ukarofi

12618 Posts
Ranar Mata ta Duniya 2026: Ana cin zarafin kaso 70 na ɗalibai mata a jami’o’in Najeriya — Dr. Comfort Adokwe

Ranar Mata ta Duniya 2026: Ana cin zarafin kaso 70 na ɗalibai mata a jami’o’in Najeriya — Dr. Comfort Adokwe

Daga JOHN D WADA a Keffi Muƙaddashin daraktar cibiyar karatun jinsi (Ag. Director, Centre for Gender Studies) a babbar Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, Dr. Comfort Adokwe, ta sanar cewa kashi 70 na ɗalibai mata da kuma kashi 30 na ɗalibai maza suna fuskantar matsalar cin zarafi ta jinsinsu a manyan makarantun ƙasar nan. Ta bayyana haka ne a lokacin da take ganawa da manema labarai jim kaɗan kafin a fara bikin Ranar Mata ta Duniya na shekarar 2026, wanda cibiyar ta shirya a ranar Litinin na wannan mako a jami’ar da ke Keffi. Ta ce wani bincike na…
Read More
Zamfara: An gargaɗi matasan APC kada su ɗauki makami wajen tarben Kashim Shetima

Zamfara: An gargaɗi matasan APC kada su ɗauki makami wajen tarben Kashim Shetima

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau An yi Kira ga mambobin jam'iyyar APC musamman matasa da su guji ɗaukar duk wani irin makami a wajen tarbon mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shetima da zai zo jihar don karɓar Gwamna Dauda Lawal zuwa jam'iyyar ta APC a gobe Talata. Shugaban kwamitin yaɗa labarai na tarbon mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shatima, Hon. Lawal M. Liman yayi wannan kira a lokacin da kwamitin ke ganawa da manema labarai a Gidan Gwamnatin Jihar cikin daren nan. A cewar sa, an kammala duk shirye shiryen taron mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shatima, yana mai nuni da cewar baza…
Read More
Sallah Ƙarama: Tafarkin Gombe ya jinjina wa Gwamna Inuwa da Sarkin Gombe

Sallah Ƙarama: Tafarkin Gombe ya jinjina wa Gwamna Inuwa da Sarkin Gombe

Daga ABUBAKAR A. BOLARI, Gombe Tafarkin Gombe, Dakta Ibrahim Jalo Daudu, ya yaba matuƙa da yadda aka gudanar da bukukuwan sallar ƙarama cikin zaman lafiya da cikakken tsaro a faɗin Jihar Gombe. Ya ce bana sallah ta gudana cikin natsuwa da kwanciyar hankali, ba tare da samun wani rahoton tashin hankali ko barazanar tsaro ba, lamarin da ya bayyana a matsayin babban abin alfahari ga gwamnati da al’ummar jihar baki ɗaya. Dakta Jalo Daudu ya danganta wannan nasara da jajircewar Gwamnatin Jihar Gombe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da…
Read More
Shan miyagun ƙwayoyi na neman kassara matasan Nijeriya

Shan miyagun ƙwayoyi na neman kassara matasan Nijeriya

A wannan makon, wasiƙata za ta fita ne kai tsaye ga matasa akan batun annobar ta’ammuli da miyagun ƙwayoyi a tsakanin rukunan al’ummar Nijeriya, domin wata babbar barazana ce da tarnaƙi a ci gaban zamantakewa, tsaro da tattalin arziki. Matsala ce mai wuyar magani wadda a keɓance ɗaya ce daga cikin gagararrun matsalolin da suka gunduri kowa, waɗanda suka tsunduma sabbin jinin shiga mawuyacin hali da yawaitar ayyukan ashsha. Masana sun tabbatar da cewa al’adar amfani da miyagun ƙwayoyin ba a kan daidai ba, ya na da alaƙar ƙut-da-ƙut wajen yaɗuwar miyagun laifuka a ƙasar nan. Bil hasali, yanayin da…
Read More
A saka hankali yayin zaɓin aure

A saka hankali yayin zaɓin aure

Assalam alaikum. Da fatan kowa ya yi sallah lafiya? Allah ya albarkaci jaridar Blueprint. A yau zan yi wasiƙa ne a kan zaɓin ma'aurata, domin shi ne babban abin da ke ci wa kowa tuwo a ƙwarya a halin yanzu. Wanda kuma hakan ke jawo yawan mace-macen aure, domin ana auren ne kawai barkatai ba tare da sanin wa ya kamata a aura ba. Babban hadafin da ya ke sanya mu zaɓar wanda zamu rayuwa da shi ko wacce zamu rayu da ita a matsayin rayuwar aure shi ne samun nutsuwar rayuwa, shi kuwa samun nutsuwar ruhi da abokiyar zama…
Read More
Shin waka da fim haram ne ko halal?

Shin waka da fim haram ne ko halal?

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Sakamakon tambaya da wani ya yi, cewar to wai ta ina ma ita harkar Fim ta sami wani halasci daga Qurani, Hadisi, ko ijtihadin Malamai? Sai na ga ya kamata na bada amsar tambayar tasa domin mahimmancinta, kuma domin a gane cewa shin a mahangar musulunci, shi kansa film din halal ne ko Haram? Abu na farko da zamu fara fahimta shine Allah ya ce mana; Q6:38 "...Ba mu yi sakacin barin komai ba cikin littafi (Quran)." Wato Qurani ya zo da duk wani hukunci, halal ko Haram, a kan duk wani abu da Allah ya…
Read More
Atiku: Daga gyangyaɗi ya zarce da minshari?

Atiku: Daga gyangyaɗi ya zarce da minshari?

Daga ALI ABUBAKAR SADIQ Duk sa'o'in Atiku Abubakar a siyasa, ko dai sun kwanta dama, ko sun yi ritaya daga siyasa. Kada mu manta Atiku Abubakar ya fara takarar shugaban kasa tun a shekarar 1993, shekaru 33 da suka gabata. Atiku ya yi gwagwarmayar siyasa da irinsu MKO Abiola, Shehu Yar Adua, Adamu Ciroma, Abubakar Rimi, Bashir Tofa, Babagana Kingibe da sauransu. A tsawon wannan gwagwarmaya tasa, sau uku ya sami cikakkiyar damar zama shugaban kasar Najeriya. Na farko a 1993 amma maslaha ta cikin gida ta sa aka ba shi hakuri ya janyewa Abiola. Bayan ya zama mataimakin shugaban…
Read More
Ai Arewa ta tsallake siraɗin Orkar

Ai Arewa ta tsallake siraɗin Orkar

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA In ba 'yan lakada-kawas ba da kuma ba mamaki wadanda ba su tashi a gaban dattawan kwarai ba, duk masu nazarin lamuran Arewa ba za su manta da yunkurin juyin mulkin 22 ga Afrilu 1990 ba da Manjo Gideon Gwaza Orkar ya jagoranta kuma ya yi wuf ya kori jihohin kokuwar Arewa daga Nijeriya. Duk muradunsa na dangantaka da yaƙi da tauhidi da kuma bunƙasa kantar ƙabilanci. Tabbas waɗannan muradun na Gideon Gwaza Orkar su ka kifar da yunƙurin kuma ya bar Arewa daram kamar yadda masu jajayen kunne su ka jarraba su ka yi bugun…
Read More
Yadda Gwamna Uba Sani ya biya diyya ga waɗanda El-Rufai ya yi wa rusau

Yadda Gwamna Uba Sani ya biya diyya ga waɗanda El-Rufai ya yi wa rusau

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnatin Jihar Kaduna a ƙarƙashin jagorancin Gwamna Uba Sani ta fara cika alƙawarin da ta ɗauka na tabbatar da adalci ga al’ummar unguwar Malali Low-Cost, inda ta miƙa sabbin filaye ga mazauna yankin da aka rushe musu gidaje a zamanin tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai. Babban Daraktan Hukumar Kula da Bayanai da Tsarin Filaye ta Jihar Kaduna (KADGIS), Dakta Bashir Garba Ibrahim, ne ya jagoranci rabon takardun mallakar filayen ga waɗanda abin ya shafa. Ya bayyana cewa, wannan mataki wani ɓangare ne na cika alƙawarin da Gwamna Uba Sani ya yi na ganin an yi wa…
Read More
Mutane da dama sun mutu bayan fashewar bom a Kwara

Mutane da dama sun mutu bayan fashewar bom a Kwara

Daga USMAN KAROFI Ana fargabar mutane da dama sun rasa rayukansu sakamakon fashewar bam da ya rutsa da wata motar haya kusa da ƙauyen Woro, a ƙaramar hukumar Kaiama, Jihar Kwara. Wannan lamari ya faru da safiyar Litinin, 23 ga Maris 2026, da misalin ƙarfe 7:43 na safe, lokacin da motar ke tafe daga ƙauyen Wurumakoto zuwa New Bussa a Jihar Neja. Direban motar, Malam Zubairu, ya yi tafiya ba tare da sani ba a kan bama-bamai da aka saka, wanda suka fashe nan take a kan motar. Fashewar ta kashe direban nan take, sannan ta jikkata wasu fasinjoji sosai,…
Read More