19
Apr
Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), ta ce matsalar rashin tsaro a Nijeriya ta kai matakin da ƙasar ta zama tamkar ana yaƙi. Ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ɗauki tsaro a matsayin matsala mafi muhimmanci cikin gaggawa. An bayyana hakan ne bayan taron shugabannin ACF ƙarƙashin jagorancin shugabanta, Bashir Dalhatu. Sun ce rikice-rikicen da ke faruwa a ƙasar, musamman a Arewa, sun wuce ƙananan hare-hare, sun koma manyan matsaloli masu barazana. ƙungiyar ta yi nuni da hare-haren baya-bayan nan a jihohin Borno, Kaduna, Katsina da Binuwai, inda aka kashe mutane da dama tare da raba wasu da…
