ukarofi

12547 Posts
Gombe 2027: Tsohon hadimin gwamna ya fice daga APC zuwa PDP domin mara wa Pantami baya

Gombe 2027: Tsohon hadimin gwamna ya fice daga APC zuwa PDP domin mara wa Pantami baya

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Tsohon babban mataimaki na musamman ga gwamnan Jihar Gombe, Barrista Aliyu Musa, ya fice daga jam’iyyar APC tare da ɗaruruwan magoya bayansa zuwa jam’iyyar PDP domin nuna goyon bayansa ga takarar gwamnan PDP tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Farfesa Isa Ali Pantami. Aliyu Musa ya sanar da sauya sheƙarsa ne a ranar Asabar yayin wani taron siyasa da shirin Awareness and Unity Programme ya shirya a garin Billiri, hedikwatar ƙaramar hukumar Billiri ta Jihar Gombe. A cewarsa, matakin da ya ɗauka ya samo asali ne daga yadda yake ganin Pantami a matsayin shugaba…
Read More
An koka kan rashin halartar taron tunawa da Marigayi Mamman Shata a Katsina

An koka kan rashin halartar taron tunawa da Marigayi Mamman Shata a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Malami a jami'ar FUDMA Farfesa Bashir Aliyu sallau ya koka kan yadda mutane suka ƙaurace wa taron tunawa da Marigayi Alhaji Mamman Shata da ya gudana a Katsina. Sallau wanda ke riƙe da sarautan Sarkin Askan Yariman Katsina wanda ya gabatar da jawabi a wajen taron ya nuna takaicin sa ganin yadda mawaƙin ya bada gudunmuwa wajen cigaban ƙasa,samar da zaman lafiya da ɗaukaka harshen Hausa a idon duniya amma mutane ƙalilan suka halarci taron. Ya ce a shekarun baya irin wannan taron ɗimbin mutane daga sassan ƙasan suke halarta amma a cewar sa wannan…
Read More
Tinubu ya samar da buhu 200,800 na takin zamani ga jihohin Arewa maso Yamma

Tinubu ya samar da buhu 200,800 na takin zamani ga jihohin Arewa maso Yamma

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samar da buhun takin zamani buhu 200,800 ga ƙananan manoma dubu 25,200 a jihohin bakwai na Arewa maso Yamma inda kowane manomi zai sami buhu huɗu kyauta. Da yake ƙaddamar da rabon takin zamanin, gwamnan jihar Katsina wanda shine shugaban ƙungiyar gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma Malam Dikko Raɗɗa ya yi gargaɗin karkatar da takin a lokacin rabawa ya ce dole takin ya isa ga manoman da aka tsara za su amfana. "Muna gargaɗi kan karkatar da takin da aka bada kyauta dole ne ya isa ga manoman da…
Read More
Ya halaka maƙwabcinsa kan jarkar ruwa a Sakkwato

Ya halaka maƙwabcinsa kan jarkar ruwa a Sakkwato

Wani matashi mai suna Ibrahim Baba, ya kashe maƙwabcinsa, Abubakar Ahmad, bayan ɓarkewar taƙaddama kan jarkar ruwa a unguwar Sabon Titi a Jihar Sakkwato. Dan uwan mamacin, Umar Ahmad, ya ce marigayin ya rasu ya bar mata ɗaya da yara biyu, yayin da matarsa ke ɗauke da juna biyu. Ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan marigayin ya ɗauki wata tsohuwar jarkar ruwa da aka ajiye a wajen ɗibar ruwa, ya yanke samanta domin amfani da ita. Daga baya mai jarkar ta nemi a biya ta kuɗinta tun da an yi amfani da ita. A cewarsa, marigayin ya…
Read More
Har fitsarinmu muke sha a hanyar Libya saboda ƙishirwa – ’Yar Nijeriya

Har fitsarinmu muke sha a hanyar Libya saboda ƙishirwa – ’Yar Nijeriya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wata matashiya ’yar Nijeriya mai shekaru 23 mai suna Endurance Daniel ta bayyana irin wahalar da ta sha a tafiyarta zuwa ƙasar Libya, inda ta ce sun kai ga shan fitsarinsu, domin tsira da rayukansu a hamada saboda tsananin ƙishirwa. Endurance, wacce tana cikin ’yan Nijeriya 182 da ƙungiyar ƙasa da ƙasa kan gudun hijira ta taimakawa wajen dawo da su gida, ta ce, ta yi tafiyar tare da mutane 52 a cikin mota ɗaya, amma bakwai daga cikinsu sun rasu a kan hanya sakamakon yunwa, ƙishirwa da tsananin wahala. Ta bayyana cewa, an…
Read More
WiFi na iya gane mutum ba tare da kyamara ba, inji masana

WiFi na iya gane mutum ba tare da kyamara ba, inji masana

Masana kimiyya a Jamus sun ƙera wata sabuwar fasaha da ke amfani da siginar WiFi wajen gane mutum ba tare da amfani da kyamara ko na'urar ɗaukar hoto ba. A cewar masu binciken, fasahar na nazarin yadda siginar WiFi ke canjawa yayin da mutum ke motsawa ko tafiya a wani wuri. Ta hanyar amfani da ƙirƙirarriyar basira ta AI, tsarin na iya bambance mutum daga wani da kusan cikakkiyar daidaito. Masanan sun bayyana cewa wannan cigaba na iya taimakawa wajen inganta tsarin tsaro, kula da tsofaffi da marasa lafiya a gidaje, da kuma ayyukan ceto a lokutan gaggawa. Sai dai…
Read More
Likitoci sun gano katako a cikin kan wani mutum bayan shekaru biyu

Likitoci sun gano katako a cikin kan wani mutum bayan shekaru biyu

Likitoci a ƙasar Rasha sun yi mamakin gano wani katako mai tsawon inci biyar a cikin kan wani mutum, shekaru biyu bayan ya samu hatsari yayin da yake aikin sare itatuwa. Rahotanni sun bayyana cewa, katakon ya shiga ne ta kusa da idon mutumin bayan wani ɓangare na itace ya karye ya buge shi. Duk da raunin da ya samu a lokacin, bai fahimci cewa, wani ɓangaren katako ya maƙale a cikin kansa ba. Bayan shekaru biyu, mutumin ya fara fama da matsanancin ciwon kai da kumburi, lamarin da ya sa ya garzaya asibiti. Bayan an yi masa gwaje-gwaje da…
Read More
Fitattun taurarin da suka yi ridda zuwa Kiristanci a Nijeriya

Fitattun taurarin da suka yi ridda zuwa Kiristanci a Nijeriya

Daga AISHA ASAS  A Najeriya, addini ba kawai wata al’ada ba ce ko wani ɓangare na rayuwar yau da kullum. Wani ginshiƙi ne da ke taka muhimmiyar rawa wajen gina mutumtaka, al’adu da yadda jama’a ke kallon mutum. Wannan dalili ne ya sa duk wani canjin addini da ya shafi fitattun mutane ke zama abin jan hankali da muhawara cikin al’umma. A masana’antar nishaɗi ta Najeriya, inda rayuwar fitattun mutane ke ƙarƙashin hasken jama’a a kowane lokaci, sauya addini na ɗaya daga cikin batutuwan da kan tayar da ƙura. Yayin da da dama daga cikin mashahuran mutane ke ci gaba…
Read More
Yadda farashin sauya fasalin NNPC ya jawo cece-kuce, bincike da shari’o’i

Yadda farashin sauya fasalin NNPC ya jawo cece-kuce, bincike da shari’o’i

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPCL) yana fuskantar ƙarin matsin lamba bayan bayanan da suka bayyana cewa, an kashe kimanin Naira biliyan 5.9 wajen yi masa rajista, sauyin tsari da kuma sake fasalin kamfanin daga tsohon Kamfanin Man Fetur na ƙasa (NNPC) zuwa Kamfanin Mai na ƙasa na Nijeriya Mai Zaman Kansa (NNPCL) a ƙarƙashin tanade-tanaden Dokar Masana’antar Man Fetur (PIA). Abin da aka yi niyya ya zama wata sabuwar alama ta gudanar da harkokin kasuwanci da kyakkyawan tsarin shugabanci a kamfanin mai na ƙasa, ya rikiɗe zuwa wata gagarumar muhawara da ta haifar da fushin jama’a,…
Read More
‘Yadda Ibo suka mallake gidajen Legas suka maida Yarabawa ’yan haya’

‘Yadda Ibo suka mallake gidajen Legas suka maida Yarabawa ’yan haya’

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Fitaccen mawaƙin Nijeriya, Tobechukwu Melɓin Ejiofor, wanda aka fi sani da IllBliss, ya shiga tsaka mai wuya a kafafen sada zumunta bayan wata muhawara mai zafi da ta shafi zuba jari da mallakar filaye da al’ummar Ibo ke yi a Jihar Legas. Cece-kucen ya fara ne bayan da mawaƙin ya wallafa saƙo a shafinsa na ɗ (wanda aka fi sani da Twitter a baya), inda ya kare gudunmawar da al’ummar Ibo suka bayar ga tattalin arzikin Legas. A cewarsa, al’ummar Ibo sun taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa harkokin kasuwanci da kuma fannin gidaje a jihar. “’Yan…
Read More