ukarofi

12571 Posts
Duniya za ta iya tashi a kowane lokaci 

Duniya za ta iya tashi a kowane lokaci 

Daga ALI ABUBAKAR SADIK Jiya wani kanina ya yi posting cewa "Nan da shekaru biliyan 5 Duniya za ta tashi in ji masana". To, a gaskiyar lamari ba haka abin ya ke ba. Abinda masana Ilimin sararin samaniya ke hasashe shine cewa Rana, wadda ita ce ginshikin wanzuwar Duniya, a yanzu ta kai rabin shekarunta. Wato an haifi wannan Rana tamu kimanin shekaru biliyan 5 da su ka wuce, kuma za ta iya sake kai wasu shekaru biliyan 5 din kafin ta mutu. Masana sun gane haka ne sakamakon nazarin ragowar makamashin nukiliya da ke ci a Rana, wato tamkar…
Read More
Abba Bichi ne wanda ya fi kowa cancantar zama Mataimakin Gwamnan Jihar Kano

Abba Bichi ne wanda ya fi kowa cancantar zama Mataimakin Gwamnan Jihar Kano

Daga UNCLE LARABI Ko kai ɗan wane jam'iyya ne, duk a dawarka, idan dai a Kano ka ke, ka san Abba Bichi ya fi kowanne ɗan majalisar tarayya dake Jihar Kano yin aiki a ƙaramar hukumarsa. Yana kuma samarwa da matasa aiki sosai. Ga shi da halin girma da dattako. Ban san Abba Bichi a zahiri ba. Ba ni da alaƙa da shi, amma Ina ganin hotonsa da ayyukansa, Ina kuma jin labarin ayyukansa daga mutanen da suke Bichi da sauran mutane ma na Jihar Kano. Daga ganin hotonsa ka san mutum ne mai kamala da muhibba. Mawuyacin abu ne ka…
Read More
Zaɓen Shugaba Tinubu: Malamai ban da igiyar zato – Aliyu Salihu Aliyu

Zaɓen Shugaba Tinubu: Malamai ban da igiyar zato – Aliyu Salihu Aliyu

Daga HAMISU IBRAHIM a Kano A tattaunawar da Wakilin Blueprint Manhaja, IBRAHIM HAMISU, ya yi da wani ɗan kasuwa mazaunin Tudun Maliki a Kano mai suna na Aliyu Salihu Aliyu, ya bayyana rashin jin daɗinsa game da yadda malamai ke hawa mumbari suna sukar Shugaba Bola Ahmad Tinubu, al’amarin da ya danganta da ƙabilanci da ɓangaranci. A cikin hirar dai ya yi nuni da cewa, wannan ba zai haifar wa Nijeriya ɗa mai ido ba. Don haka ya gargaɗe su kan lallai kada su ɗora mutane a azargagiyar igiyar zato tamkar yadda suka kwata a baya. Ga yadda hirar ta kasance:…
Read More
Ba a abokin hamayya na dindindin a siyasa

Ba a abokin hamayya na dindindin a siyasa

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA Tun sauya sheƙar Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara daga PDP zuwa APC na zuba ido ko zan ga wani ɗan zilla ya yi fatar alheri cewa Allah ya sa manyan Zamfara su haɗa kai don salamar jihar, sai shiru tsit ka ke ji. Ba ma kawai rashin addu’ar alheri ba, yanzu idan ‘yan zilla za su lissafa manyan ‘yan siyasar da su ka yi wa rejista a farafagandarsu, ba sa ambatar sunan gwamna Dauda! Shin hakan ya damu gwamnan kuwa? Ba na tsammani don ko a suɓutar baki ba mu taɓa jin ya ambaci sunan…
Read More
Yadda ’yan siyasa ke jefa matasa bangar soshiyal midiya!

Yadda ’yan siyasa ke jefa matasa bangar soshiyal midiya!

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ana ci gaba da samun sauye-sauye a harkokin siyasa a ƙasar nan, yayin da ake ƙara kusantar Babban Zaɓe na shekarar 2027. 'Yan siyasa, musamman sabbin yanka masu neman a san da su da gwamnoni masu neman tazarce suna ta ƙoƙarin sauyin sheƙa daga wannan jam’iyya zuwa waccan. Mun ga yadda jihohi irin su Kano, Filato, Adamawa, Taraba da Zamfara gwamnoninsu suka yi sauyin jam'iyya zuwa babbar jam’iyya mai mulki ta APC. Matakin da wasu ke kallo a matsayin wayon a ci ne, wato kowa ƙoƙari yake yi a dama da shi a siyasar tarayya, a…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta sayar da takin zamani a rabin farashin da ta saya

Gwamnatin Katsina za ta sayar da takin zamani a rabin farashin da ta saya

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa ya sanar da haka a lokacin da yake ƙaddamar da sayan takin zamani buhu 400,000 ga manoma a garin Malumfashi. Gwamna Raɗɗa ya sanar da cewa gwamnatin jihar za ta sayar da takin ne a farashi mai rahusa na Naira 25,000 ga kowane buhu. Wannan farashi, wanda shine kwatankwacin rabin farashin da ake sayar da takin a kasuwannin, wanda hakan ke nuna cewa gwamnati ta ɗauki nauyin biyan kashi 50 cikin 100 na kuɗin domin sauƙaƙa wa manoma da ƙarfafa samar da abinci. Gwamnan ya ƙara da cewa wannan shi ne karo…
Read More
Kwamitin daidaita iyakokin masarautun Katsina sun kai ziyarar ban girma ga Sarkin Daura

Kwamitin daidaita iyakokin masarautun Katsina sun kai ziyarar ban girma ga Sarkin Daura

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Kwamitin daidaita iyakokin masarautun hakimai a jihar Katsina ƙarƙashin mai ba gwamna shawara kan ayyukan ƙananan hukumomi Alhaji Ahmed Rufa'i Safana. Alhaji Umar Faruk Umar ya bayyana wa 'yan kwamitin cewa, masarautar Daura na matuƙar yabawa da ƙoƙarin Gwamna Raɗɗa wajen warware dukkan wasu matsalolin al'umma da kan taso inda ya jaddada cewa masarautar Daura a shirye take ta aiwatar da dukkan shirye-shiryen gwamnatin jihar katsina na raya ƙasa. Sarkin ya bayyana cewa masarautar Daura tsaye take wajen tabbatar da haɗin kai da gudanar da harkokin sarauta cikin tsari, ladabi da biyayya. Alhaji Umar Faruq…
Read More
Babban hafsan tsaro ya ba da umarnin ƙara yawan hare-hare kan ‘yan bindiga

Babban hafsan tsaro ya ba da umarnin ƙara yawan hare-hare kan ‘yan bindiga

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Babban hafsan tsaro, Janar Olufemi Oluyede, ya umarci sojoji a ƙarƙashin Operation Fansan Yamma da su ƙara yawan hare-haren da ake kai wa 'yan bindiga a Arewa maso Yamma, yana mai cewa dole ne a tabbatar da tsaron Najeriya ko ta halin ƙaƙa. CDS ya ba da umarnin ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki a Jihar Zamfara yau Litinin. A cewar sa ziyarar ta kasance don tantance shirye-shiryen yaƙin da sojoji suke yi da 'yan ta'adda, sauraron ƙalubalensu, da kuma basu ƙwarin gwiwa yayin da suke ƙara ƙaimin yaƙi da 'yan bindiga da…
Read More
‘Yan bindiga sun sace mahaifin marubuciya Hadiza Auta

‘Yan bindiga sun sace mahaifin marubuciya Hadiza Auta

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba, sun yi garkuwa da Dagacin Sabon Garin Ƙauran Namoda a Jihar Zamfara,Alhaji Ibrahim Dan-Auta, wanda mahaifi ne ga wata fitacciyar marubuciyar littattafan Hausa, Hadiza Ibrahim D. Auta. Tun da sanyi safiyar jiya Lahadi 19 ga Afrilu, 2026 ne marubuciyar ta fitar da wani rubutu a shafukanta na zaurukan sada zumunta, inda take bayyana labarin sace mahaifin nata da ƴan bindiga su ka yi. Ta rubuta cewa, 'Inna Lillahi wa inna ilaihirraji'un! Ɓarayi sun tafi da babanmu.' Wannan sanarwa ta ɗaga hankalin marubutan Hausa da dama,…
Read More
Muttaƙa Rabe Darma ya kammala rangadin ƙananan hukumomi 11 da ke Katsina

Muttaƙa Rabe Darma ya kammala rangadin ƙananan hukumomi 11 da ke Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Ɗan takarar kujerar majalisar Dattijai a Katsina ta tsakiya injiniya Muttaƙa Rabe Darma ya kammala rangadin ƙananan hukumomi 11 da ke Katsina ta tsakiya. Injiniya Darma wanda ya fito takarar kujerar Sanata a jihar Katsina ƙarƙashin jamiyar APC ya kai ziyarar a ƙananan hukumomin ne domin neman goyon bayan shugaban jam'iyar a gabanin zaɓen fidda gwani. Ya nuna godiya matuƙa kan yadda ya samu kyakkyawar tarba a ƙananan hukumomin 11 na shiyyar Katsina da ya ziyarta domin tuntuba, a cewar sa Ɗan takarar, kuma tsohon shugaban asusun bunƙasa kimiyyar man fasahar man fetur ta ƙasa,…
Read More