ukarofi

12571 Posts
Matar aure ka ke nema ko ingantacciyar uwar ‘ya’yanka?

Matar aure ka ke nema ko ingantacciyar uwar ‘ya’yanka?

Tare da BILKISU YUSUF ALI, PhD Mata da yawa idonsu ya kan rufe kan cewa, duk namijin da ya zo wurinsu da sun fara soyayya sai su zata wanda ya zo wurin nasu aure ne ya kawo shi. Amma da tafiya ta yi tafiya sai su nemi saurayin su rasa. Wannan yana cikin babbar hujjar da ta sanya da yawan mata na kallon maza mayaudara, saboda ƙin auren su duk kuwa da soyayyar da suka sha, amma a ƙarshe sai ka ji sun ce “wai suna neman mace ta gari ne uwar ‘ya’yansu, ba matar aure ido rufe ba.” Amma…
Read More
Hukumar tace fina-finai a Kano ta rufe shagon maganin gargajiya kan tallan batsa

Hukumar tace fina-finai a Kano ta rufe shagon maganin gargajiya kan tallan batsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta ɗauki matakin gaggawa kan wani mai sayar da maganin gargajiya da ake zargi da amfani da wasu ƙananan yara a cikin wani talla mai ɗauke da kalaman da ba su dace ba. Hukumar ta bayar da umarnin rufe shagon mai sayar da maganin gargajiya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da ta samu. Kazalika, shugaban hukumar, Alh Abba El-Mustapha, ya gayyaci mai saida maganin wanda ake kira da Nagwale domin ya bayyana a gaban hukumar domin amsa zarge-zargen da ake yi masa. Da yake jawabi kan lamarin, daraktan da ke lura…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa shigar mata harkokin siyasa

Gwamna Raɗɗa ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa shigar mata harkokin siyasa

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa rawar da mata ke takawa da kuma haɗa su cikin harkokin siyasa da shugabanci a faɗin jihar. Taron, wanda ya gudana a ɗakin taro na gidan gwamnatin Katsina ya haɗa da manyan masu ruwa da tsaki na mata, shugabannin jam’iyyun siyasa da jami’an gwamnati da mata ƙarƙashin ƙungiyar Reserved Seats for Women Association wanda uwargidan Gwamnan jihar Hajiya zulaihatu Dikko Raɗɗa ta jagoranta. Tattaunawa a wajen taron yafi mayar da hankali ne kan faɗaɗa rawar mata a shugabanci, shiga siyasa da…
Read More
An maka mataimakin gwamnan Zamfara ƙara bisa zargin ɓata sunan tsohon ɗan majalisa

An maka mataimakin gwamnan Zamfara ƙara bisa zargin ɓata sunan tsohon ɗan majalisa

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Tsohon ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Maru a Majalisar Dokokin Jihar Zamfara, Hon. Yusuf Alasan Kanoma, ya shigar da ƙarar mataimaki na musamman kan harkokin watsa labarai da sadarwa ga Gwamnan Jihar Zamfara, Mustafa Jafaru Kaura a gaban Kotun Majistare ta ɗaya da ke Gusau, kan zargin barazana ga rayuwarsa da kuma ɓata masa suna. Yayin da yake jawabi ga manema labarai a yau Talata a Kotun Majistare ta ɗaya, jim kaɗan bayan fara sauraron shari'ar da ke gaban kotu, lauyan mai ƙara, Barista Surajo Garba Gusau, ya bayyana kalaman da Mustafa Jafaru Kaura…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya bada umarnin gaggauta biyan hakimai sabon tsarin albashi

Gwamna Raɗɗa ya bada umarnin gaggauta biyan hakimai sabon tsarin albashi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Raɗɗa ya ƙaddamar da fara biyan sabon tsarin albashi na Hakimai da ke faɗin jihar tare da kira ga hukumar kula da ma'aikatan ƙananan hukumomin jihar da ta gaggauta basu takardar kama aiki da zai taimaka masu wajen fara biyan su albashin. Sabon tsarin albashi ya kai hakiman da magadan a matakin albashi na 16 wanda yayi daidai da muƙamin daraktan a gwamnati,sai kuma magadai da aka ɗaga su a matakin albashi zuwa GL 10. Gwamnan ya bayyana dokar masarautu ta 2025, wani muhimmin mataki da ke nuna ƙudirin gwamnatinsa na ƙarfafa cibiyoyin gargajiya,…
Read More
Harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu a Katsina

Harin ‘yan bindiga ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Mutane biyu suka mutu wasu biyar sun sami mummunan raunuka sakamakon hare haren 'yan bindiga a kan hanyar Guda zuwa Turare a karamar hukumar Bakori da ke jihar Katsina. Wata majiya mai tushe ta shaida cewa 'yan bindiga ɗauke da muggan makamai suka tare hanyar Guda zuwa Turare inda sukai ta kai hare hare akan matafiya da ƙauyukan da ke kan hanyar. Sai dai bayan samun kiran gaggawa haɗin gwiwa na jami'an tsaro da ke zirga-zirga a kan hanyar suka garzaya zuwa wajen,amma da isar su sun tarar da yan bindiga sun raunata mutane bakwai.…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya buƙaci masu hali su taimaka wajen cigaban al’umma

Gwamna Raɗɗa ya buƙaci masu hali su taimaka wajen cigaban al’umma

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya buƙaci masu hannu da shuni a jihar da su riƙa ware wani ɓangare na dukiyar su domin ayyukan jin ƙai da ci gaban al’umma, a matsayin taimako ga ƙoƙarin gwamnati. Gwamnan ya yi wannan kira ne yayin ya ke ƙaddamar da wasu ayyuka da wani mai taimakon jama’a, Injiniya Muntari Sagir, ya aiwatar a ƙaramar hukumar Malumfashi. Gwamna Raɗɗa ya bayyana ayyukan da Injiniya Muntari Sagir ya aiwatar da suka haɗa da cibiyar kula da lafiya a Al-Makiyayi, ginin ajujuwa uku tare da ofis a kwalejin ungozoma…
Read More
Duniyar ce ta sauya ko mutanen cikinta?

Duniyar ce ta sauya ko mutanen cikinta?

Assalamu alaikum. Tarbiyyar yara a wannan lokacin ta wuce ace iyaye ne kawai za su kula da ita, zamani ya zo na sauyin rayuwa, yara da manya kowa ya san kuɗi kuma ya san inda ake kashe su, saɓanin shekarun baya da muka samu labarin cewa wani sai ya haura shekaru goma sha biyar ba ya kashe kuɗi da kansa sai dai in aikensa aka yi sayen wani abu. A zamanin iyaye da kakanni ana rayuwa ne ba tare da dogon buri ko hangen wani ya fini ba, mutum mai wadata yana iya riƙe yaran maƙotansa da sauran yaran ’yan…
Read More
Addini daban siyasa daban

Addini daban siyasa daban

Assalamu alaikum, da fatan mun yi sallah lafiya? Allah ya maimaita mana, Amin. Akwai wani abinda ke faruwa a ƙasar nan, mutane suna gwama lamarin siyasa da addini. Suna kamfen da sunan da sunan addini, wuce wani musulmi, wane ba Musulmi ba. Wasu har ɗaukar siyasa suke a matsayin jihadi. Da masu addini Kirista da Musulmai za su gane, da kuma ’yan ƙabilanci za su gane, da basu riƙa damuwa da wannan siyasa ba. Domin addini daban siyasa daban, musamman ma a ƙasar Nijeriya. Idan Addini ka ke so, ka koma gefe, domin babu ruwan Siyasa da Addini, idan kuma…
Read More
Neman alfarma ga masu kaɗa ƙuri’a da masu yin kamfen na zaɓen 2027

Neman alfarma ga masu kaɗa ƙuri’a da masu yin kamfen na zaɓen 2027

Daga UNCLE LARABI Don Allah a daure, duk wanda za a zaɓa a yi yarjejeniya da shi akan ba ma son ya yi mana komai tsahon shekaru huɗu na farkon mulkinsa sai waɗannan abubuwan guda uku kacal. Sune kamar haka; 1. Samar da tsaro a ƙasarmu Nijeriya. 2. Samar da wutar lantarki. 3. Samar da hanyoyin sufuri na ƙasa masu inganci (titina).  Idan ya amince zai samar da iyakar waɗannan abubuwan ukun kacal, mu amince mu ba shi ƙuri'unmu bisa amana. Kada mu ruɗu da yawan ƙarya da alƙawuran da duk wani ɗan takara zai yi mana na cewar zai yi…
Read More