ukarofi

12570 Posts
Dambe wasan maza, kowwayyi hankali ya barka: Waiwaye kan tarihin kiɗan dambe na Dan’anace (1)

Dambe wasan maza, kowwayyi hankali ya barka: Waiwaye kan tarihin kiɗan dambe na Dan’anace (1)

"Waƙa adabi ce, shi kuma adabi al’ada ne" Daga IBRAHIM MUHAMMAD  (Danmadamin Birnin Magaji) 0.0 Shimfiɗa Hausawa musamman mazauna karkara (ƙauyuka) suna wanzar da al’adu da yawa masu sha’awa da adana tarihin wannan al’umma. Waɗannan al’adun su ne taskokin da suka adana tarihinmu. Kuma waɗannan al’adu su ne suka samar da adabimmu. Wajen wanzar da al’adun aure ake samar da waƙoƙin aure. Wajen wanzar da wasanni ake gwada yin salailan maganganun hikima da gwada zalaƙar harshe. A nan salon magana da adon magana da karin magana ke tasowa. A nazarin tarihi da rayuwar wannan bawan Allah an ci karo da…
Read More
Yusuf Buhari ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar majalisar wakilai

Yusuf Buhari ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar majalisar wakilai

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Yusuf Muhammadu Buhari, ɗan tsojon shugaban ƙasar Nijeriya, Marigayi Muhammadu Buhari, ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takarar kujerar Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Daura/Sandamu/Mai’adua a Jihar Katsina ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC). Yusuf Buhari ya bayyana hakan ne a yayin wata ziyarar girmamawa da ya kai wa Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, a gidan gwamnati da ke Katsina. Ziyarar ta samu rakiyar manyan shugabannin siyasa, sarakunan gargajiya, wakilan al’umma, ’yan uwa da sauran masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na mazaɓar. Jagoran tawagar, Hon. Musa Haro, Hakimin Dumurkul, ya bayyana ɗan…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta tallafa wa ƙananan ‘yan kasuwa 62,000

Gwamnatin Katsina za ta tallafa wa ƙananan ‘yan kasuwa 62,000

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A zaman ta karo na bakwai majalisar zartarwa ƙarƙashin gwamna Dikko Raɗɗa ta amince ta aiwatar da shirin tallafawa ƙananan da matsakaitan kasuwanni (Nano, Micro da Small Enterprises) a manyan hanyoyin jihar, wanda zai tallafa wa ‘yan kasuwa 62,000 a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar. Wannan shiri na da nufin ba su jarin kasuwa domin bunƙasa kasuwancinsu da inganta rayuwarsu da tattalin arziki a matakin ƙasa. Haka kuma majalisar ta amince da aikin ginawa da shimfida kwalta a hanyar Rahamawa zuwa Gidan Shehi sai Namadi zuwa Inwala Jan Gefe ta miƙe zuwa Ring Road…
Read More
Babu alamar yaɗuwar korona – NCDC

Babu alamar yaɗuwar korona – NCDC

Daga USMAN KAROFI Hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta kwantar da hankalin jama’a bayan tabbatar da samun sabon mutum da ya kamu da cutar korona a jihar Kuros Ribas, inda ta ce babu wata alamar yaɗuwar cutar a yanzu. A wata sanarwa da Darakta Janar na hukumar, Jide Idris, ya fitar, ya bayyana cewa ana sa ido kan dukkan mutanen da suka yi hulɗa da wanda ya kamu da cutar, kuma komai na tafiya yadda ya kamata. Gwamnatin jihar Kuros Ribas ta tabbatar da ɓullar cutar ne a ranar Talata, bayan shekaru da hukumar…
Read More
Jam’iyyar APC a Zamfara ta faɗa mummunan rikicin cikin gida

Jam’iyyar APC a Zamfara ta faɗa mummunan rikicin cikin gida

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam'iyyar APC a Jihar Zamfara ta faɗa mummunan rikicin cikin gida biyo komawar Gwamna Dauda Lawal Jam'iyyar, yayin da ƙaramin ministan tsaro Bello Muhammad Matawalle ya koka kan abunda ya kira yin watsi da shi a siyasance. Matawalle yayi wannan tsokaci a wata hirar wayar tarho da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta. Matawalle ya koka bisa yanda Gwamna Dauda Lawal yaƙi tuntuɓar sa tun bayan komawar sa APC dangane da makomar jam'iyyar da rabon muƙamai a jam'iyyar kafin a gudanar da taron APC a Jihar. Idan za a iya tunawa, jam'iyyar ta ƙasa ta…
Read More
Gwamna Raɗɗa ya duba aikin gina makaranta ta musamman a Jiƙamshi

Gwamna Raɗɗa ya duba aikin gina makaranta ta musamman a Jiƙamshi

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ya kai ziyarar duba aikin gina makaranta ta musamman (Special School) a garin Jiƙamshi, ƙaramar hukumar Musawa. Makarantar na daga cikin guda uku da gwamnati ke ginawa a kowace shiyya ta jihar, domin bai wa ɗalibai masu basira (gifted) marasa galihu damar samun ingantaccen ilimi da zai bunƙasa hazaƙarsu. Sauran makarantun akwai ta garin Raɗɗa a shiyyar Katsina wacce ake daf da ƙaddamar wa, da kuma ta Dumurƙul a shiyyar Daura, wacce ita ma tuni aikin yayi nisa.
Read More
Waye Ibrahim Taiwo?

Waye Ibrahim Taiwo?

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An haifi Ibrahim Taiwo a shekarar 1940, a ƙaramar hukumar Wushishi ta Jihar Neja da ke tarayyar Nijeriya. (Bincikenmu bai samo rana wata da kuma kwanan watan da aka haife shi ba). Ya taso a garin Kagara, har ma a lokacin da ya ke makaranta a kan kirashi da suna Ibrahim Kagara. Ya yi Firamare ɗinsa a Senior Primary School Minna, sai kuma Bida Middle School. Ya halarci Proɓincial Secondary School da ke Okene na ɗan wani taƙaitaccen lokaci, inda ya samu shaidar kammala karatun sakandare. Aikin Soja: Ya fara shiga aikin damara ne a shekarar…
Read More
Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa 

Dandalin shawara: Mijina ba ya son haihuwa 

(Ci gaba daga makon jiya) Daga AISHA ASAS  TAMBAYA: Salam. Ina wuni Asas. Allah Ya taimake ki ga dukan lamuranki. Ki taimake ni, yadda Allah ya taimake ki. Mijina da muka yi aure da shi shekara takwas. Da aka kawo ni gidanshi, kullum sai ya ba ni magani zai kusance ni, bai taɓa fashi ba, sai da na yi shakara biyu da aure, har shan maganin ya ishe ni, amma ko na yi ƙorafi sai ya rarashe ni, idan na ƙiya sai ya ƙi kusanta ta ko da kuwa ya matsu da son yi. To da iyaye suka fara zancen…
Read More
Motsa jiki ma kwalliya ne

Motsa jiki ma kwalliya ne

Daga AISHA ASAS Motsa jiki wata ɗabi’a ce da har yau ba ta gama zama ‘yar gida a ƙasar Hausa ba. Har a wannan lokacin akwai waɗanda ke kallon sa a layin ɗaya daga cikin gutsiri-tsoma da bature ke rajin karewa tare da ba shi muhimmanci, wanda a wurin su duk rashin aikin yi ne. Da yawa ba su amince cewa, atisaye na taka muhimmiyar rawa a layifar gangar jikinsu ba. Wannan ne ya sa jaridar Manhaja ta zaƙulu wannan darasin don ya zama wayar da kai ga waɗanda suka jahilce shi, ya kuma ƙara wa masu yi karsashi, sannan…
Read More
Matar aure ka ke nema ko ingantacciyar uwar ‘ya’yanka?

Matar aure ka ke nema ko ingantacciyar uwar ‘ya’yanka?

Tare da BILKISU YUSUF ALI, PhD Mata da yawa idonsu ya kan rufe kan cewa, duk namijin da ya zo wurinsu da sun fara soyayya sai su zata wanda ya zo wurin nasu aure ne ya kawo shi. Amma da tafiya ta yi tafiya sai su nemi saurayin su rasa. Wannan yana cikin babbar hujjar da ta sanya da yawan mata na kallon maza mayaudara, saboda ƙin auren su duk kuwa da soyayyar da suka sha, amma a ƙarshe sai ka ji sun ce “wai suna neman mace ta gari ne uwar ‘ya’yansu, ba matar aure ido rufe ba.” Amma…
Read More