ukarofi

12571 Posts
Da ɗumi-ɗumi: Kotun ƙoli ta ɗage shari’ar masarautar Kano

Da ɗumi-ɗumi: Kotun ƙoli ta ɗage shari’ar masarautar Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Babbar kotun ƙolin Najeriya ta saka ranar 19 ga watan Aprilun 2027 domin ci gaba da shari’ar masarautar Kano. Kotun ta sanya ranar ne domin saurare tare da karɓar martanin waɗanda aka yi ƙara a shari'ar wadda Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya shigar gabanta. Kazalika, mai ƙarar yana ƙalubalantar hana shi damar da doka ta ba shi a matsayinsa na babban ɗan majalisar sarki wanda majalisar dokokin Kano ta yi ta hanyar sauya dokar masarautu. Wannan shari'ar dai ta nuna cewa sai bayan shekara guda za'a cigaba da shari'ar.
Read More

Makarantu ba za su tafi hutun ƙarshen zango na biyu ba a Katsina – Sani Ɗanjuma

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Katsina ta tabbatar da cewa ba za a rufe makarantun firamare da na sakandire ba bayan kammala jarabawar zangon karatu na biyu (Second Term) da ɗalibai ke yi a halin yanzu. Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar, Malam Sani Ɗanjuma Suleiman, ya sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai. Sanarwar ta yi kira ga iyaye da masu ruwa da tsaki a fannin ilimi da su lura cewa, ɗalibai masu jeka-ka-dawo da kuma na makarantun kwana ba za su tafi hutun ƙarshen zangon…
Read More
Ba lallai ka haifi ’ya’ya masu sikila idan ka auri mai cutar – Khadija Baba

Ba lallai ka haifi ’ya’ya masu sikila idan ka auri mai cutar – Khadija Baba

“Me ya sa mutane ba sa taya mu yarda da ƙaddara kan cutar da muke tare da ita” Daga AISHA ASAS  Cutar amosanin jini, wato sikila cuta ce da ke da matuƙar wuyar sha'ani, wani lokacin akan yi wa masu ita kallon masu ƙarancin rayuwa kasantuwar ba sosai ne suke wuce lokutan ƙurciya ba. Cutar sikila cuta ce ta gado, ma'ana akan same ta ne ta sanadiyyar kalar jinin da iyaye suke da shi. Wannan na nufin takan samu ne idan iyayen biyu suna ɗauke da sinadarin cutar kamar AS ya haɗu da AS, ko kuma wani ɓangare AS da…
Read More
Yadda ƙabilar Toraja ke rayuwa da mamaci a Indonesiya

Yadda ƙabilar Toraja ke rayuwa da mamaci a Indonesiya

A wannan mako, jaridar Blueprint Manhaja ta kewaya duniya inda ta yada zango a ƙasar Indonesiya da ke yankin Asiya. A yau shafin na mu na ‘Al'ajabi’ ya yi tattaki na musamman zuwa yankin Gabas-ta-tsakiya, inda za mu yi nazari a kan al’adar ƙabilar Toraja. Wani abu mafi ɗaukar hankali ta yadda har idon duniya ya ɗarsu a kan waɗannan al’umma shi ne yadda su ke tafiyar da sha’anin gawa ko kuma mu ce mamaci. Su dai waɗannan mutane suna rayuwa ne a cikin duwatsun da ke Kudancin Sulawesi ta ƙasar Indonesiya, Kalmar ‘Toraja’ ta samo asali daga yaren ‘Buginese’…
Read More
Amurka da Iran na shirin komawa teburin tattaunawa duk da killace tashoshin jiragen ruwa

Amurka da Iran na shirin komawa teburin tattaunawa duk da killace tashoshin jiragen ruwa

Rahotanni sun nuna cewa tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin Iran na iya sake farawa a ƙasar Pakistan cikin kwanaki biyu masu zuwa, kamar yadda Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana, bayan da zaman sulhun ƙarshen mako ya rushe, abin da ya sa Amurka ta ɗauki matakin killace tashoshin jiragen ruwan Iran. Jami’an diflomasiyya daga Pakistan, Iran da ƙasashen yankin Gulf sun tabbatar da cewa akwai yiwuwar tawagogin Amurka da Iran za su koma Pakistan nan da ƙarshen wannan mako domin ci gaba da tattaunawa, duk da cewa wani babban jami’in Iran ya ce har yanzu ba a tsaida takamaiman ranar ba.…
Read More
Rikicin siyasa tsakanin Amurka da Italiya na ƙara tsananta

Rikicin siyasa tsakanin Amurka da Italiya na ƙara tsananta

*Trump ya soki Meloni, ya ce ya yi mamaki da halinta *Firaministar ta ce ta dawo daga rakiyar Trump kan yaƙi da Iran  Shugaban Amurka Donald Trump ya caccaki Firaministar Italiya Giorgia Meloni, yana mai cewa ta nuna rashin jaruntaka kuma ta ba Amurka kunya, a wani mataki da ya girgiza dangantakar siyasa tsakanin ƙasashen biyu. Meloni, wadda a baya ta kasance mai goyon bayan Trump, ta fara nesanta kanta da shi bayan yaƙin Iran, sannan ta soki kalaman da Trump ya yi kan Paparoma Leo, tana kiran su marasa dacewa. Trump ya mayar da martani cikin hira da jaridar…
Read More
Congo za ta karɓi baƙin haure da Amurka ta kora a wannan mako

Congo za ta karɓi baƙin haure da Amurka ta kora a wannan mako

Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo na shirin karɓar fiye da mutane 30 da Amurka ta kora daga ƙasarta a wannan mako, a wani sabon salo da Washington ke amfani da shi na haɗin gwiwa da ƙasashen Afirka wajen sarrafa batun baƙin haure. Majiyoyi sun ce waɗanda za a kawo ba ’yan Congo ba ne, kuma wasu daga cikinsu sun fito ne daga Amurka ta Tsakiya da Kudanci. Ana sa ran adadin zai kai tsakanin mutane 37 zuwa 45. Za a sauke su a Kinshasa kafin a kai su wani otel kusa da filin jirgin sama, inda za su zauna na tsawon kwanaki…
Read More
Togo na shirin gabatar da taswirar duniya da ke nuna ainihin girman Afirka

Togo na shirin gabatar da taswirar duniya da ke nuna ainihin girman Afirka

*Kasashen Afirka na neman gyara yadda duniya ke kallonsu Kasar Togo na shirin roƙon ƙasashen Majalisar ɗinkin Duniya su amince da sabuwar taswirar duniya da za ta nuna ainihin girman nahiyar Afirka, tare da watsi da tsohuwar taswirar Mercator. Masu sukar Mercator sun ce tana nuna Greenland kamar tana da girman Afirka, alhali Afirka ta fi ta ninki 14 girma. Kungiyar Tarayyar Afirka ta ɗora wa Togo alhakin jagorantar kamfen ɗin “Correct The Map” domin kawo ƙarshen amfani da wannan tsohuwar taswira. Kamfen ɗin na kira da a rungumi taswirar Eƙual Earth ta 2018, wadda ke ƙoƙarin nuna ainihin girman…
Read More
Tsohon tsarin haraji ne ya talauta Nijeriya – Tinubu

Tsohon tsarin haraji ne ya talauta Nijeriya – Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa tsoffin dokokin haraji da aka gada tun zamanin mulkin mallaka sun taka rawar gani wajen talauta ’yan Nijeriya, sakamakon rikice-rikice, yawaitar dokoki da rashin daidaito da suka dabaibaye tsarin tattara kuɗaɗen shiga. Shugaban ya yi wannan bayani ne a Abuja yayin ƙaddamar da sabon babban ginin hedikwatar Hukumar Haraji (NRS) mai hawa 16, inda ya jaddada cewa sabbin gyare-gyaren haraji da gwamnatinsa ta ɓullo da su za su samar da ci gaba mai ɗorewa da kuma tsarin tattalin arziki mai amfani ga kowa. A cewarsa, sabbin dokokin harajin…
Read More
Yadda satar kayan tashoshin sadarwa ke durƙusar da kamfanoni – Bincike

Yadda satar kayan tashoshin sadarwa ke durƙusar da kamfanoni – Bincike

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Fannin sadarwa na Nijeriya na fuskantar mummunar asara ta biliyoyin naira sakamakon ƙaruwa da satar muhimman kayayyakin aiki na tashoshin sadarwa, lamarin da ke barazana ga ɗorewar ingantaccen sadarwa a ƙasar. Bayanan da Hukumar Kula da Sadarwa ta ƙasa (NCC), ta fitar sun nuna cewa a shekarar 2025 kaɗai an sace sama da kayayyaki 650 da suka haɗa da janareto, batirori da sauran muhimman na’urorin samar da wuta da ake amfani da su don samar da sabis mai kyau a tashoshin sadarwa. Rahoton ya nuna cewa wannan matsala ta wuce matakin tangarɗar aiki kaɗai, inda ta…
Read More