ukarofi

12550 Posts
Fatima Paga ta goyi bayan ƙudirin bai wa mata kujeru na musamman a majalisa

Fatima Paga ta goyi bayan ƙudirin bai wa mata kujeru na musamman a majalisa

Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe Jami'ar hulɗa ta UN Women ga gwamnan Jihar Yobe, Hajiya Fatima Muhammad Paga, ta yi kira ga 'yan majalisar tarayya da su amince da ƙudirin kujeru na musamman ga mata, tana mai bayyana shi a matsayin muhimmin mataki na ƙarfafa wakilcin mata a harkokin siyasar Najeriya. Paga ta ce amincewa da ƙudirin zai buɗe ƙarin damammaki ga mata domin su taka rawa sosai wajen tsara manufofi da yanke shawarar da suka shafi ci gaban ƙasa. A cewarta, duk da irin gudunmawar da mata ke bayarwa wajen bunƙasa al'umma, har yanzu ba su da isasshen wakilci…
Read More
Harin sama na Isra’ila a Lebanon ya yi sanadin mutuwar mutum 13

Harin sama na Isra’ila a Lebanon ya yi sanadin mutuwar mutum 13

Akalla mutum 13 ne suka rasa rayukansu sakamakon sabbin hare-haren sama da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon a ranar Laraba, kamar yadda majiyoyin tsaro na Lebanon suka bayyana, a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da matsa kaimi wajen kai farmaki kan kungiyar Hezbollah, yayin da ita kuma ƙungiyar mai samun goyon bayan Iran ke iƙirarin kai sabbin hare-hare kan dakarun Isra'ila a kudancin ƙasar. Rahotannin cikin gida sun nuna cewa cikin waɗanda suka mutu akwai mutum tara da suka rasa rayukansu a ƙauyen Dayr Debba, mai nisan kusan kilomita takwas daga gabashin birnin Tyre. Kamfanin dillancin labarai…
Read More
Firaministan Isra’ila ya tabbatar da shirin sake tsayawa takara bayan kalaman Trump da suka tayar da ƙura

Firaministan Isra’ila ya tabbatar da shirin sake tsayawa takara bayan kalaman Trump da suka tayar da ƙura

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai sake neman wa'adin mulki a zaɓen da ake sa ran gudanarwa a bana, kamar yadda jam'iyyarsa ta Likud ta tabbatar a ranar Laraba, bayan wasu kalamai daga Shugaban Amurka Donald Trump sun haifar da tambayoyi kan ko zai sake shiga takara ko kuwa. A cikin takaitaccen sanarwar da jam'iyyar Likud ta fitar, ta bayyana cewa Netanyahu zai tsaya takara a zaɓen, tare da nuna fatan cewa, da yardar Allah, zai sake samun nasara. Ko da yake har yanzu ba a ayyana ranar gudanar da zaɓen a hukumance ba, dokokin ƙasar sun tanadi cewa dole ne…
Read More
Cutar Ebola ta yi sanadin mutuwar jaririya bayan mutuwar mahaifiyarta a Kongo 

Cutar Ebola ta yi sanadin mutuwar jaririya bayan mutuwar mahaifiyarta a Kongo 

Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo ta sake tsintar kanta a tashin hankali sakamakon annoba mai tayar da hankali ta sake bayyana a gabashin Kongo bayan wata jaririya mai suna Buswaza ta rasa ranta sakamakon cutar Ebola, lamarin da ya sake fito da irin haɗarin da yara ƙanana da jarirai ke fuskanta a yayin barkewar wannan muguwar cuta. Rahotanni sun bayyana cewa bayan rasuwar mahaifiyarta a karshen watan Mayu, an kai Buswaza zuwa wani gidan marayu da Cocin Kirista ke gudanarwa a garin Bunia. Sai dai ba da jimawa ba limaman mata masu kula da gidan suka lura cewa jaririyar na fama da…
Read More
Kada a yi wannan fim don samar da zaman lafiya ga juna

Kada a yi wannan fim don samar da zaman lafiya ga juna

Daga ABDULYASSAR AMINU ABUBAKAR Duk lokacin da aka ce an rasa kusanceceniyar alaƙa da gundarin fahimta a koma wanne bigire ne, lallai babu wata hanya da za a fahimci juna har ma a shirya wasu abubuwan cigaba ko kuma da za a samu har ’yan baya ma su mora. Bari na yanke zancen. ɗazun kenan na ga wannan fasta da kamfanin Sultan Film Factory za su ɗauka (Aure Goma). Ban sani ba sun fara ‘shooting’ ko kuwa ba su fara ba, Allah shine mafi sani. To, amma Ina da shawara. Ga yadda na ga ya yi ‘posting’, alamu ya nuna…
Read More
Yadda shirin ‘Kannywood Abba Care’ ya buɗe ƙofar kula da lafiyar masu finafinan Hausa 

Yadda shirin ‘Kannywood Abba Care’ ya buɗe ƙofar kula da lafiyar masu finafinan Hausa 

Daga AISHA ASAS  A tsawon shekaru, ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da suka daɗe suna addabar masana'antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood shine yayata matsalar kula da lafiyar masu ruwa da tsaki a cikinta. Duk da irin gudunmawar da masana'antar ke bayarwa wajen nishaɗantarwa da bunƙasa al'adu, an sha ganin fitattun jarumai, mawaƙa da sauran masu sana'o'in da suke da alaƙa da sana’ar suna fuskantar matsalolin rashin lafiya ba tare da samun isasshen tallafi ba. Sai dai a wani sabon yanayi da ya jawo farin ciki a tsakanin zukatan masu harkar, an bayyana wani shiri da ake ganin zai kawo…
Read More
Kannywood a jiya da yau

Kannywood a jiya da yau

Daga ABDULYASSAR AMINU ABUBAKAR  A duk lokacin da aka ce an tashi ba da wani misali ko kuma kwatance a kan Kannywood, to fa babu wata masana’anta da ake hada kwatancen na su illa Bollywood ko Tollywood. Abin zai iya yin ciwo a ranka ace kana kallon kai kana ta ƙoƙari domin girmamar da kanka amma wasu gungu na yi maka kallon ba ka ma da niyya, ko ba ka ma fara ba. In dai mutum na bibiyar al’amuran fina-finan Indiya musamman ma na kudanci, watau Tollywood, lalle ne zai riƙa ganin irin fashin bakin da Aliyu Wazzyyr ke yi.…
Read More
Daminar 2026: Jihohi 33 da Abuja na fuskantar barazanar ambaliya

Daminar 2026: Jihohi 33 da Abuja na fuskantar barazanar ambaliya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Yayin da damina ke ƙara ƙarfi a sassa daban-daban na Nijeriya, fargaba na ƙaruwa kan yiwuwar ambaliyar ruwa, toshewar magudanan ruwa, raba jama’a da muhallansu da kuma ɓarkewar cututtuka a jihohi da dama. Duk da gargaɗin da hukumomi ke yi tun da wuri, masana na nuna damuwa kan ko ƙasar ta ɗauki matakan da suka dace domin kauce wa maimaita bala’o’in da aka sha fama da su a shekarun baya. A farkon wannan shekara, Gwamnatin Tarayya ta fitar da Rahoton Hasashen Ambaliyar Ruwa na Shekarar 2026, wanda Hukumar Kula da Harkokin Ruwa ta ƙasa (NiHSA) ta…
Read More
Majalisar Wakilai ta tilasta CBN maida biliyan N522 na harajin VAT

Majalisar Wakilai ta tilasta CBN maida biliyan N522 na harajin VAT

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kwamitin Kula da Asusun Gwamnati na Majalisar Wakilai ya bayyana cewa ya samu nasarar ƙwato kusan Naira biliyan 522 na Harajin ƙarin Kima, wato VAT, da ba a miƙa wa Gwamnatin Tarayya ba daga hannun Babban Bankin Nijeriya (CBN). Kwamitin ya ce wannan nasara ta samo asali ne daga binciken da yake ci gaba da gudanarwa kan zubewar kuɗaɗen shiga da kuma kuɗaɗen da ya kamata a biya Gwamnatin Tarayya amma ba a biya ba. A cewar kwamitin, wannan kuɗi da aka kwato na daga cikin sakamakon wani cikakken bincike da aka ƙaddamar bayan Majalisar Wakilai…
Read More
Kamfanonin lantarki sun yi fatali da tsarin gwamnati bayan bashinsu ya haura tiriliyan N7

Kamfanonin lantarki sun yi fatali da tsarin gwamnati bayan bashinsu ya haura tiriliyan N7

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Fannin samar da wutar lantarki a Nijeriya na fuskantar sabon ƙalubale bayan da bashin da kamfanonin samar da wuta (GenCos) ke bi ya haura zuwa Naira tiriliyan bakwai, yayin da kamfanonin suka yi watsi da tsarin da Gwamnatin Tarayya ta gabatar na sasanta bashin. Babbar Sakatariya kuma Babbar Daraktar ƙungiyar Kamfanonin Samar da Wutar Lantarki ta Nijeriya (APGC), Dakta Joy Ogaji, ce ta bayyana hakan a ranar Litinin yayin ƙaddamar da taron horas da shugabannin fannin wutar lantarki na Nijeriya na shekarar 2026. A cewarta, nauyin bashin da kamfanonin samar da wutar lantarki ke bi na…
Read More