ukarofi

12547 Posts
Bom ya fashe a kasuwar Legas

Bom ya fashe a kasuwar Legas

Daga USMAN KAROFI Wani abu da ake zargin na'urar IED ne ya fashe a kasuwar kayan takalma da ke Mushin a jihar Legas ranar Litinin, lamarin da ya jefa 'yan kasuwa da mazauna yankin cikin fargaba. Kwamishinan 'yan sanda na jihar Legas, Mista Fatai Tijani, ya tabbatar wa jama'a cewa jihar na nan cikin aminci, yana mai cewa jami'an tsaro sun yi gaggawar killace wurin tare da gudanar da bincike domin tabbatar da tsaron al'umma. Tijani ya bayyana cewa binciken farko ya nuna an ɓoye na'urar fashewar ne a ƙarƙashin wata mota ta gefen kujerar fasinja, kuma ya tashi ne…
Read More
PCRC ta yaba da sauye-sauyen IGP tare da jinjinawa Inuwa kan ƙarfafa tsaro a Gombe

PCRC ta yaba da sauye-sauyen IGP tare da jinjinawa Inuwa kan ƙarfafa tsaro a Gombe

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Kwamitin hulɗa tsakanin ‘yan sanda da al’umma (PCRC) a Jihar Gombe ya yaba da sauye-sauyen da sufeto janar na ‘yan sanda (IGP) ya ɓullo da su, yana mai bayyana su a matsayin muhimman matakai da za su ƙara ƙarfafa tsarin aikin ‘yan sanda na kusanci da al’umma, inganta amincewar jama’a ga rundunar ‘yan sandan Najeriya, da kuma bunƙasa tsaro a faɗin ƙasar nan. Shugaban PCRC na Jihar Gombe, Alhaji Garba Muhammad Ubale, ne ya bayyana hakan yayin wani taron hulɗa da al’umma da mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda (DIG) mai kula da shiyyar Arewa…
Read More
An ɗauke mata da ɗan shugaban jam’iyyar APC a Kebbi

An ɗauke mata da ɗan shugaban jam’iyyar APC a Kebbi

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Bayanai daga ƙaramar hukumar Yauri da ke jihar Kebbi sun bayyana cewa cikin daren Lahadi wayewar garin wannan Litinin waɗansu mutane kan babura sun yi dirar mikiya a gidan shugaban jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar mulki ta Yauri Alhaji Abu Manaja inda suka ɗauke matarsa da kuma ɗansa. Majiyoyin sun bayyana wa waƙilin jaridar Blueprint Manhaja da cewa da misalin ƙarfe uku na dare ne waɗansu mutane kan babura suka shiga gidan da ke anguwar GRA Yauri suka tafi da mutanen guda biyu sai dai kawo yanzu dai babu wani sahihin bayanin ko su wanene…
Read More
Sojoji sun kashe ‘yan bindiga biyu tare da raunata wasu a Katsina

Sojoji sun kashe ‘yan bindiga biyu tare da raunata wasu a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar sojoji na 17 brigade sun kashe 'yan bindiga biyu da raunata da dama sun kuma ƙwato makamai a wani samame da suka kai a dajin Ginchawa a ƙaramar hukumar Matazu. Sojojin sun kai samame bayan da suka sami sahihin bayanin maɓoyar 'yan bindiga a yankin. Kaman yadda mai magana da yawun rundunar ta 17 a Katsina,Kaftin Abayomi Adisa ya ce ,sojojin sun Kai mamaya ga 'yan bindigan a dajin Gachewa inda suka ta ɓarin wuta wanda har ya kai kashe 'yan bindiga biyu da yawa sun gudu suna ɗauke da raunuka. Ya ce sojojin…
Read More
Fatima al-Fihri: Matar da ta mayar da dukiya hasken da har yau bai gushe ba

Fatima al-Fihri: Matar da ta mayar da dukiya hasken da har yau bai gushe ba

Ba na son dukiyata ta ƙare tare da ni, saidai ta rayu bayan ni - Fatima al-Fihri  Daga AISHA ASAS Shafin Gimbiya na wannan makon dai ya ɗan bambanta da saura, domin yana ɗauke da tarihin da ba a samu takamaiman inganci ko kalma ɗaya kansa ba, duk da hakan bai hana shi zama abin faɗa ƙarni bayan ƙarni ba. Hakan kuwa ta faru ne ta dalilin ƙarfin namijin ƙoƙarin da ita Gimbiyar tamu ta wannan makon ta yi.  Idan kun shirya Aisha Asas ce za ta zama jagorar ku a wannan daɗaɗen tarihi.  MANHAJA: Shin wacce ce Fatima al-Fihri?…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya kai ziyara cibiyar haɗa kekunan lantarki

Gwamna Raɗɗa ya kai ziyara cibiyar haɗa kekunan lantarki

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya kai ziyara a cibiyar hada kekunan lantarki guda 500 masu amfani da hasken rana (Keke EVs) ta gwamnatin jihar da ke Katsina, inda aka yi gagarumin shiri na nufin sauya tsarin sufurin birane tare da samar da damammakin tattalin arziki masu ɗorewa ga al'ummar jihar. A yayin ziyarar duba aikin, mai bai wa gwamna shawara na musamman kan wutar lantarki da makamashi, Dakta Hafiz Ibrahim Ahmed, ya zagaya da gwamnan a cibiyar, inda ya yi masa cikakken bayani kan matsayin aiwatar da aikin, ciki har da yadda…
Read More
‘Yan sanda a Katsina sun kama mutum biyar kan zargin sata da sayar da kayan gwamnati

‘Yan sanda a Katsina sun kama mutum biyar kan zargin sata da sayar da kayan gwamnati

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta kama mutane biyar da ake zargi da haɗa baki, sata da sayar da kadarorin gwamnati a ƙauyen Bugaje, ƙaramar hukumar Jibia. Mai magana da yawun rundunar 'yan sanda a katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu eanda ya fitar da sanarwa ya ce kamen ya biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu. Waɗanda ake zargin sun haɗa da Hassan Ibrahim, Lawal Ibrahim, Abubakar Sani, Umar Isa da Ibrahim Rabiu. Bincike ya nuna cewa sun cire sassan wayoyin lantarki da wasu kayan gwamnati da suka lalace sakamakon iska, sannan suka sayar…
Read More
Tsuntsaye jan-baki sun lalata gonakin shinkafa a Kebbi

Tsuntsaye jan-baki sun lalata gonakin shinkafa a Kebbi

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi Tsuntsaye jan-baki da su kai hijira daga maƙwabtan jihohi, sunyi diran-mikiya akan gonakin shinkafa a ƙananan hukumomi biyar a Jihar Kebbi sun lalata shinkafa na dubban hekta, da akayi kimar kuɗin su, ɗaruruwan miliyan na Naira. A wani taron gaggawa na 'yan jarida da ya kira a ofishisa da ke Birnin Kebbi, Kwamishinan aikin gona na Jihar Kebbi, Alhaji Shehu Mu'azu, yace gwamnatin jihar tuni ta miƙe tsaye domin kawar da fitinar waɗannan miyagun tsuntsaye. "Muna samun labarin bayyanar jan-baki, ma'aikatar aikin gona, nan-da-nan ta tura rahoto ga Gwamnar Jihar Kebbi, Dakta Nasir…
Read More
‘Yan sanda a Kebbi sun tura jami’ai garin Tsamiya

‘Yan sanda a Kebbi sun tura jami’ai garin Tsamiya

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi Rundunar 'yan sanda ta Jihar Kebbi ta tura jami'an 'yan sanda masana dabarun-yaƙi zuwa Tsamiya sakamakon farmakin da 'yan ta'adda suka kai a garin da tsakar daren Asabar. Yan ta'addan sun dira a yanki suna ta harbe-harbe ba-ji-ba- gani, sannan kuma, suka cinna wuta akan wani shingen wucin-gadi na jami'an tsaro na sibil difens. A wata takardar sanarwa da jami'in hulda da jama'a, SP Bashir Usman ya bayar, a Birnin Kebbi, ya ce sun kuma ƙona wani gidan karuwai na ƙauye, da kuma gidan wani mutum da ake kira Sule mai goge, sannan…
Read More
APC ta lashe zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar Kebbi mai wakiltar Zuru

APC ta lashe zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar Kebbi mai wakiltar Zuru

Daga MUHAMMAD SADISU ABUBAKAR a Birnin Kebbi Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta, INEC, ta ayyana ɗan takarar jam'iyyar APC, Garba Aiki Rabi'u a matsayin wanda ya ci zaɓen cike gurbi na shiga Majalisar Dokokin Jihar Kebbi mai wakiltar mazaɓar Zuru, da aka gudanar a ranar Asabar, 20/6/2026. Jami'in bayyana sakamakon zaɓen, Farfesa Muhammad Bashar Danlami, na Jami'ar Gwamnatin Tarayya dake Birnin Kebbi, shi ne ya faɗi sakamakon zaɓen a Zuru a daren Asabar. Farfesa Danlami ya sanar da cewar Garba Aiki Rabi'u na jam'iyyar APC ya samu ƙuri’a 4871 wanda ya doke abokin takararsa Aliyu Galadima Muhammad na…
Read More