ke baiwa wata ƙungiya a siyasar Kano, yana mai cewa bai kamata hukumomin tarayya su karkata kan…
