ukarofi

12571 Posts
Shawarar Bankin Duniya kan shigo da mai na iya jefa Nijeriya cikin matsala — Masana

Shawarar Bankin Duniya kan shigo da mai na iya jefa Nijeriya cikin matsala — Masana

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wasu ƙwararrun masana a fannin man fetur sun bayyana damuwarsu kan sabuwar shawarar Bankin Duniya ga Nijeriya, inda suka gargaɗi cewa hakan na iya maida ƙasar baya zuwa dogaro da shigo da man fetur daga waje, abin da suka ce ya saɓa wa burin ci gaban tattalin arziki da kuma dokokin ƙasar. A cewarsu, shawarar da bankin ya bayar cikin rahotonsa na sabunta tattalin arzikin Nijeriya, wadda ke ƙarfafa ƙara shigo da mai da kuma cikakken ’yantar da kasuwar man fetur ta ƙasa (downstream), ba ta zo a lokacin da ya dace ba, kuma na iya…
Read More
Tallafin lantarki ya kai biliyan N418 yayin da fannin ya yi asarar biliyan N300 – Rahoto

Tallafin lantarki ya kai biliyan N418 yayin da fannin ya yi asarar biliyan N300 – Rahoto

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani rahoto ya nuna cewa ɓangaren wutar lantarki a Nijeriya na ci gaba da fuskantar manyan ƙalubale na kuɗi da aiki, inda Gwamnatin Tarayya ta kashe kusan Naira biliyan 418.79 a matsayin tallafi a ƙarshen shekarar 2025. Wannan bayani ya fito ne daga rahoton ƙarshen shekarar 2025 da Nigerian Electricity Regulatory Commission ta fitar, wanda ya yi cikakken bayani kan raguwar kuɗaɗen da ake tarawa, asarar da ake samu a rarraba wuta, matsalolin rashin daidaiton tashoshin lantarki, da kuma ɗan raguwar ƙarfin samar da wuta. Rahoton ya bayyana cewa kamfanonin samar da wutar lantarki sun fitar…
Read More
Masu zuba jari sun ci ribar biliyan N443 bayan tashin kasuwar a Nijeriya

Masu zuba jari sun ci ribar biliyan N443 bayan tashin kasuwar a Nijeriya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kasuwar hannayen jari ta Nijeriya ta fara makon nan da ƙarfi, inda masu zuba jari suka samu ribar kusan Naira biliyan 443 sakamakon sabon aaruwar saye da aka gani a kasuwar ranar Litinin, 13 ga Afrilu, 2026. Rahotanni sun nuna cewa wannan ci gaba ya samo asali ne daga ƙarin buƙata da aka nuna ga hannayen jari na wasu manyan kamfanoni kamar NGX Group, Trans-Nationwide Express, MC Nichols, VFD Group, CHAMS da wasu da dama. Jimillar darajar kasuwar ta tashi daga naira tiriliyan 131.165 zuwa naira tiriliyan 131.608, wanda ke nuna ƙarin kashi 0.34 cikin ɗari,…
Read More
Kotu a Italiya ta amince da ƙarar gamayya kan Meta na zargin satar bayanai na Facebook

Kotu a Italiya ta amince da ƙarar gamayya kan Meta na zargin satar bayanai na Facebook

Daga AISHA ASAS  *Masu amfani da Facebook sama da miliyan 533 ‘yan Italiya na iya shiga ƙarar neman diyya *Meta ta ce hukuncin bai nuna ta taka doka ba, ta kuma yi hasashen za a watsar da ƙarar Wata kotu a birnin Milan na ƙasar Italiya ta amince da ci gaba da wata ƙarar gamayya (class action) da wata ƙungiyar kare haƙƙin masu amfani da kafafe ta shigar kan kamfanin Meta Platforms, dangane da zargin satar bayanan sirri da ta shafi masu amfani da Facebook. A cewar umurnin kotun da aka bayar a ranar Talata, wannan matsala ta satar bayanai…
Read More
Yadda fasahar AI ke sauya masana’antar fina-finai a Indiya cikin sauri

Yadda fasahar AI ke sauya masana’antar fina-finai a Indiya cikin sauri

Daga AISHA ASAS  *Masana’antu na rage kuɗi da lokacin shirya fim, amma ana tafka muhawara kan ingancinsa *Indiya na gaba a amfani da AI, yayin da Hollywood ke fuskantar takunkumi daga ƙungiyoyin ma’aikata Masana’antar fina-finai ta Indiya ta shiga wani sabon zamani mai cike da sauyi, inda fasahar Artificial Intelligence (AI) ke sauya yadda ake shirya fina-finai, rage kuɗin samarwa, da kuma ƙara yawan harsunan da ake fassara fina-finai zuwa gare su. A yau, a wasu ɗakunan shirya fim a Indiya, hayaniyar kyamarori da umurnin daraktoci ta ragu, yayin da aka maye gurbinta da ƙarar na’urorin kwamfuta da masu rubuta…
Read More
Tsare-tsaren Tinubu sun jefa kaso 63 na ‘yan Nijeriya cikin matsanancin talauci – Atiku

Tsare-tsaren Tinubu sun jefa kaso 63 na ‘yan Nijeriya cikin matsanancin talauci – Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya soki tsare-tsaren tattalin arziƙin shugaba Tinubu tare da kafa hujja da rahoton bankin duniya wanda ya ce talauci na ci gaba da tsananta a Nijeriya. A cikin jawabin da ya fitar a ranar Juma’a a Abuja, mai taimaka wa Atiku kan yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya ce, bankin duniyar ya nuna irin “mahuyacin halin” da miliyoyin ‘yan Nijeriya ke fama da ita. Ya abato bankin na cewa sama da kaso 60% na ‘yan Nijeriya na rayuwa ƙasa da ma’aunin talauci idan aka kwatanta da kaso 40% da…
Read More
Zan iya ficewa daga ADC idan aka yi maguɗi a zaɓen fidda gwani – Peter Obi

Zan iya ficewa daga ADC idan aka yi maguɗi a zaɓen fidda gwani – Peter Obi

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  ɗan takarar Shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Peter Obi, ya bayyana cewa zai iya ficewa daga jam’iyyar idan aka samu matsala ko magudi a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa gabanin zaɓen 2027.  Jam’iyyar dai ta gudanar da babban taronta na ƙasa a Abuja a ranar Talata. Obi, wanda shi ne dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, ya bayyana haka ne a daren Litinin yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Arise News Prime Time. Mai gabatar da shirin, Charles Aniagolu, ya tambaye shi…
Read More
Wakilan ofishin jakadancin Birtaniya da China sun halarci taron ADC

Wakilan ofishin jakadancin Birtaniya da China sun halarci taron ADC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Wakilan ofishin jakadancin Birtaniya a Nijeriya sun halarci babban taron jam’iyyar ADC da ɓangaren da David Mark ke jagoranta ya shirya a ranar Talata. Haka kuma, jakadan ƙasar Sin a Nijeriya, Yu Dunhai, ya halarci taron da aka gudanar a Rainbow Event Centre da ke Abuja. Sakataren jam’iyyar na ƙasa na ɓangaren, Rauf Aregbesola, ne ya tabbatar da halartar wakilan ƙasashen biyu. Ofishin jakadancin Birtaniya ya samu wakilci ne daga tawaga mai mutum uku ƙarƙashin jagorancin sakataren siyasa, Thomas Samson, yayin da wata ma’aikaciyar ofishin, Damilola Oyedele, ta kasance cikin tawagar. Bayan fara taron,…
Read More
Shirin ‘Renewed Hope’ na Tinubu ga ‘yan Nijeriya yaudara ce – Aregbesola

Shirin ‘Renewed Hope’ na Tinubu ga ‘yan Nijeriya yaudara ce – Aregbesola

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Sakataren Jam’iyyar ADC na ƙasa, Rauf Aregbesola, ya ce, shirin shugaba Tinubu na sabunta fata ba zai kawo wa ‘yan Nijeriya wani ci gaba ba. Aregbesola, tsohon gwamnan Osun ya yi wannan kalamai ne a yayin da yake magana a lokacin gangamin taron jam’iyyar na ƙasa wanda tsagin shugabancin da David Mark yake jagoranta a Abuja. Ya kuma buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi tsakatsantsan, yana mai cewa gwamnatin ta gaza wajen cika alƙawuran yaƙin neman zaɓen da ya yi ba. “Shirin sabunta fata yaudara ce. Yaushe za a cimma shirin sabunta fatan?” ya…
Read More
Nijeriya ta zama tamkar ƙasar da ake yaƙi saboda matsalar tsaro — ACF

Nijeriya ta zama tamkar ƙasar da ake yaƙi saboda matsalar tsaro — ACF

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta ce matsalar rashin tsaro a Nijeriya ta kai matakin da ƙasar ta zama tamkar ana yaƙi. Ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ɗauki tsaro a matsayin matsala mafi muhimmanci cikin gaggawa. An bayyana hakan ne bayan taron shugabannin ACF ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Bashir Dalhatu. Sun ce rikice-rikicen da ke faruwa a ƙasar, musamman a Arewa, sun wuce ƙananan hare-hare, sun koma manyan matsaloli masu barazana. ƙungiyar ta yi nuni da hare-haren baya-bayan nan a jihohin Borno, Kaduna, Katsina da Binuwai, inda aka kashe mutane da dama tare da raba wasu da…
Read More